Janar M.B. Uba: Muzakkarin Da Ya Sadaukar Da Ransa Ga Najeriya
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

•••••••
Akwai takaici matuƙa yadda muzakkarin soja, Janar Uba ya rasa ransa, a sakamakon azarɓaɓi da kauɗin ‘yan jaridar jeka-nayi-ka na Soshiyalmidiya. Kowane lamari yana da sanadi amma tabbas, babu wanda za a ɗora wa sanadin rashinsa sai ‘yan kwarmaton Soshiyalmidiya.
Tun da farko dai, kamar yadda labari ya tabbata, ‘yan ƙungiyar ISWAP sun yi wa sojoji kwantan-ɓauna a hanyar Burum zuwa Kubua a tsakanin Damboa zuwa Biu. Muzakkarin Janar ɗin ya yi nasarar kuɓutar da mutanensa, ta hanyar kinaya da dubarar yaƙi kuma ya samu fakewa a cikin dajin Sambisa.
Daga wannan wurin da ya ɓuya, ya riƙa tattaunawa da Kwamandan Yaƙi, inda ya tabbatar masa da cewa yana lafiya kuma yana raye. Ya aika saƙon ne ta hanyar WhatsApp. Haka kuma ya tura masu taswirar ainahin inda yake ɓoye a dajin. Nan take kuma sojojin Operation Haɗin Kai suka ƙaddamar da aikin ceto shi ta sama da ƙasa.
Sai dai kafin mahukunta su fitar da sahihan bayanai, shafukan Soshalmidiya suka cika da labarun ƙarya, masu tayar da hankali. Wasu kafafen sun yi gaugawar yaɗa cewa ‘yan ISWAP sun sace wani Kwamandan Soja. Wannan labari mai firgitarwa, shi ne ya bazu kamar wutar daji da bazara.
Wannan azarɓaɓi da kauɗi na ‘yan Soshiyalmidiya, shi ne ya haifar da tsintsinar tsaya, ya haddasa ruɗanin bayanai. Yayin da labarin ke yawaita, ta haka ‘yan ta’adda, waɗanda tun farko ba su da cikakken bayanin inda Kwamandan yake, suka fahimci lamarin. Dalili ke nan dakarun ISWAP, ɓangaren Ba Shuwa da Abu Ƙudama suka ƙara matsa bincike cikin dajin, domin gano maɓoyar Janar Uba.
A lokacin da labaran na ƙarya ke kan bazuwa, ƙwararren ɗan jarida mai rahoto kan lamurran tsaro, Zagazola ya ƙaryata dukkan su, yana tabbatar da cewa saƙonnin bidiyo da Kwamandan ya fitar sun tabbatar da cewa yana raye, ba a ji masa ciwo ba, kuma ba ya cikin haɗari.
Abin takaici, daga baya sai sojojin ceto suka kasa samun wayar Janar Uba, sannan ba su same shi a wurin da ya ce yana ɓoye ba da farko. Kwamandan Yaƙi da kansa ya jagoranci sojoji zuwa Azir, inda suka shafe kusan awa 24 suna nemansa, ba tare da samun wata alama ta inda yake ba. Daga ƙarshe dai, ‘yan ta’addan sun rutsa da Janar ɗin ne a yayin da yake ƙoƙarin fita daga dajin da suka mamaye. Daga nan kuma abin da zai faru ya faru.
Wannan lamari ya sake nuna babban ƙalubale da ake fama da shi a rahoton rikici. Ya nuna yadda bayanai da aka yi gaggawar yaɗawa za su iya jefa jami’an tsaro cikin haɗari, tare da taimaka wa ƙungiyoyin ta’addanci ta hanyar ba su bayanan sirri ba tare da sani ba.
A nan, lallai ya kamata duk wani mai amfani da shafukan Soshiyalmidiya ya yi taka-tsan-tsan da irin bayanan da zai riƙa yaɗawa. Haka kuma, ya kamata hukumomi su ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kan duk wata kafar labarai da take watsa bayanai masu haɗari ga lamurran tsaro. Hakan zai taimaka wajen rage irin waɗannan matsaloli.
_______________













