A Yayin Da Taron Katsina Facebook Connect Ke Ƙaratowa

•••••••
Kamar yadda aka saba, idan Allah ya kai mu Disamba, za a gabatar da taron Katsina Facebook Connect Kashi Na Shida. Wannan ke nuna cewa yau shekara shida ke nan da fara gudanar da wannan taro na sada zumunta da wayar da kan al’umma.
Taken taron na bana shi ne: “Rawar Da Kafafen Sadarwar Zamani Ke Takawa Wajen Ingantawa Ko Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa.” Hakan ke nuna cewa masana da manazarta al’amuran rayuwa za su tattauna dangane da wannan take, inda za a duba rawar da wannan kafa ke takawa dangane da ci gaban al’adunmu ko kuma akasin haka.
Babu shakka Soshalmidiya ta zo mana da abubuwa masu tarin yawa, wasu na amfani, wasu kuma masu kassara mu. Misali, an samu canje-canje wajen ɗabi’a, kasuwanci, ilimi, nishaɗi da sauransu. Wannan ke nuna cewa al’amarin ya zama tamkar hanjin jimina – akwai na ci kuma akwai na zubarwa. Don haka nazari da tafiyarsu, abu ne mai amfani, domin ɗora al’umma zuwa ga nagartattun hanyoyi da kuma gargaɗi wajen guje wa gurɓatattu.
Muna roƙon Allah ya ka mu lafiya kuma ya ba mu ikon halarta cikin ƙoshin lafiya, Amin.
_______________












