• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, April 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (2)

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
December 28, 2025
in Gizago
0
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (2)

Bikin Hawan Sallah a ƙasar Hausa

59
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (2)

Daga Yahuza Malumfashi

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Bikin Hawan Sallah a ƙasar Hausa

 

                       __________

√ Muradun Kafa Ƙungiyar Ƙabilancin Hausawa Zalla:
Ɗaya daga cikin iƙirarin da Hausawan Bogi, masu kwarmato a Soshalmidiya suke yi shi ne, muradunsu na kafa ƙungiyar ƙabilanci ta Hausawa Zalla, kamar dai yadda ƙananan ƙabilu suke yi, kamar Miyetti Allah ta Fulani, Ohaneze Ndigo ta Inyanurai ko Afenifere ta Yarabawa da sauran ƙungiyoyi irin su.

Amma abin tambaya nan shi ne, shin ko al’ummar Hausawa Zalla suna da ‘yancin kafa ƙungiya ta ƙabilanci a Najeriya? To, in sha Allahu yanzu zan ɗan yi ƙoƙarin amsa ta, tare da ɗan tsokaci madaidaici.

Tabbas, ba wai Hausawa zalla ba, duk wani ɗan ƙasa yana da ‘yancin kafawa ko shiga cikin kowace ƙungiya da yake muradi, domin kuwa Sashi na 40 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ne ya ba shi wannan ‘yancin.

Ga abin da wannan Sashe na 40 yake cewa: “Kowane mutum yana da ‘yancin haɗa taro da sauran mutane kuma musamman zai iya kafawa ko kuma ya shiga cikin kowace jam’iyyar siyasa, ko ƙungiya, domin kare muradunsa. Sai dai kuma wannan ‘yanci ba zai ci karo da ikon da Kundin Tsarin Mulkin nan ya ba Hukumar Zaɓe ta Ƙasa Mai Cin Gashin Kanta ba, dangane da abin da ya shafi jam’iyyun siyasa, wanda hukumar ba ta amince da shi ba.”

Ke nan Tsarin Mulkin Najeriya ya amince wa ‘yan ƙasa kuma ya ba su ‘yancin yin taro cikin lumana, ko su kafa ƙungiya, misali ta ƙabila, ko addini, ko siyasa, ko ta sana’a, ko kuma ta kare muradun ma’aikata da makamantansu.

Bisa ga doron doka da ‘yancin ɗan ƙasa, al’ummar Hausawa zalla, kamar sauran ƙabilu, suna da ‘yancin kafa ƙungiyar kare muradunsu, kamar dai yadda sauran ƙabilu, misali Fulani, Yarabawa, Ibo da sauransu suke kafawa.

Sai dai kuma, kamar yadda masana al’amuran Shari’a da Tsarin Mulki suka sha nanatawa, inda haƙƙin wani ɗan ƙasa ya fara, nan kuma haƙƙin wani ɗan ƙasar yake tsayawa. Ma’ana dai, duk ƙungiyar da za a kafa, dole ne ta kasance bisa doron doka da odar ƙasa. Dole ta kasance mai manufar zaman lafiya da mutunta sauran al’ummar ƙasa.

Nan zan ɗiga aya a yau. Mu tarbi kashi na gaba, domin tattauna tambaye ta gaba mai cewa, shin da wace manufa ake son kafa Kungiyar Hausawa Zalla? Manufa ce ta alheri ko sharri?

Naku, Bashir Yahuza Malumfashi, Taskar Gizago.
__________

Previous Post

Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

Next Post

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (3)

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (3)

Yunkurin 'Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (3)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

YAU 40: ALLAH YA JI ƘAN HAJIYA ZAINAB AHMAD

YAU 40: ALLAH YA JI ƘAN HAJIYA ZAINAB AHMAD

June 26, 2024
SHUGABA BUHARI: TA’AZIYYAR JAN GWARZO

SHUGABA BUHARI: TA’AZIYYAR JAN GWARZO

July 20, 2025
Ya Kamata Marubuta Mu Karkata Alƙalaminmu Ga Matsalolin Al’umma

Ya Kamata Marubuta Mu Karkata Alƙalaminmu Ga Matsalolin Al’umma

May 26, 2025
Buɗe Boda Ba Zai Durƙusar Da Mu Ba – Shugaban Ƙungiyar Makiyaya Kaji

Buɗe Boda Ba Zai Durƙusar Da Mu Ba – Shugaban Ƙungiyar Makiyaya Kaji

July 24, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.