• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, April 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Na Zaune Bai Ga Gari Ba

TSARABAR MATAFIYA

Fa'izah Muhammad Sajoh by Fa'izah Muhammad Sajoh
January 4, 2025
in Adabi
0
One Who Sits Put would Not Know The Town

D-H: Farfesa Sola Akinrinade, Shugaban Ƙungiyar Kwararrun Masana Ta Najeriya (NAL), a yayin da yake miƙa wa Dokta Bukar Usman Lambar Girmamawa ta FNAL. Sai Farfesa Andrew Haruna, Mataimakin Shugaban Ƙungiyar ta NAL yake taimaka wa Shugaban (Agusta 8, 2024).

63
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Na Zaune Bai Ga Gari Ba
Daga Fa’izah Muhammad Sajoh

Fa’izah Muhammad Sajoh

Na zaune bai ga gari ba, in ji masu iya magana. Sai yau na ƙara yarda da wannan karin maganar. Ranar wata Asabar da misalin ƙarfe shida da minti arba’in na yamma (6:40pm), na ci karo da saƙo a akwatin adana saƙonnina na Gimel. Saƙon yana sanar da ni cewa Ƙungiyar Ƙwararrun Masana Ta Najeriya ( NAL – Nigerian Academy of Letters) za ta bai wa shahararren marubucin nan, mai taimaka wa manya da ƙananan marubuta, wato Dokta Bukar Usman lambar karramawa. Bayan na buɗe na karanta, sai na ga cewa za a gudanar taron ne a can Lagos, wato Ikko, a ranar 18 ga watan Agusta, 2024.

Related posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026

Ikon Allah! Ban yi ƙasa a gwiwa ba, sai na aika saƙon cewa lallai ina so in halarta idan an ba ni dama. Duk da kasancewar ban taɓa zuwa Lagos ba kuma ba ni da ɗan uwa ko wani wanda na sani a can; haka na yi karambani da ƙundunbalar amsa cewar zan je. Rikicin duniya ai da mai rai ake yin sa kuma tafiya mabuɗin ilimi ce. Sai dai in da gizo ke saƙar kuma matar za ta kayar da mijin shi ne, ba ni da ko sisi, sannan ban san nawa ba ne kuɗin mota daga Kaduna zuwa Ikko. Amma babu shakka na sa a raina cewa zan je Lagos.

Bayan isar saƙon nawa, sai aka dawo mini da amsa, haɗe da jin daɗin jin cewa zan samu halarta.

Wata ranar Juma’a ina aiki a waje, na shigo ɗaki domin ɗaukar wani abu. Ina duba waya sai na ci karo da alamar cewa Dokta Bukar ya kira ni. Bayan na bi kiran, bai ɓata lokaci ba ya ɗauka ba tare da nuna girman kai ba. Bayan na gaishe shi cikin girmamawa sai yake tambaya ta cewa “ko kin taɓa zuwa Lagos ne?” Na ce a’a. Ya ƙara tambayar cewa “kina da ‘yan uwa a can ne?” Na sake cewa a’a. Shi ne ya sake cewa “na ga kin ce za ki je Lagos, ba kya jin tsoro?” Na amsa da eh! Ya ce “to shi ke nan, na gode.”

Bayan mako ɗaya da maganar, sai aka tura mini adireshin masaukin da aka kama mini a Lagos.

Kwatsam ana cikin haka sai aka fara zanga-zangar yunwa a faɗin Najeriya (#EndBadgovernanceInNigeria), inda a sakamakon haka, kusan kowacce jiha aka kafa dokar hana fita ta awa ashirin da huɗu; ciki har da jihata ta Kaduna.
Duk da haka ban ji gwiwata ta yi sanyi a kan tafiyar ko in fasa ba, sai ma ɗoki da kuma ƙosawar ranar tafiyar ta zo nake yi. Rana ba ta ƙarya. Ranar Talata na shirya da sanyin safiya na fita don zuwa in kama kujera a Garejin Mota na Mando. Bayan kai ruwa rana da sojoji a hanya, a kan ba za su bar ni in wuce ba, daga bisani na samu suka bari da taimakon Katin Shaida (ID Card).

H-D: Mista Hilary Oche, Wakilin Ƙungiyar StandTall Africa Initiative, Fa’izah Muhammad Sajoh, Madina Mamman, Dokta Bukar Usman, Farfesa GMT Emezue da Uwargida Bukky Olonilua.

Wasu matasa na ji suna tambayar wani, cewa ko Lagos zai je. Hakan ne ya ba ni ƙwarin gwiwar tambayar su inda ake hawa motar zuwa Lagos. Ɗaya daga cikinsu ne ya yi mini jagora har cikin tashar. Bayan an gaya mini kuɗin motar, na je shagon POS na cire na biya. Duk da yawan kuɗin motar, sai na raya a raina cewa lallai nisan garin ya ci kuɗin motar da aka yanka mini.

Kasancewar babu manyan motocin Makapolo, motar Homa na biya, aka ba ni rasiɗin shaidar na biya, ina ɗaya daga cikin fasinjoji da za su yi balaguro zuwa Lagos.

Suka ce in je in dawo ƙarfe huɗu na yamma. Ina kan hanyar dawowa gida, sai na tsaya a shagon sayar da magani na sayi ruwan gishiri da suga, kasancewar na yi fama da zazzaɓi a ‘yan kwanakin. Isa ta gida ke da wuya na haɗa ruwan a gora, sannan na shirya jakata, inda na ɗauki kaya kala biyu da sauran tarkace. Na kasa runtsawa – ina Allah-Allah lokaci ya yi. Ƙarfe huɗu saura na yi sallama da iyaye da ‘yan’ uwa. Suka yi mini addu’a da fatan sauka lafiya. Kasancewar ana cikin dokar hana zirga-zirga (curfew), a ƙafa na kusa ƙarasa zuwa tashar; inda a hanya wani soja daga cikin mota ya tsayar da motarmu, ya kira ni. Bayan na isa ya saka wani a gaba ya buɗe mini ƙofa, shi ya ƙarasa da ni tashar. Na je na samu wasu fasinjoji abokan tafiya, har sun ƙaraso.

Ƙarfe tara na dare motar mu ta bar Garejin Mando, bayan dogon zaman jiran da na yi, na kusan awa biyar. Idona biyu har muka kusa shiga Abuja. Direba ya tsaya shan mai, muka sauka muka kama ruwa sannan aka ci gaba da tafiya har muka isa Lokoja ban runtsa ba. Ana ruwa mai ƙarfi a lokacin. Haka muka yi ta tafiya muna wuce garuruwa, wasu ido biyu wasu suna barci. Gab da asuba aka sauke wani fasinja a Ekiti, sannan muka ƙara ɗaukat hanya. Gari ya waye tangaran sai ga mu a Akure Jihar Ondo. Muka sauka muka ba da farali. A lokacin na ji wani sabon zazzaɓi ya dawo mini. Ƙarfe sha biyu na rana muka ƙarasa Ibadan.

Nan ma wasu fasinjojin suka ƙara sauka, mutanen cikin motar na ta ƙara raguwa. Yau ne za mu shiga cikin Lagos, gobe ne, har na ƙosa da zama. Na rasa abin da ke mini daɗi. Sai ƙarfe uku saura motarmu ta samu damar tsayawa a Berger. Na kasa saukowa, domin ƙafafuwana sun kumbura. A haka sai cire takalmi na yi, na sauko ƙasa.

Bayan tambayar inda za ni, kasancewar ina da adireshin masaukina; sannan zamowata baƙuwa a garin da kuma yadda ake ta faɗin tsagerancin garin, don ƙara tsoratar da ni a kan tafiyar, sannan ga shigar da na yi, wadda a kallo ɗaya za ka gane daga in lda na fito, wato Arewa. Amma na haɗu da mutanen kirkin da suka yi mini kwatance har na kai ga masaukina, wato King Celia Hotel. A lokacin agogo ya nuna mini ƙarfe huɗu daidai. Isa ta cikin zauren saukar baki suka karɓe ni da mutunci, bayan na yi musu bayanin kaina da sunana, suka ba ni takarda na yi rubutu a kan sunan nawa sannan suka ba ni mabuɗin ɗakina.

Ina shiga ɗakin na yi arba da gadon da ya sha shimfiɗa fari fat, sai dukkan gajiyata ta dawo, sanyin AC kuma ya taso mini da zazzafan zazzaɓi, har jikina na karkarwa. Da ƙyar na samu na yi odar abinci wanda na kasa cin shi. Bayan na sha magani na kuma samu barci sai na ji na dawo dai-dai.

H-D: Dawn Zaasi Meneh, Deborah C. Uzoma, Hassan A. Kangiwa, Bashir Yahuza Malumfashi, Amos Joshua da Madina Mamman, abokan tafiya da suka halarci bikin karrama Dokta Usman

Washegari bayan mun karya kumallo sai aka kwashe mu zuwa Jami’ar Jihar Lagos, inda za a karrama Dokta Bukar. A wurin na haɗu da sauran abokan tafiya, waɗanda suka haɗa da Bashir Yahuza Malumfashi da Hassan Kangiwa da Bala Mohammed da Anti Madina da sauransu. An ɗauki hotuna bayan an tashi taron, inda Dokta Bukar ya yi matuƙar mamaki haɗe da jin daɗin halartar taron da na yi.
Bayan an mayar da mu masauki aka haɗu a wurin cin abincin rana. Nan ma aka haɗu aka yi ta hira. Kasancewar washegari kowa zai koma garinsu, sai aka yi musayar lambobin waya.
Washegari ranar Juma’a kowa ya bar masauki da misalin ƙarfe sha biyu na rana. Ƙarfe huɗu na yamma motarmu ta baro Lagos zuwa Kaduna. Ba mu samu shiga Kaduna ba sai ranar Asabar da misalin ƙarfe biyu na rana. Lallai na yarda da azancin maganar da ke cewa na zaune bai ga gari ba.

Iyalan Dokta Bukar Usman tare da abokan arziƙi da suka halarci bikin karrama shi. H-D: Hadizat Omolola Usman, Fa’izah Muhammad Sajoh, Madina Mamman, Gbenga Odumewu, MC Muomah, Segun Ajibola, Mista Hilary Oche, Wakilin Shugaban Ƙungiyar StandTall Africa Initiative, Uwargida Raliat Dupe Usman, Dokta Bukar Usman, Zara Oreoluwa Usman, Abdul’Talib S. Umar, Bashir Yahuza Malumfashi, Mista Amos Joshua, Bala Ibrahim Mohammed, Uwargida Olabisi Adenigba da kuma Uwargida Bunmi Odumewu.

Na ji daɗin zuwa Lagos, duk da cewa ban yi yawo a cikinta ba. Ban je wuraren shaƙatawa ba, kasancewar tafiyar ta kwana biyu ce, sannan na so in je in ga teku ikon Allah, wadda shahararren mawaƙin Hausar nan Alhaji Dokta Mamman Shata ya waƙe (Beach). Amma ina ji a raina cewa zan sake ziyartar Lagos kwana kusa, in Allah Ya yarda. Na ji daɗin karamcin da Dokta Bukar ya yi mini da sauran abokan tafiyata. Allah Ya ƙara ɗaukaka.
________________
Fa’izah Muhammad Sajoh
Disamba 21, 2024
Kaduna Najeriya.

Previous Post

One Who Sits Put would Not Know The Town

Next Post

CANJIN ZAMANI: Rayuwar Mata A Ƙarni Na 21

Related Posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza
Adabi

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue
Adabi

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026
Next Post
CANJIN ZAMANI: Rayuwar Mata A Ƙarni Na 21

CANJIN ZAMANI: Rayuwar Mata A Ƙarni Na 21

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Plateau Massacre/American National: Open Letter to the NSA Malam Nuhu Ribadu

Plateau Massacre/American National: Open Letter to the NSA Malam Nuhu Ribadu

March 30, 2026
RAMADAN KARIM: 04-1447

RAMADAN KARIM: 04-1447

February 21, 2026
Taya Ni Mu Gyara: Kisan Baƙi Sai Gayya

Taya Ni Mu Gyara: Kisan Baƙi Sai Gayya

November 1, 2025
NANA Rahma Abdulmajid Ta Bankaɗo Sharrin Hausawan Bogi

NANA Rahma Abdulmajid Ta Bankaɗo Sharrin Hausawan Bogi

December 4, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.