• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 17, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

GWAMNAN JIHAR NIGER YA ƘADDAMAR DA YAƘI DA TSAGERU DA ƁATAGARI

BABBAN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
April 23, 2025
in Babban Labari
0
GWAMNAN JIHAR NIGER YA ƘADDAMAR DA YAƘI DA TSAGERU DA ƁATAGARI

Gwamna Bago ya ɗaura ɗamarar yaƙi da 'yan ta'adda

13
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

GWAMNAN JIHAR NIGER YA ƘADDAMAR DA YAƘI DA TSAGERU DA ƁATAGARI

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
Gwamna Bago ya ɗaura ɗamarar yaƙi da ‘yan ta’adda

Gwamnan Jihar Niger, Umar Muhammad Bago ya ƙaddamar da tsattsauran yaƙi da tsageru, ‘yan ta’adda da kuma ɓatagari.

Gwamnan ya ƙaddamar da sababbin dokoki ne a kan haka, waɗanda a cewarsa, za su taimaka wajen daƙile duk wata fitsara da barazanar tsaro a jihar. Haka kuma ya bayyana cewa dokokin zasu fara aiki nan take a faɗin jihar.

A cikin dokokin, Gwamnatin jihar ta Niger ta haramta bangar siyasa da duk wani abu mai kama da haka a faɗin jihar.

A tsarin dokokin, duk wanda aka same shi da wani makami da ya haɗa da wuƙa ko sanda, za a ɗauke shi a matsayin ɗan fashi da makami, idan kuma ya yi gardama da jami’an tsaro aka harbe shi da bindiga, to ba za a miƙa shi ga ‘yan uwansa ba, har sai sun biya kuɗin wannan alburushi da aka harbe shi da shi.

Duk wani namiji da aka samu da kitso ko dada a kansa, za a kama shi a kuma aske kan nasa.

An haramta amfani da babur da Keke-Napep daga ƙarfe shida na yamma zuwa shida na safe.

Wasu daga dokokin sun haɗa da cewa, duk wani mai Unguwa, Dagaci ko Hakimin da aka samu yana ɓoye ‘yan bangar siyasa, za a tsige shi kuma a kama shi. Duk wani gida da aka samu suna sayar da kowane irin nau’in kayan maye, za a rushe shi kuma a kama duk wanda aka samu a gidan.

Domin aiwatar da waɗannan sababbin dokoki, za a kafa kotu ta musamman ƙarƙashin kulawar babban Alƙalin jihar, wacce za ta kula da hukunta ‘yan bangar siyasa tare da tasa ƙeyarsu zuwa waƙafi. Jami’an tsaro za su sanya idanu sosai a wuraren da suka yi ƙaurin suna wajen aikata laifuka.

Haka kuma, duk wata mota da za ta shiga Babban Birnin Jihar Niger, wato Minna, idan aka same ta da duk wani nau’in kayan maye, za a ƙwace ta a sanya ta cikin asusun gwamnatin jihar.

Waɗannan tsauraran dokoki, ana sa ran za su magance matsaloli da barazanar tsaro a jihar.
______
Jama’a, mene ne ra’ayinku game da wannan babban mataki na Gwamnan Jihar Niger, Umar Muhammad Bago? Ku bayyana a Comment Section:
👇

Previous Post

TA’AZIYYAR PAPAROMA FRANCIS: SHIN INA LAIFIN PANTAMI?

Next Post

A 2027 Talakawan Najeriya Za Su Nuna Wa Tinubu Iyakarsa –  Aminu Waziri

Related Posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Babban Labari

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume
Babban Labari

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel
Babban Labari

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

April 2, 2026
Next Post
A 2027 Talakawan Najeriya Za Su Nuna Wa Tinubu Iyakarsa –  Aminu Waziri

A 2027 Talakawan Najeriya Za Su Nuna Wa Tinubu Iyakarsa -  Aminu Waziri

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Littafin Bango Ya Tsage: Takaitaccen Tsokaci Da Shawara

Littafin Bango Ya Tsage: Takaitaccen Tsokaci Da Shawara

August 28, 2023
Johann Ya Doke Dangote: Shi Ne Ya Fi Kowa Kuɗi A Afirka

Johann Ya Doke Dangote: Shi Ne Ya Fi Kowa Kuɗi A Afirka

June 21, 2023
Sojoji Sun Bankaɗo Kamfanin Ƙera Bindigogi A Kafanchan

Sojoji Sun Bankaɗo Kamfanin Ƙera Bindigogi A Kafanchan

September 24, 2023
₦16,000 Za Mu Sayar Da Taki A Jigawa – Gwamna Namadi

₦16,000 Za Mu Sayar Da Taki A Jigawa – Gwamna Namadi

July 26, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Mu Ji Tsoron Allah
  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Mu Ji Tsoron Allah

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.