• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, April 6, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)

FITILAR MATASA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
February 25, 2026
in Adabi
0
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)

Fitilar Matasa (02)

22
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)

BABI NA ƊAYA

Related posts

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026
Fitilar Matasa (02)

 

__________

Wane Ne Matashi?

Shin wane ne matashi kuma wane matsayi ke gare shi ga al’umma? Yaya rayuwar matashi ta kamata ta kasance kuma ta yaya matashi zai inganta rayuwarsa domin ta zama mai amfani ga karan kansa da ma al’umma baki ɗaya? In sha Allahu, a wannan bunƙasasshen tsokaci, za mu yi ƙoƙarin tattauna waɗannan tambayoyi da ma wasunsu da dama. Babban burinmu a nan shi ne, domin a ilimantar, a fahimtar da matasanmu, su fahimci rayuwa kuma su zama tsayayyu da ƙafafunsu, domin fuskantar kowane irin ƙalubale.

Ya kamata matasa su fahimci cewa, duniya ta dafe ƙeyarta, tana famfalawa da gudu ba tare da waiwaye ba. Don haka ya zama wajibi mu tashi tsaye domin ganin mun samu rayuwa daidai da zamanin da duniya ta kawo mu. Idan ba mu shirya, mun tunkari tsari da yanayin da duniya ke tafiya ba, babu shakka za mu ci gaba da zama kurar-baya. Za mu zama an dankwafar da mu – wanda kuma ba haka ya kamata ba, wai ƙanin miji ya fi miji kyau!

Matashi, kana da buƙatar jagora, kana da buƙatar busta, kana da buƙatar fitila mai haska maka gaba, domin ka kai ga gaci a lamuranka na rayuwa. Kamar yadda aka ambata a yayin gabatarwa, mun zaɓi yin amfani da salo da tarihin rayuwar wannan bawan Allah, Injiniya, Dokta Tukur Hassan Tingulin, domin gabatar da wannan muhimmin aiki ga al’umma. Ba don komai ba sai domin tafiya cikin tunani da hikima da azamarsa. Yana daga cikin cikin burinsa da ƙudurinsa, ya ga al’umma ta bunƙasa, matasa sun samu abin yi kuma sun samu nasara a rayuwa.

Har ila yau, bari mu ƙara tambaya, shin wane ne matashi? Wannan tambayar tana da muhimmanci ga matasa da ma al’umma gaba ɗaya, domin sai ka san kanka sannan za ka san matsayinka da ƙimarka a cikin al’umma. Ga sauran al’umma kuwa, yana da kyau su san wane ne matashi kuma ta yaya za a mu’amalance shi, domin inganta al’umma gaba ɗaya?

Kamar yadda Ƙamus ɗin Oxford ya ce, matashi shi ne mutum (mace ko namiji) mai ƙuruciya, wanda ya kusa ko kuma ya balaga. Kundin Encyclopedia Americana kuwa cewa ya yi: Rayuwar Matashi (mace ko namiji), wani lokaci ne ko yanayi da yake shirya yara zuwa ga balaga, sannan su kai ga zama mutane, ta hanyar tsarabe-tsaraben rayuwa, ƙalubale ta fuskar zamantakewa, ɗabi’a da halayya da tohon jiki da na ƙwaƙwalwa.

Ita kuwa Ƙungiyar Haɓaka Ilimi, Zamantakewa da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) da Ƙungilar Ƙwadago ta Duniya sun bayyana cewa matashi (mace ko namiji) na kasancewa ne daga shekara 15 zuwa 24. Shi kuwa Asusun Tallafa wa Matasa na Majalisar Ɗinkin Duniya (UN Habitat – Youth Fund), cewa ya yi matashi na kasancewa ne daga shekara 15 zuwa 35. A yayin da ita ma Ƙungiyar Matasan Afirika (The African Youth Charter) ta jaddada cewa matshi na kasancewa ne daga shekara 15 zuwa 35. Akwai kuma masanan da ke nuna cewa matashi na kasancewa ne tun daga shekara 15 zuwa shekara 40.

Ya kai matashi, bisa ga waɗannan bayanai da suka gabata, lallai ne ka gane cewa ba ka da isasshen lokacin ɓatawa wajen wasa. Ka yi ƙoƙarin fuskantar rayuwa bisa fahimta, domin ta zama mai amfani gare ka da ma al’ummarka.

Ta yaya haka za ta faru? Ku nazarci wannan littafi da natsuwa da basira, domin kuwa yana ƙunshe da hikimomi ta sigar tsokaci, misalai, falsafa da  shawarwari da jagora.

__________

Za a ci gaba ranar Lahadi, in sha Allah

Previous Post

Nazari Da Sharhin Littafin AJN Tremearne ‘Hausa Superstitions and Customs’

Next Post

Jigawa State Government is Proactive on Walida’s Case – Hamisu Mohammed Gumel

Related Posts

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue
Adabi

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)

March 1, 2026
Next Post
Jigawa State Government is Proactive on Walida’s Case – Hamisu Mohammed Gumel

Jigawa State Government is Proactive on Walida's Case - Hamisu Mohammed Gumel

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Air Strikes Decimate Terrorist Hideout in Katsina State

Air Strikes Decimate Terrorist Hideout in Katsina State

June 18, 2024
TAURARON GIZAGO: Idris Ibrahim Kubau

TAURARON GIZAGO: Idris Ibrahim Kubau

August 13, 2023
ALLAH JI ƘAN AMINU DOGO

ALLAH JI ƘAN AMINU DOGO

June 29, 2025
Katsina State at 37: Reflecting on Successes, Challenges, and the Way Forward

Katsina State at 37: Reflecting on Successes, Challenges, and the Way Forward

September 23, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)
  • JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles

Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles

April 5, 2026
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)

April 4, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.