• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, April 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (3)

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
December 30, 2025
in Gizago
0
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (3)

Al'adar Hausawa da Fulani ɗaya ce

45
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (3)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi
                         __________

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Al’adar Hausawa da Fulani ɗaya ce

√ Mece Ce Manufar Kafa Ƙungiyar Hausawa Zalla?
A wannan muƙala, a yau za mu yi ninƙaya ne a cikin kogin wata muhimmiyar tambaya, mai cewa, shin mece ce manufar kafa Ƙungiyar Hausawa Zalla? Shin alheri aka nufa ko kuwa sharri?

Masu salon magana dai sun ce, sonsomin hauka, zubar da miyau. Haka kuma sun ce, Juma’ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake gane ta. Kamar kuma yadda suka ce, sanin asali, shi ke sanya kare gurgurar alli. Duka dai, masu azancin na magana sun ce, nuna mani abokinka, ni kuma in gaya maka ko kai wane ne.

Daga dukkan alamu, babu alheri, babu gaskiya, babu mutunci a batun samar da wannan ƙungiya ta Hausawa zalla. Shin wane dalili ne ya sanya na ce haka? Ku yi haƙuri ku biyo ni. Da sannu zan rarrabe maku zare da abawa. Zan bakace maku tsakanin aya da tsakuwa.

Dalili na ɗaya, me ya sanya masu ƙumajin kafa ƙungiyar nan suke ta zagaye-zagaye, suna ta kai gwauro da mari da yasassun zantuttuka a soshalmidiya, game da ƙungiyar, tun ma kafin su kafa ta? Haka kuma me ya sa suke yin basaja, suke canja suna, suna bijiro da kalaman ɓatanci, tozarci da ƙabilanci a dukkan musharaƙarsu da mutane, musamman ma idan ka saɓa da ra’ayinsu.

A tsarin tunani mai kyau, idan har ƙungiyar alheri ake son kafawa, to kai tsaye za a tunkari al’amarin, bisa doron doka. Maimakon kwarmato da habaice-habaice da zage-zage da zarge-zarge da ƙullatar wasu al’umma na daban da ‘ya’yan ƙungiyar suke yi tun kafin a kafa ta, da kawai za su tafi Hukumar Yi Wa Kamfanoni da Ƙungiyoyi Rijista (CAC), su gabatar da takardar buƙatarsu; su cika dukkan sharuɗɗan da doka ta tanada, domin samun rijista salun-alun, kamar yadda duk wata ƙungiya ta Allah da Annabi take yi.

Amma ina! Maimakon haka sai masu Ƙungiyar Hausawa Zalla suka fara saƙa da mugun zare. Tun ma kafin a je ko’ina, duk inda ka ga zancensu a soshalmidiya, to zance ne mai kaushi. Zance ne ko dai na zagi ko kuma na tsokanar fitina, ko kuma na kawo saɓani da rashin jituwa tsakanin al’umma.

Kuma za ka ga cewa ba su son a yi masu wata tambaya ko ƙalubale da ya saɓa wa ra’ayinsu. Cikin lokaci za ka ga sun azazzalo da zage-zage da yarfe da halayya irin ta a-ware da nuna bambanci da baƙin ƙabilanci. Kuma mafi yawa daga cikinsu, za ka ga sun kulle profile ɗinsu. Wasu da dama daga cikinsu, suna amfani ne da sunayen bogi. Mutumin da ke da niyyar alheri, me ya kai shi ɓoye sunansa na asali? Me ya sa zai kulle hanyar da za a san shi sosai?

Wata baƙar halayya da ke tattare da mutanen nan ita ce, yadda suke jirkita tarihi, musamman ma dangane da al’ummar Arewa. Maimakon su fito da manufarsu kai tsaye, sai ka ga sunanta rara-gefe da sukar Jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, su yi ta la’antar Fulani tare da bijiro da kalaman tsana da ƙiyayya ga ƙabilar Fulani. Kamar kuma yadda suke kawo batun raba alaƙa tsakanin al’ummar Arewa, wai da sunan kishin Hausawa.

A hannu ɗaya kuma, wani abu mai ɗaura kai, za ka ga suna alaƙanta kansu da addinin da ba na Musulunci ba, wanda kuma shi ne addini mafi kusanci da mafi yawan al’ummar Hausawa. A hannu ɗaya, za ka ga suna kishin Inyamurai da ƙabilun Middle Belt. A zahiri, Hausawa da Fulani, su ne aka san suna jiɓantar juna, su ne suke tare da juna, su ne suke da kamanceceniyar al’ada, wurin zama da addini. To, wane dalili zai sanya a ƙirƙiri ƙungiyar da za ta haifar da saɓani da rashin jituwa tsakanin al’ummu biyu da je zaune da juna na tsawon shekaru. Al’ummun da suka yi auratayya, suka hayayyafa kuma suka saje da juna, kamata ya yi a samu dalilin da zai ƙarfafa zamantakewa da aminci da juna, ba wai a kawo ƙungiyar da za ta wargaza su da dafin ƙabilabci ba

Shin duk ƙungiyar da ke nufin al’ummar ƙasa da alheri, anya za ta riƙa nuna waɗannan baƙaƙen halaye ga sauran al’umma? Kayya! – Lallai akwai lauje cikin naɗi. Kuma da sannu lamura za su fito fili. Al’umma za su fahimci mugun ƙuduri da nufin wannan muguwar ƙungiya da ta zaɓi kafa ƘABILANCI a cikin al’ummar da ke buƙatar ZUMUNCI da LUMANA da juna.

Jama’a, nan zan ɗiga aya. Sai a tari kashi na gaba, domin amsa dalilan da ke tabbatar da cewa, babu shakka Ƙungiyar Hausawa Zalla, ƙungiya ce ta Hausawan Bogi, ƙungiyar ‘yan Basaja, ƙungiyar ‘yan Ba-Zara kuma babu shakka, ba da alheri ta taho ba.

Previous Post

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (2)

Next Post

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (4)

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (4)

Yunkurin 'Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (4)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

SHUGABA BUHARI: TA’AZIYYAR JAN GWARZO

SHUGABA BUHARI: TA’AZIYYAR JAN GWARZO

July 20, 2025
SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA

SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA

December 11, 2024
Ba Mu Goyon Bayan Juyin Mulki Kuma Ba Ma Goyon Bayan Yaƙi Da Niger

Ba Mu Goyon Bayan Juyin Mulki Kuma Ba Ma Goyon Bayan Yaƙi Da Niger

August 5, 2023
Abba Kyari: Ya Kamata A Duba Lamarinsa Da Adalci

Abba Kyari: Ya Kamata A Duba Lamarinsa Da Adalci

July 2, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.