• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, April 6, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Dokta Bukar Usman, Sarkin Daura Da Bikin Ranar Hausa Ta Duniya

BABBAN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 2, 2025
in Babban Labari
0
Dokta Bukar Usman, Sarkin Daura Da Bikin Ranar Hausa Ta Duniya
28
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Dokta Bukar Usman, Sarkin Daura Da Bikin Ranar Hausa Ta Duniya

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

April 2, 2026
Gwamnan Jigawa Ya Amso Walida Daga Hukumar DSS

Gwamnan Jigawa Ya Amso Walida Daga Hukumar DSS

February 26, 2026
Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, CON. Hoton Tsakiya: Daga Hagu; Yawale Kallah Musa, Bashir Yahuza Malumfashi da Magaji Daura

__________
Hausa, bunƙasasshen harshe ne mai daɗaɗɗen tarihi, wanda a halin yanzu ya kama hanyar kutsawa da mamaye harasa da dama a faɗin duniya. Girmansa da tasirinsa ne suka sanya har aka kai ga ware rana ta musamman domin gudanar da shagulgulan biki a kansa.

Bikin Ranar Hausa na Duniya na bana, wanda aka gudanar a Fadar Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, a ranar Talata, 26 ga Agusta, 2025 ya zama daban da na sauran shekaru da suka gabata, saboda dalilai masu dama.

Bashir Yahuza Malumfashi yana gaisuwa ga Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, CON, jim kaɗan da kammala karanta waƙar Sadauki daga littafin Galadima

A bikin na bana, wanda shi ne karo na goma, Hukumar Kiyaye Tarihi da Al’adu ta Jihar Katsina tare da haɗin gwiwar Masarautar Daura ne suka ɗauki nauyin gudanar da shi, bisa kulawar fitaccen ɗan jarida kuma mai kishin Hausa, Abdulbaƙi Aliyu Jari, wanda tun da farko, shi ne ya fara ƙirƙiro shi a shekarar 2015.

Taken bikin na bana shi ne, “Amfani da Harshen Hausa Domin Wanzar Da Zaman Lafiya.” Wannan kuwa yana zuwa ne, bisa lura da yadda yankunan Arewa ke fama da matsalolin tsaro, musamman ma yadda ‘yan bindiga suka addabi al’umma da kashe-kashe, lalata dukiya da kuma sace mutane tare da amsar kuɗin fansa.

Mafarauta, a yayin bikin Ranar Hausa Na Duniya

Muhimman mutane masu kishin Hausa daga sassa daban-daban na duniya, sun taka muhimmiyar rawa wajen ƙara wa bikin armashi. Ɗaya daga cikinsu, shi ne fitaccen marubuci, tsohon Babban Sakatare a Fadar Gwamnatin Tarayya kuma masanin al’amuran tsaro, Dokta Bukar Usman.

A matsayinsa na Shugaban Ƙungiyar Nigerian Folklore Society, mai kiyaye al’adun al’ummar Najeriya, Dokta Usman ya tattara manyan littattafai na dubban Nairori, ya aika zuwa ga Fadar Mai Martaba Sarkin Daura, a matsayin gudunmowarsa ga bikin na Ranar Hausa ya Duniya.

Da yake gabatar da litattafan ga mai martaba Sarkin, wakilin Bukar, Malam Bashir Yahuza Malumfashi ya bayyana cewa littattafan muhimmai ne da suka shafi al’amura da dama na rayuwar al’umma, wanda suka haɗa da tarihi, al’adu da tatsuniyoyi.

Abdulbaƙi Aliyu Jari, tare da Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar, CON

“Ya mai martaba, a cikin littattafan nan da suka haura guda 20, akwai kamar guda biyar da zan ɗan yi ƙarin bayani a kansu. Na ɗaya, akwai babban kundin Taskar Tatsuniyoyi, wanda shi Bukar da kansa ya tattara su kuma ya rubuta su, sannan ya ɗauki nauyin wallafa su. Kundi ne da yake ƙunshe da littattafai guda 14, na tatsuniyoyin Hausa daban-daban, domin bunƙasa adabin Hausa,” in ji Malam Bashir.

“Akwai kuma littafin Zaɓaɓɓun Tatsuniyoyin Hausa, wanda aka wallafa da Ajami, domin wayar da kan al’umma, musamman a makarantun tsangaya na karkara. Shi ma wannan littafi, Dokta Bukar ne ya samar da shi domin farfaɗo da rubutun Ajami da al’adun Hausawa.”

Ya ci gaba da cewa, “Akwai kuma littafin A History of Biu (Tarihin Biu). Dokta Bukar, wanda shi ne ya rubuta littafin, ya zaɓi ya aiko wa Masarautar Daura da shi, saboda akwai alaƙar tarihi tsakanin al’ummar Daura da ya Biu, ta ɓangaren Bayajidda (Daura) da kuma Yamtarawala (Biu), waɗanda jarumai ne da suka yi zamani shekaru aru-aru da suka shuɗe;” in ji Bashir.

Manyan baƙi, tare da Mai Martaba Sarkin Daura, a yayin bikin

Ya kuma ce akwai littafin da babban ɗan jarida, Malam Garba Shehu ya rubuta, mai taken According to the President inda ya bayyana yadda ya yi aiki da Marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari (ɗan Daura).

“Baya ga waɗannan,” in ji Bashir Malumfashi, “akwai kuma littafin waƙoƙin fasaha, wanda ni na rubuta, mai taken Galadima. A cikin littafin, akwai waƙar kirari ga mai martaba Sarkin Daura, mai taken Sadauki. Duka waɗannan littattafai, Dokta Bukar, a ƙarƙashin gidauniyarsa, ya ce in kawo maka.” A cewar Bashir, wanda daga bisani ya karanta waƙar Sadauki a gaban Sarki da fadawansa.

Mahaya, a yayin Bikin Ranar Hausa Na Duniya a Daura

Da yake nasa bayanin, bayan kammala karanta waƙar Sadauki, mai martaba Sarkin Daura ya yi murna tare da godiya ga Dokta Bukar Usman. “Babu shakka waɗannan littattafai da ka aiko mana suna da muhimmanci a gare mu. Musamman ma Masarautar Daura tana da abin tarihi dangane da jarumi Yamtarawala. Tarihi ya tabbatar da cewa ya taɓa zuwa Daura, har ya yi aure, sannan ya wuce da iyalinsa zuwa Biu. Don haka muna godiya, Allah saka da alheri.”

An yi ittifaƙin cewa akwai kimanin mutum miliyan 200 da ke amfani da harshen Hausa a faɗin duniya, inda ƙasar Nijar a yanzu haka sun saka harshen a matsayin na gudanar da al’amuran gwamnati.

Bikin na bana ya samu halartar hukumomin ƙasar Nijar, inda Gwamnan Zinder, Muhammad Sani Masallaci ya wakilci Shugaban Ƙasa, Janar Muhammad Tchani.

Mahaya dawakai, a yayin Bikin Ranar Hausa Na Duniya a Daura

Haka kuma an samu wakilai daga ɗaukacin manyan garuruwan Hausa Bakwai da ‘yan uwansu bakwai. Sanata Ibrahim Ida, Sakataren Masarautar Katsina, wanda ya wakilci Sarkin Katsina Abdulmunini Kabir Usman a wurin bikin, ya yi kira ga hukumomi da a maida hankali wajen bunƙasa harshen, musamman ganin yadda ɗaliban da ke nazartar harshen suke raguwa a jami’o’i da kwalejojin ilimi a Najeriya.

Bikin ya yi armashi, inda aka gudanar da kaɗe-kaɗe da raye-rayen gargajiya, hawan dawakai, damben gargajiya da sauran shagulgula na al’adar Bahaushe. An kammala komai lafiya, tare da fatan za a gudanar da wanda ya fi shi armashi a shekara ta gaba.

Previous Post

Dr. Bukar Usman, Emir of Daura, and the 2025 World Hausa Day Celebration

Next Post

BAKIN JAƁA (2) (Labarin Cin Amana)

Related Posts

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel
Babban Labari

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

April 2, 2026
Gwamnan Jigawa Ya Amso Walida Daga Hukumar DSS
Babban Labari

Gwamnan Jigawa Ya Amso Walida Daga Hukumar DSS

February 26, 2026
Wata Mata Ta Haifi “Hatsabiban Jarirai” A Ofishin Hukumar NDLEA
Babban Labari

Wata Mata Ta Haifi “Hatsabiban Jarirai” A Ofishin Hukumar NDLEA

February 22, 2026
Next Post
BAKIN JAƁA (2) (Labarin Cin Amana)

BAKIN JAƁA (2) (Labarin Cin Amana)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

GIRO ALLAH KYAUTA MAKWANCI

GIRO ALLAH KYAUTA MAKWANCI

September 6, 2023
Rusau A Kano: Ba A Gyara Kuskure Da Kuskure

Rusau A Kano: Ba A Gyara Kuskure Da Kuskure

June 11, 2023
Burina In Samar Da Maslaha Tsakanin Ma’aurata – LIKITAR MA’AURATA

Burina In Samar Da Maslaha Tsakanin Ma’aurata – LIKITAR MA’AURATA

August 8, 2023
Shin Ka Kuwa Kalli Fim Ɗin The Lord of the Ring

Shin Ka Kuwa Kalli Fim Ɗin The Lord of the Ring

May 29, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)
  • JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles

Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles

April 5, 2026
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)

April 4, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.