SHUGABA BUHARI:
TA’AZIYYAR JAN GWARZO
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Tun da farko, wannan waƙe mai taken SHUGABA BUHARI, Bashir Yahuza Malumfashi ne ya rubuta shi shekara ta 2019 kuma aka wallafa shi shafi na 20 zuwa na 22, a cikin jerin waƙoƙin littafinsa mai taken GALADIMA – WAƘOƘIN FASAHA; wanda aka wallafa a shekara ta 2020. A wannan karo, Bashir ya yi masa Tahamisi, ya koma mai ɗango biyar daga mai ɗango biyu, a matsayin ta’aziyya ga tsohon Shugaban Ƙasa Janar Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi 18-01-1447 (Hijiriyya), 13-07-2025 (Miladiyya).
__________
Allah mun maka godiya.
Don kai ne mai Rahamaniya.
Kai ka aiko Manzon Shiriya.
Mun dace mutanen Najeriya.
Ka ba mu zaki mai juriya.
Dogo fari, ba ya fariya.
Ba ya zamba a aminciya.
Sunansa ne mai gaskiya.
An shaida haka bai ƙullalliya.
Jarumi irin ya mazan jiya.
Jajitacce ga batun gaskiya,
Tun yarinta har tsufiya,
Tun makaranta can jiya,
A mu’amala ba ya zamiya,
Adalci ya tsare ba togacciya.
Inuwarsa zalumai ba sa kwanciya,
“Wane mutum” kun ji kalamiya,
In ji mutuwa ta Bahaushiya.
A daɗe anai sai gaskiya.
Jirgin fiton da ba ya tangalniya.
Ya kama aiki babu hayaniya.
Ƙirjinsa kishin Najeriya,
Domin a gyara duka nahiya.
Mutane su zamto kintsiya.
Burinsa kullum a zauna lafiya.
A harkokinsa babu ma’asiya.
Ba ya zina, ba ya shan giya.
Ba ya sata ko taɓa haramiya.
Ba ya faɗa ko ko hayaniya.
Ba ya ashar ba ya hauragiya.
Adalci tutur yaka dulmiya.
Burinsa tsarin gaskiya.
Babba ko ƙarami ai tafiya.
Ko a mulki ko yarjejeniya.
Talaka, attajiri ba bambanciya.
A yi alheri ya yi ishariya.
A riƙe zumunci kulliya.
A riƙe amana babu zalamiya.
A riƙe iyali, a zam riƙa yafiya.
A bar zalunci yai gargaɗiya.
Al’ummun kowace shiyya,
A cikin ƙasa Najeriya,
Goro marsa ya wuce tsutsiya.
Sun aminta da Buhariya.
Sun ba shi amana bai ɗaya.
Farko a gida ba tambaya.
Kowa bar gida ya yi asariya.
Gida zai bar shi cikin tsiya.
Lallai Buhari ko ya tsaya,
A Arewa bai gogayya.
Hausa, Angas da Fulaniya,
Gwari, Babur da Batorankiya.
Kano, Kaduna, Haɗejiya
Binuwai, Borno da Lafiya.
Tibi, Margi da Bakilbiya.
Musulmi kam na haƙiƙiya
Masoyan Manzo na Arebiya.
Baban Fati Batula Sarauniya.
Ina ‘yan amana a Ikilisiyya,
Kiristocinmu jimla a nahiya?
Sun yo caffar lamari ɗaya.
Babban aiki sai gayya.
Kai ko raggo ka ja baya.
Ga jarumi mai juriya.
Farin aiki nemo tumfafiya.
A Kudunmu gida Najeriya,
Mutan Ikko jerangiya.
Mu je Kalaba tun safiya.
Mutan Anambara kwan lafiya.
Yarabawa har da Ibon niya.
Sun yo ɗauki babu kacaniya,
Sun amince da Buhariya.
Sun yarda a zo tafiya ɗaya.
Gyaran lamarin Najeriya.
Sun yarda da halin juriya.
Aikinka Buhari ijariya.
Ka yi naka mu sai godiya.
Ka bauta Allah shi ɗaya.
Ka yo zumunci bai ɗaya.
Allah ya hana ka tijariya.
Allah ka yo masa kariya
Sannan ka yo masa yafiya.
Sanya shi cikin Firdausiya.
Ka inganta shi da kariya.
Daga zaluncin ‘yan duniya.
__________
© Bashir Yahuza Malumfashi,
Laraba 22-01-1447 (Hijiriyya)
17-07-2025 (Miladiyya)













