• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, June 18, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

IDAN APC TA AMSHI KANO: INA MAKOMAR SARAKUNA BIYU?

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
April 17, 2025
in Gizago
0
IDAN APC TA AMSHI KANO: INA MAKOMAR SARAKUNA BIYU?

Ina makomar sarakunan Kano?

5
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

IDAN APC TA AMSHI KANO: INA MAKOMAR SARAKUNA BIYU?

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa

Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa

June 16, 2026
A Yayin Da Aka Kashe Janar Saura Wa Kuma Ya Rage?

A Yayin Da Aka Kashe Janar Saura Wa Kuma Ya Rage?

June 14, 2026
Ina makomar sarakunan Kano?

Wani babban al’amari da ya daɗe yana ɗaukar hankalin al”umma a Jihar Kano, shi ne tataɓurzar Masarautar Kano, inda sarakuna biyu ke ta sañatta-juyatta da juna.

A gefe guda, akwai Sarki Aminu Ado Bayero, wanda Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta sauke. Sai kuma ɗaya gefen, na Sarki Muhammadu Sanusi II, wanda gwamnatin ta dawo da shi bisa karaga, kasancewar tsohuwar Gwamnatin Jihar Kano, a ƙarƙashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta sauke. Al’amarin da ya kawo rarrabuwar kai, ya kawo hautsini, kuma ake ta fafata Shari’a a kansa.

Babban abin da ya haifar da wannan matsala shi ne, yadda aka samu al’amarin na Masarautar Kano ya faɗa komar siyasa da ‘yan siyasa. A lokacin da Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta NNPP, bisa jagorancin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ke goyon bayan Sarki Muhammadu Sanusi II, ita kuma Gwamnatin Tarayya ta APC, bisa sahalewar Shugaban Jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, take goyon bayan Sarki Aminu Ado Bayero.

A yanzu da ake tsammanin wani sabon al’amari zai gudana a siyasance a Jihar Kano, akwai yiwuwar kawo ƙarshen wannan taƙaddama da ta baibaye Masarautar Kano. Wannan kuwa shi ne, jita-jita ta yi tsauri, cewa Madugun Kwankwasiyya, Injiniya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai koma Jam’iyyar APC, inda zai haɗe da tsohon mataimakinsa, wanda suka raba gari da juna, wato Abdullahi Umar Ganduje.

Kasancewar ɗaki ba ya tashi ragaya ta zauna, ana sa ran idan Kwankwaso ya shiga APC, to kuwa Gwamna Abba Kabir Yusuf ma, tare da ayarinsa ‘yan Keankwasiyya su ma za su koma APC. Ke nan Jihar Kano za ta koma hannun Gwamnatin Tarayya, ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Hakan zai sa a ɗinke, a zama ɗaya – babu adawa ko tsama ke nan a siyasance.

Idan haka ta faru, to ina makomar sarakunan nan biyu da ke gwara kan juna, wato Sarki Sanusi da kuma Sarki Aminu? Shin za a dawo da sauran masarautu biyar ne da aka soke, shi Aminu ya koma Sarkin Bichi, a bar Sarki Sanusi da ƙwaryar Kano, ko kuwa?

Tabbas dai idan Gwamnatin Tarayya ta APC ta karɓe Kano, dole ne a samar da matsaya game da matsalar Masarautar Kano.

Al’ummar Allah, me kuke zaton zai faru da sarakunan nan biyu? Ku bayyana ra’ayinku a Comment Section!
_______________
Bashir Yahuza Malumfashi,Taskar Gizago.

Previous Post

Ƙungiyar BUWDA Abin Alfahari Ce Ga Al’ummar Bura Da Duniya Baki Ɗaya

Next Post

ƊAN IYA MAI ALLAH

Related Posts

Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa
Gizago

Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa

June 16, 2026
A Yayin Da Aka Kashe Janar Saura Wa Kuma Ya Rage?
Gizago

A Yayin Da Aka Kashe Janar Saura Wa Kuma Ya Rage?

June 14, 2026
Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji
Gizago

Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji

June 7, 2026
Next Post
Ɗan'Iyan Galadiman Katsina, Alhaji Shehu Musa Ɗankano

ƊAN IYA MAI ALLAH

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Taron editoci: Tinubu na so a riƙa yaɗa kyawawan labarai don jawo zuba jari a Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai Ya Kafa Kwamitin Wayar Da Kan Al’umma, Cusa Ɗa’a, Kishin Ƙasa Da Kyawawan Ɗabi’u

December 7, 2023
Organized Crime: AANI Calls for Enhanced Collaboration to Combat the Menace in Africa

Organized Crime: AANI Calls for Enhanced Collaboration to Combat the Menace in Africa

October 24, 2023
Shin Ka Kuwa Kalli Fim Ɗin The Lord of the Ring

Shin Ka Kuwa Kalli Fim Ɗin The Lord of the Ring

May 29, 2023
KO YANZU ZA A IYA FARA KARATU A BABBAR KWALEJIN NOMA TA NABANJE – Malam Labiru Ƙafur

KO YANZU ZA A IYA FARA KARATU A BABBAR KWALEJIN NOMA TA NABANJE – Malam Labiru Ƙafur

August 5, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya
  • Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa
  • BARKA DA SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1448 HIJIRIYYA

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya

Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya

June 17, 2026
Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa

Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa

June 16, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.