TSOKACINMU NA YAU (08)
Yau Asabar, 08-Ramadan-1446, Hijirar Manzon Allah (saw), wacce ta yi daidai da 08-Maris-2025, Miladiyya.
Ga tsokacinmu na yau:
“Ya ku ‘yan uwa, tsokacinmu na yau, kira ne a gare mu da mu kasance masu taimakon juna. Abu ne mai muhimmanci, mu waiwayi baya cikin tarihi, mu ga yadda al’ummarmu ta yi zamantakewa da juna cikin taimakekeniya ga juna ta fuskokin rayuwa.
Ta hanyar taimakon juna ne ake saita lamurran rayuwar al’umma. Mai shi yana taimakon mara shi. Wannan zai samar da ƙauna da soyayya a cikin al’umma kuma hakan zai kawar da gaba da ƙyashi da hassada a cikin al’umma.
Haka kuma, taimakekeniyar juna hanya ce ta samar da zaman lafiya da farin ciki tsakanin al’umma. Akwai alheri babba a cikin taimakon juna.”
Allah sa mu dace, Amin.
Mu wuni lafiya.
Naku,
Bashir Yahuza Malumfashi,
Editan Mujallar Taskar Gizago.













