Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine
Daga Farfesa Dauda Ojobi

•••••••
Shahararren malamin Musulunci, Farfesa Dauda Ojobi ya shahara wajen muƙabala dangane da addinan Musulunci da Kiristanci, kamar yadda ya yi suna wajen wallafa littattafan tarihin addinai da makamantansu, ya fitar da sabon littafinsa, wanda ya rubuta a kan tarihin Muhammadu Marwa Maitatsine.
Shin waɗanne dalilai ne suka sanya malamin ya rubuta wannan littafi? Ga wasu dalilai guda huɗu da mawallafin ya fitar dangane da wannan mashahurin littafin:
√ Maganar Wani Malami A Katsina:
Wannan shi ne abu na farko da ya fara janyo hankalina a kan in yi bincike mai zurfi dangane da Maitatsine.
A shekarar 2023 aka samu wani Malami kuma shugaban ƙungiyar masu bin koyarwar Maitatsine a Jihar Katsina, mai suna Dr. Isma’il Zakariyya Al-Kashnawy. Shi ne ya fito ƙarara ya ce: “Muhammadu Marwa Maitatsine, zaluntarsa aka yi kuma za mu rama wannan zaluncin da aka yi masa.”
Lallai wannan maganar ta girgiza hukumomi a lokacin saboda a cikin sati ɗaya sai aka ji wannan malamin ya ƙara fitowa yana cewa: ” Na ba da haƙuri a kan maganar da na yi satin da ya gabata saboda ta yi wa wasu zafi.”
Dalili na farko ke nan da ya sa na zabura, domin tattaro tarihin Maitatsine saboda in san wane ne shi kuma mene ne ya faru da shi?
√ Babu Wani Gamsasshen Rubutu A Kan Tarihin Maitatsine:
A lokacin da na zabura domin tattaro bayanai, sai na lura cewa a rubuce, gaskiya babu wani gamsasshen rubutu a kan tarihin Maitatsine, tun daga farkon rayuwarsa har zuwa mutuwarsa. A inda na tarar cewa mafi yawan littattafan sun karkata ne kawai zuwa ga wani abu ɗaya ko biyu game da maitatsine.
Daga cikin littattafan da aka yi rubuta a kan Maitatsine, akwai: 1-The Kano Disturbances Tribunal of Inquiry. 2-The New Nigerian Newspaper (1979, 1980, 1981, 1982). 3-The New Standard Newspaper (1979, 1980, 1981, 1982). 4-The Maitatsine Risings in Nigeria by Elizabeth Isichei. 5-The Maitatsine by Nasiru Zaharaddeen. 6-Hira ta musamman a kan tarihin Maitatsine, a Gidan Rediyon Rahama ta Jihar Kano. 7-‘Yan Al-Kur’aniyyun, ‘Yan Tatsine, Ƙalaƙato: Tarihin Kafuwarsu Da Aƙidunsu, Daga Sheikh Ja’afar Mahmud Adam.
Waɗannan su ne littafai da bayanai, waɗanda na samu a taƙaice game da tarihin Maitatsine.
√ Na Ƙuduri Rubuta Tarihin Maitatsine Domin Ankarar Da Al’ummar Baya:
Lallai wannan shi ne babban maƙasudina na wannan aiki. Kodayake tabbas hukumomin ƙasarmu ba su wasa da bibiyar ƙananan labarai, sai dai kash, idan sun gano matsala, to ɗaukar mataki yana zama musu wani aiki mai wahala. Ina fatan Allah ya taimake su a kan aiki da gaskiya kuma ya sauwaƙe musu bin ta, Amin.
√ Rashin Adalcin Wasu Daga Cikin Waɗanda Suka Yi Rubutu A Kan Maitatsine:
Tabbas wasu daga cikin marubuta sun ɓoye gaskiya a kan ilimi ko akasin hakan. Sannan sun canza asalin abin da ya faru, shi ma a kan ilimi ko akasin hakan. Sannan sun yi rashin adalci ga harkar almajiranci da sauran wasu al’amura da suke da alaƙa da Musulunci.
_______________













