Ƙungiyar Marubutan Nahiyar Afirka (PAWA) Ta Buƙaci Marubuta Su Koma Yin Rubutu A Harsunan Gida
– An Karrama Dokta Bukar Usman, OON
Daga Muhammadl Salissou Hamissou
(Wannan rahoton musamman ne da marigayi Muhammad Salissou Hamissou ya gabatar a Sashen Hausa na Gidan Rediyon Faransa RFi a watan Yuni na shekarar 2022)

A ranar 25-06-2022, Ƙungiyar Marubutan Nahiyar Afirka (PAWA), wacce ta hada ƙasashen Nahiyar Afirka 36, ta gudanar da babban zaman taronta a Birnin Ibadan na Jihar Oyo da ke yankin Kudu Maso Yammacin Tarayyar Najeriya. A sanarwar bayan zaman taron, ƙungiyar ta buƙaci marubutan Nahiyar Afirka da su mai da hankali wajen rubuce-rubucensu a cikin yarukan gida na Nahiyar Afirka. Wannan kuma domin warware ɗaurin tankilan da salon mulkin mallaka ya yi wa sashen al’adu da kuma rubuce-rubucen Nahiyar ta Afirka.
Dokta Bukar Usman Biu, shahararren marubuci ne a Najeriya, wanda kuma ƙungiyar ta karrama shi. Ya yi mana tsokaci a kai: “Dukkan abubuwan da wannan ƙungiya take tattaunawa, wato Ƙungiyar Marubutan Nahiyar Afrika da ka yi magana, su sun yi ta maganar cewa ya kamata a cikin rubuce-rubucen da ake yi, a riƙa yin su a cikin harsunanmu na gida na Afirka. Sun ce ya isa haka nan, ana rubutu da Turanci da Faransanci da Larabci, cewa ya kamata a riƙa yin sa da Swahili da Hausa da sauran yarukan Afirka. Abin da suke son ƙarfafawa ke nan, wato a riƙa yin su da yaruka na gida.”

Wannan mataki, yana nufin warware ɗaurin tankilan da mulkin mallaka ya yi wa fannin al’adu a nahiyar Afirka ne? Dokta ya ce: “Ƙwarai, ƙwarai kuwa, shi ne abin nufi. An ce ya isa haka nan. Wani mutumin Kenya ya yi fushi da yanayin, har ma ya fita daga addinin Kiristanci. Ya yi rubutu da yarensa na mutanen Kenya – yanzu ya yi wajen shekara fiye da 20. Ya ce ya yi fushi kuma ya isa haka nan yadda ake rubuce-rubuce, a wancan zamani na baya cikin harsunan waje. Ya ce batun ’yanci ba yana nufin samun ’yanci na siyasa kaɗai ne ba. Wajen al’adu ma ya kamata a samu ’yanci. Ya ce kuma idan mutum yana rubutu, to ya fi tasiri ya yi shi da yaren gida. Abin da yake nufi ke nan.”
To mene ne fatanka ga ire-iren marubuta masu yin rubutu a yaren gida a Tarayyar Najeriya da ma sauran ƙasashen na Afirka? Dokta Usman ya ce: “Eh, ni na goyi bayan batun wannan ƙungiya, cewa ya kamata a riƙa yin rubuce-rubuce da wasu yarukan gida. Misali, su yanzu mutanen ƙasar Sin da Jamus da sauransu, ba da yarukansu suke rubutu ba? To me ya sa mu za mu kasa yin rubutu da namu yarukan? Wajen rubutu idan ka rubuta da harshenka na gida, ya fi kaifafa tunani fiye da idan ka yi da yaren wasu ƙasashen daban. Ya kamata mu ma mu tashi tsaye. Abin da yake hana mu a Najeriya yin haka, saboda yawan yaruka wajen fiye da 250. Muna tunanin shin da wanne za a riƙa yin rubutun? Wannan shi ne abin da yake ɗan taka mana burki. Idan ba haka ba, ai mutane suna son lallai a riƙa yin rubutu da yarukan gida.”

Ba ka ganin wani zai iya cewa fa wataƙila lokaci ya ƙure? Yaya kake gani ko kuma me za ka ce game da wannan hangen? Ya amsa cewa: “Ya ƙure wa su wa? Idan dai mu ne kam, a yanzu shekaruna wajen 80 a ƙarshen wannan shekara, za ka iya ce mani wataƙila lokacin ya ƙure amma dai akwai mutane masu tasowa nan gaba, yaya za a ce masu lokacin ya ƙure? Duniya za ta tashi ne kwanan nan? Wa ya gaya maka cewa duniya za ta tashi a kwanan nan? Akwai shekaru masu yawa a nan gaba. Saboda haka babu wani lokacin da ya ƙure, babu batun ƙurewa sam. A gare mu dai za a iya cewa ya kusa ƙurewa amma wasu masu tasowa, ba haka ba ne.”
Richard Ali A Mutu K, marubuci kuma Shugaban Ɗakin Karatu na Gidauniyar Wallonie- Bruxelles da ke Birnin Kinsasha a Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Kongo; ya ce ai faɗuwa ce ta zo daidai da zama, wajen ɗaukar wannan mataki na komawa rubutu cikin harsunan Afirka.
“Batun yin rubutu a cikin yarukan Afirka, faɗuwa ce ta zo daidai da zama, domin ni da kaina marubuci ne na ƙasashen Ƙungiyar Francophone (Ƙungiyar Ƙasashe Rainon Faransa). Ina rubutu a cikin yaren Faransanci, haka kuma da na Lingala. Lingala yare ne da ya samu ɗaukaka sosai a yankin Tsakiyar Afirka, a shekara ta 1994. Na samu damar rubuta littafi da yaren Lingala da ake kira Ebamba Kinsasha makambo (Isolo) kuma ta sanadiyyar wannan littafi ne aka taɓa gayyata ta a Tarayyar Najeriya, a Fatakwal, inda na gabatar da wannan littafi a ƙarƙashin Taron Tarihin Afirka na 39. Don haka wannan taro mai girma ne kuma maudu’in yana da ƙarfi. Domin idan marubutan Nahiyar Afirka suka haɗa kansu, to ina tsammanin a matsayinsu na waɗanda ake ɗauke masana, idan har muka koma yin rubutu a cikin yaruka na Afirka; ina ganin gudunmowa ce mai karfi. Idan kun lura, yarukan da aka ɗauka a Ƙungiyar Nahiyar Afirka, Swahili, Ingilishi, Larabci da Fortugese amma wani lokaci ana ɗar-ɗar ɗin saka wasu yarukan Afirka. Ana iya cewa wannan mataki ne na ƙara warware igiyar mulkin mallaka daga wuyan Nahiyar Afirka. Za a iya cewa haka ne, ganin cewa shekaru sittin da suka gabata, har yanzu ana ɗari-ɗari da saka yarukanmu a matsayin yarukan aikin hukuma. Wannan ina ganin abin mamaki ne. Shekaru sittin bayan samun ’yancin kai, ya kamata a yau a ƙasashen Afirka, a samu yarukan Afirka da ake amfani da su a matsayin yarukan aikin hukuma. A Najeriya, bai kamata a ji kunyar ɗaukar Yarabanci a matsayin yaren hukuma ba. A Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Kongo, bai kamata ba a ji kunyar ɗaukar Lingala a matsayin yaren hukuma da za a riƙa aiki da shi a Majalisar Dokoki. Ina zaton yanzu da marubuta suka fara aiki da yarukan gida, to wannan babbar alama ce mai armashi. Shekaru masu zuwa, na yi amanna cewa marubutanmu na Afirka za su rubuta yawancin littattafansu ne a cikin yarukan Afirka da suka kasance na gado, waɗanda al’ummomi ke magana da su a kowane lokaci. Don haka ina zaton wannan Ƙungiya ta Marubutan Nahiyar Afirka ta shiga cikin wani babi mai matuƙar muhimmanci. Ina kuma ganin za mu samar da tarihi mai ƙarfi, wanda zai sanya a tuna da wannan Ƙungiya. Mun gode, ni ke maku godiya.”

Da aka ƙara juyowa kan Dokta Usman kuwa, an sake tambayarsa cewa, kana cikin waɗanda Ƙungiyar Marubutan Nahiyar Afirka ta karrama da lambobin yabo; yaya ka ji da wannan kyauta? Shi kuwa sai ya amsa da cewa: “Sai in ce ina gode wa Allah Ubangiji da Ya ba ni wannan dama ta karɓar wannan karramawa. Ban yi zaton zan samu ba, sai kawai mako uku zuwa huɗu da suka gabata, na samu wannan wasiƙa, wadda Babban Sakatare na wannan Ƙungiya ya kawo mani a Abuja. Na yi masa godiya kuma na karɓa.”
Ko sun faɗa maku dalilin da ya sanya suka ga ya dace su karrama ku? “Abin da suka ce mani da Turanci, suna son su karrama ni saboda ƙoƙarin da nake yi na taimakon harkar rubutu da abubuwan gargajiya, ba na Najeriya kawai ba, har duka Afirka. Abin da suka ce mani ke nan.”
Akwai muhimmin aikin da kuka yi na kammala Taskar Tatsuniyoyi. Ke nan suna yin tsokaci a kai? Ya ce: Taskar Tatsuniyoyi yana ɗaya daga cikinsu amma sun duba dukkan rubuce-rubucen da nake yi. Suna da kwafi na littattafaina, kuma sun baza su a zauren baje koli, tare da na sauran mutanen da suka rubuta. To shi dai Sakatare Janar, Honorabul Wale Okediran ya samu kusan dukkan littattafaina da na buga, fiye da 20 zuwa 30, yana tare da su.”
Daga cikin ayyukan da kuka yi, akwai fassara ko rubuta tatsuniyoyi a cikin wasu yaruka daban-daban na Najeriya, waɗanda kuka yi niyyar yi. To ina aka kwana a nan? Dokta ya bayyana cewa: “A cikin littattafan da na rubuta, an fassara su, wasu na rubuta a cikin Hausa kuma waɗanda na rubuta a cikin Turanci, wasu sun fassara. Akwai kuma wasu ’yan ƙasidu da na yi, waɗanda na ba da a yi mani fassara a harshen Igbo da Yarabanci. Ina fata kafin shekarar nan ta ƙare, za a buga su. ’Yan ƙanƙananan littattafai ne amma dai an yi su a wasu yare, ban da Hausa da Turanci.”
______________
Jama’a masu saurare, da wannan tattaunawa ta Dokta Bukar Usman muka kawo ƙarshen shirin namu. A madadin ɗaukacin waɗanda aka ji muryoyinsu a cikin shirin, da Richard Ali Mutu K, marubuci a Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Kongo, ni Muhammad Salissou Hamissou tare da ɗaukacin Sashen Hausa na Radio France International (RFi) ke cewa da ku Bissalam, a huta lafiya.











