Gwamnan Jigawa Ya Amso Walida Daga Hukumar DSS
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, a daren jiya Laraba ya karɓo Walida Abdulhadi Ibrahim daga hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da ke Abuja.
Walida dai ta jima a hannun Hukumar ta DSS, wacce take binciken jami’inta mai suna Ifeanyi, wanda ake zargin ya sace ta daga Jigawa, ya tilasta mata shiga addinin Kirista, sannan kuma ya yi mata ciki har ta haifi jaririya, ba tare da sanin iyayenta ba.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, a yayin da Gwamna Namadi ke ƙarin bayani game da batun, ya ce batutuwan da suka shafi sace Walida, za a bar su ga kotu ta warware, yana mai tabbatar da cewa za a yi adalci a kan batun.
Gwamnan ya ce Walida ‘yar Jihar Jigawa ce kuma gwamnati za ta tabbatar da tsaron lafiyarta tare da cikakkiyar murmurewarta daga duk wata damuwa ko tashin hankali da take fuskanta.
Gwamnan ya samu rakiyar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Haruna Aliyu da Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari’a, Barista Bello Abdulƙadir Fanini da Kwamishiniyar Harkokin Mata, Hajiya Hadiza Abdulwahab da takwaransa na Ma’aikatar Muhalli, Dakta Nura Ibrahim Doka da sauransu zuwa hedikwatar DSS da ke Abuja.
A nasa ɓangaren, Babban Daraktan Hukumar DSS, Adeola Oluwatosin Ajayi, tare da manyan jami’an hukumar ne suka miƙa Walida ga gwamnan. Sannan kuma ya ce wanda ake zargi da sace Walida, wato Ifeanyi, yana tsare a hannun hukumar, wadda za ta ci gaba da bincike har zuwa ƙarshe. Yana mai tabbatar da cewa muddin wanda ake zargi ya aikata laifin, to zai fuskanci hukunci a hannun Shari’a.
Ya zuwa yanzu dai, ƙungiyoyin ‘yancin ɗan Adam daban-daban da sauran al’umma sun zuba ido tare da kiran cewa lallai a yi wa yarinya Walida da iyayenta adalci. Suna masu buƙatar lallai a hukunta Ifeanyi bisa cin zarafinta da ake zargin ya aikata.
__________













