• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, April 6, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

ZINATU MATAR GWANMA (1)

ƘIRƘIRARREN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
January 7, 2024
in Adabi
0
ZINATU MATAR GWANMA (1)

Zinatu Matar Gwamna

66
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

ZINATU MATAR GWANMA (1)

~~~
✓Daga Alƙalamin Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026

✓Za a riƙa tsakura littafin nan a kowace LAHADI.
✓Za ku iya sauraron karatun littafin nan a tashar YouTube ta @taskargizago
~~~
_____________
Babi Na Ɗaya
—————

Zaune take bisa ’yar ƙaramar kujerar mata. A gabanta, tsibin kwanukan abinci ne tare da tukwanen da ke danƙare da ƙanzo, ƙudaje na ta shawagi bisansu. Zinatu ta ƙura masu hajar mujiya kamar mai zullumin wanka. Ga dukkan alamu, hankalinta ba ya kan wannan tsibin kayan wanke-wanken da ke gabanta. Babu shakka akwai wani abu muhimmi da ya ɗauke mata hankali kuma take tunaninsa.

“Saboda me za a matsa mani kan maganar aure, alhali ba kaina farau ba? Ko kuwa dai an gaji da ni ne a gidan nan?”

Tunaninta ya gawurta, ya rikiɗe daga na zuciya zuwa magana. Ta samu kanta cikin furta wasu kalamai ita kaɗai kamar zautatta. Ita kaɗai take magana, babu kowa kusa da ita, in ban da waɗannan tsibin kwanoni da ke gabanta, suna jiran wankewa.

“…Ko kuwa dai ni ba ɗiyar gidan nan ba ce, ko ba inna da baba ne suka haife ni ba?”

Ta ci gaba da magana a fili. “To, idan ba haka ba, yaushe za a maida ni kamar wata baiwa? Kullum ni ake tara wa duk wani aikin gida. Sannan ga shi an tsangwame ni da faɗa da tsegumi, wai na ƙi yin aure; kamar so ake in kai kaina talla kasuwa!”

Cikin alamar damuwa da ɓacin rai take waɗannan kalamai.

“Ke sababba, ke za mu jira ko kuwa? Kin tasa kwanoni gaba kin ƙi wankewa, ko kuwa ni kike jira in wanke maki?”

Wannan magana mai kama da tsawa, ta sanya Zinatu ta yi firgigi, kamar wacce aka tada daga barci da ruwan sanyi.Ta waigo cikin kaɗuwa, idanunta suka yi arba da Tabawa, mahaifiyarta.

Nan take ta dawo cikin hayyacinta. Cikin ƙanƙanen lokaci ta ankara da cewa, ashe tun ɗazu mahaifiyarta ta gargaɗe ta da cewa ta wanke kwanonin da sauri, domin ta samu damar gama girkin abincin dare da sauri saboda tana son zuwa barkar haihuwa. Yanzu ne Zinatu ta gane cewa, ashe ta ɗauki dogon lokaci, kusan awa biyu tana zaune, ba ta taɓuka komai ba.

“Inna, don Allah ki yi haƙuri, kaina ne ke ɗan sarawa, ba na jin daɗi.” Ta yi ƙarya da gangan.

“Ai kuwa lokacin da kika naɗe ƙafa kina shara loma ɗazu, ai kan naki bai sara ba ko, sai yanzu? To, ki shiga taitayinki, kada ki ƙure ni!”

Tabawa ke nan cikin fushi, tana riƙe da wata doguwar tsintsiyar kwakwa a hannu; a yayin da ta daka wa ɗiyar tata harara. Ɗaure take da wani zane na kamfala, yana ɗauke da dauɗa, kamar ya shekara bai ga ruwa ba. Sanye a jikinta kuwa, wata riga ce ta gwanjo, mai kalar ɗorawa amma dauda ta ci ƙarfinta, har ta canza kala zuwa ruwan makuba-makuba. Bakinta kuwa ya yi dashasha da goro!

“Sau nawa na gaya maki cewa ki wanke kwanonin nan da wuri? Ina son kafin magariba in gama tuwon nan, domin ina da uzuri amma ke ga ki ’yar laushi, kin samu wuri, kin rashe, kina sharholiya.”

Ta ɗan dakata, sannan ta ci gaba.“Ni, yanzu ma na fara gane gaskiyar Malam, da kullum yake tsegumin kin ƙi aure ne saboda ɗan Turancin angulun da ke cikin kanki. Shi ke nan ba ku son aiki, don gadarar kun yi karatun zamani?”

Zinatu, babu abin da ke ƙara dugunzuma mata rai kamar irin wannan ƙorafi. Yanzu ma ji take kamar an yafa mata wuta. Wani gululun baƙin ciki ya tokare mata maƙogwaro. Ba ta koma batun Tabawa ba sai ta fizgo kwano ɗaya ta fara wankewa. Mahaifiyarta kuwa ta shuri takalma, ta qara gaba, bayan ta doka mata wani uban tsaki.

Tana ƙwalla ta gama ɗimbin wanke-wanken nan amma yaya za ta yi da ranta? Nan dai gidansu ne kuma iyayenta ne take tare da su, ba wasu bare ba. To, amma saboda me mahaifiyarta ke mata gorin abinci? Wannan abu yana ɗaure wa Zinatu kai matuƙa.

Duk da cewa ta kammala wanke-wanken kwanonin, sai ta samu kanta zaune a kujera, ta kasa tashi daga wurin. Wannan abin baƙin ciki da ke dabaibaye ta, ya saka ta cikin ƙunduttu. Dalili ke nan ya sanya ta ci gaba da tunano hirar da suka yi jiya da ƙawarta.

Ƙawarta ce Balaraba ta ƙara tabbatar mata da cewa, lallai ita da samun sauƙin irin waɗannan tsegunguma sai ta yi aure ko kuma wani sanadi ya zo, yadda za ta rabu da iyayenta.

~~~~~~~
Za mu ci gaba a ranar Lahadi in sha Allahu. Ku ci gaba da bibiyar mu.
~~~~~~~

Previous Post

ZUMUNCI: Ƙungiyar Ɗalibai Ta Karrama ACC Tasi’u Saulawa

Next Post

BADAƘALAR NAIRA MILIYAN 585: Gwamnati Ta Fara Binciken Ministar Agaji – Idris

Related Posts

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue
Adabi

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)

March 1, 2026
Next Post
Kasafin 2024 Ya Fitfita Jaddada Ajandar Sassaita Nijeriya – Idris

BADAƘALAR NAIRA MILIYAN 585: Gwamnati Ta Fara Binciken Ministar Agaji - Idris

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

HAWAYE DON AFIRKA

HAWAYE DON AFIRKA

August 16, 2023
Women Group Congratulates Hon. Rabi Salisu

Women Group Congratulates Hon. Rabi Salisu

September 14, 2023
Jihar Katsina Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Daminar Bana

Jihar Katsina Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Daminar Bana

July 9, 2023
Zaɓen gwamna: Mutum 2,318,919 za su yi zaɓe a Imo, 1,833,160 a Kogi, 1,017,613 a Bayelsa, inji INEC

INEC Ta Yi Wa Daraktocin Hukumar Huɗu Ritayar Dole

December 28, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)
  • JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles

Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles

April 5, 2026
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)

April 4, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.