• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Wednesday, April 15, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (2)

RAHOTON ZIYARA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
December 13, 2023
in Babban Labari
0
BIU: A Visit to a City on a Plateau (2)

Mai Martaba Sarkin Biu, Mai Mustapha Umar Mustapha II

12
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (2)

Daga hagu, Laftanar-Janar Tukur Yusufu Buratai (mai ritaya) da Laftana-Janar Faruk Yahaya (mai ritaya), a yayin bikin karrama Buratai a naɗin Sarautar Betaran Biu

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026

~~~~~~~

Yadda Na Sauka Garin Biu:

Kamar yadda na bayyana a kashi na farko na wannan rahoton, na sauka garin Biu ne a ranar Laraba, 10-04-1445 (Hijriyya), daidai da 25-10-2023 (Miladiyya). Na sauka daga mota daidai misalin ƙarfe 7:30 na dare, lokacin dai an kammala Sallar Isha’i a mafi yawan masallatan unguwar da na sauka. Na samu tarba daga aboki mai zumunci da karimci, Malam Umar Mohammed Maidala.

Amma ko yaya tafiya ta kasance daga Abuja zuwa Biu? Lallai abu ne mai kyau, in ɗan koma baya, yadda muka kwashe tsawon yini guda cur a kan hanya. Tun da farko dai ban taɓa zuwa Biu ba a rayuwata, sai a wannan karon kodayake na taɓa zuwa wasu garuruwa a cikin jihohin da ke maƙwabtaka da Biu ko Jihar Borno. Misali, na sha zuwa Gombe da Bauchi.

Tun kafin ranar da zan yi wannan tafiya na yanke hukuncin cewa ba zan tafi da motata ba, musamman saboda dalilai kamar biyu zuwa uku. Na farko dai ga tsadar man fetur. Na biyu ga shi ban san yanayin hanyar ba. Don haka lallai ne in fuskanci matsaloli, idan na ce zan ɗauki motata in saka hanya. Dalili ke nan na yanke hukuncin shiga motar haya kuma tuni aka sanar da ni cewa idan na je Nyanya/Mararraba a Jihar Nasarawa, zan samu motar zuwa Gombe, daga nan kuma in samu wacce za ta kai ni Biu.

Tun da asubahin fari, daidai misalin ƙarfe 5:40, bayan kammala Salla na samu mai acaɓa da ya kai ni tashar motar Zuba, inda na samu mai tasi ya kai ni Nyanya. Daga nan wani ɗan acaɓar ya ƙarasa da ni zuwa tashar motar Sani Abacha Terminal. Ina zuwa ’yan kamasho suka taso haiƙan a kaina, suna ƙoƙarin amsar mani jikka tare da tambayar inda za ni. Na yi zaton ba zan samu motar Biu ba kai tsaye, don haka na shaida wa ɗan kamasho na farko da ya amshi jikkata, cewa Gombe za ni. Har mun shiga tasha, sai wani ɗan kamashon ya rugo yana cewa “Biu, Biu ne, Alhaji?”

Ni kuma ina jin ya ambaci sunan Biu, sai na ce ƙwarai kuwa, Biu zan je. Nan take ɗan kamasho na farko ya murtuke fuska, ya ɓata rai, domin kasuwarsa ta ɓaci. Nan take ya miƙa jikkar tawa ga mai lodin Biu. Lokacin da muka isa zuwa motar da ke lodin farko, sai muka iske ta cika. Sai aka saka wata Sharon, aka amshi Naira 13, 200, aka ba ni rasiɗi. Na ce to me ya kawo ɗoriyar Naira 200 kuma? Sai suka ce wai ta harajin tasha ce. A raina na ce, har fasinja ma sai ya biya harajin tasha? Daidai misalin ƙarfe 8:00 na safe muka kama hanyar zuwa Biu.

Direban, wani ɗan tsattsaura ne da ake kira da suna Ɗanfulani. Yana da himma sosai kuma ya iya tuƙi, kamar kuma yadda na fahimta da cewa ya naƙalci hanyar nan sosai. Wani abin mamaki shi ne, duk da cewa daban-daban muka shiga motar amma sai abin ya zama kamar arashi, domin kuwa kusan dalili ɗaya ne ya sanya mu zuwa Biu a wannan lokaci – bikin naɗin sarauta ga wasu muhimman mutane uku da mai martaba Sarkin Biu, Mai Mustapha Umar Mustapha II zai gabatar, cikinsu har da Laftanar-Janar Tukur Yusuf Buratai, wanda aka naɗa a sarautar Betaran Biu. A motar akwai sojoji uku zuwa huɗu, akwai jami’in Hukumar Kare Hadurra ta Ƙasa, akwai wata ‘yar jarida ɗaya, sai kuma ni ma ɗan jarida.

A gaban motar, mutane biyu ya kamata a sanya amma wani muhimmin mutum ya biya ya zauna shi kaɗai tare da direba. Bayan tafiya ta yi nisa, sai muka fahimta da cewa ashe tsohon Daraktan Hukumar Matasa ‘Yan Hidimar Ƙasa ne, Janar Muhammad Fada. Shi ma zai je Biu ne domin wannan hidima ta naɗin sarauta. Ya ce ya zaɓi ya yi tafiya a motar haya ce, domin ya samu abokan hira, maganin kaɗaici. Ai kuwa mun ga karimci a tattare da shi, domin kuwa duk inda muka tsaya da nufin sayen wani abin ƙwalama, shi yake saya mana. Kuma ya taimaka mana sosai wajen shingayen jami’an tsaro da ke hanya. Duk inda muka je, da ya lura za a ɓata mana lokaci, sai ya nuna sanayya, sai mu wuce.

Tafiyarmu ta yi armashi kuwa, domin ba mu samu wata matsala ba a hanya. Wani abu da na lura da shi, shi ne garuruwan da ke kan hanyar zuwa Biu tun daga Abuja, suna da wani yanayi mai kama da juna – duwatsu da tsaunuka. A Jihar Nasarawa, mun wuce ta Keffi, Akwanga, Gwantu da Fadan Karshi. A garin Riyom na Jihar Filato kuwa na riƙa ganin mata da maza, yara da manya a gonaki suna aikin acca, wasu gonakin kuwa suna aikin bugun shinkafa.

Daidai misalin ƙarfe 11:36 na safe muka isa Jos, inda ƙwararren dirbanmu ya shiga da mu ta hanyar kewayen gari, hanya mai kwanoni da yawa. Haka muka wuce muna hango dam ɗin Lamingo. Ga shuke-shuken furen-rana (sunflower) da suka ƙawata wasu wuraren, gwanin ban sha’awa. Mun tsaya a wani gidan mai a Jos, inda muka yi karin kumallo. Mun ci gaba da tafiya, har muka kai Tsaunin Fanshanu, wanda na samu bayanin Hukumar Kula Da kayan Tarihi ta Ƙasa ta ayyana shi a matsayin kayan tarihi na ƙasa a shekarar 1956. Akwai maganganu da yawa na tarihi game da wannan tsauni.

A haka muka shiga Jihar Bauchi ta garin Tilden Fulani, muka miƙa har Zaranda. Muka shiga Jihar Gombe daidai misalin ƙarfe 4:16, inda muka tsaya gidan man Barkidi Oil Nig. Limited. Nan muka yi sallolin Azahar da La’asar, a masallacin da ke gidan man. Ga masallaci an kintsa amma babu ruwan alwala. Sai da Janar Fada ya aiki ɗaya daga cikin sojojin da ke tare da mu, ya sayo mana ruwan leda, muka yi alwala da shi.

A haka muka ci gaba da tafiya, har muka zo inda ake aikin hanya, dole sai a hankali tafiya. Ga dare ya fara kawo jiki, ga shingayen jami’an tsaro masu tantancewa da binciken motocin da ke safara a hanyar. Ba mu muka samu sauƙi ba, har sai da muka isa garin Kwaya Kusar, daidai misalin ƙarfe 6:27. Daga ƙarshe dai mun isa garin Biu lafiya, daidai misalin ƙarfe 7:30.

Abubuwan Mamaki Da Na Fara Karo Da Su A Biu:

Kamar yadda na ambata a baya, ban taɓa zuwa garin Biu ba sai a wannan karon. Sai dai kuma na sha jin labarin garin tun shekaru masu yawa a baya, musamman abin da ya shafi mashahuran mutane masu kyawawan al’adu da sauran bayanai amma ban taɓa sanin cewa zan samu garin yadda na same shi ba.

Ni dai na san cewa Biu ɗaya ne daga cikin manyan ƙananan hukumomin Jihar Borno, don haka na yi zaton matsayinta ba zai wuce ƙaramar hukuma ba, kamar yadda sauran ƙananan hukumomi suke a sauran garuruwan Arewa. Amma abin mamaki sai na ga gari hamshaƙi, kamar babban birnin wata Jiha. Kasancewar da dare na isa garin amma saboda wadatar hasken lantarki, sai ka ce rana ce – ko’ina haske fayau, gwanin ban sha’awa! Ga hanyoyin cikin gari male-male da kwalta, ababen hawa na ta karakaina.

Wani abin mamaki da na ƙara lura da shi a Biu da mutanensa, shi ne mutane ne masu martaba baƙi. Na ankara da haka tun a cikin motarmu, wato direban namu da kuma wasu daga cikin abokan tafiyar tamu, waɗanda ‘yan Biu ne. Sun yi ta haba-haba da ni cikin mutunci da karimci. Haka ma yadda abokina, Malam Maidala ya amshe ni cikin karimci, abin ya ba ni mamaki. Tun kafin ya raka ni zuwa masauki, sai da ya kai ni gidan abinci na zamani. Na ci abinci tare da farfesun kifi mai daɗi. Na samu masauki a Yamele Otel da ke titin Damaturu.

~~~~~~~
A rahoto na uku, zan zayyano sauran abubuwan mamaki da na ci karo da su a Biu. Sun haɗa da yanayin tsaftarsu, kyan gari da tsarinsa, kishin ƙasa da addini na mutanen da kuma yadda suke da son zaman lafiya.
~~~~~~~

Previous Post

BIU: A Visit to a City on a Plateau (2)

Next Post

Kasafin 2024: Majalisar Dattawa Ta Buƙaci A Ƙara Wa Ma’aikatar Yaɗa Labarai Kuɗi

Related Posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Babban Labari

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume
Babban Labari

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel
Babban Labari

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

April 2, 2026
Next Post
Kasafin 2024: Majalisar Dattawa Ta Buƙaci A Ƙara Wa Ma’aikatar Yaɗa Labarai Kuɗi

Kasafin 2024: Majalisar Dattawa Ta Buƙaci A Ƙara Wa Ma'aikatar Yaɗa Labarai Kuɗi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Barkwancin Ƙarshen Mako

Barkwancin Ƙarshen Mako

June 25, 2023
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (8)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (8)

July 10, 2025
SUBHANALLAHI: ‘Yan Sanda Sun Kulle Danladi Haruna

SUBHANALLAHI: ‘Yan Sanda Sun Kulle Danladi Haruna

October 7, 2023
NIJER DA ECOWAS DA NIGERIA: Wani Nazari Na Musamman

NIJER DA ECOWAS DA NIGERIA: Wani Nazari Na Musamman

August 13, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye
  • Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
  • MARTABAR MANZON ALLAH (SAW)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.