• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, June 13, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

SUBHANALLAHI: ‘Yan Sanda Sun Kulle Danladi Haruna

Danladi Z. Haruna by Danladi Z. Haruna
October 7, 2023
in Adabi
0
SUBHANALLAHI: ‘Yan Sanda Sun Kulle Danladi Haruna

Haruna Ɗanladi

42
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

SUBHANALLAHI:
‘Yan Sanda Sun Kulle Danladi Z. Haruna

~~~~~~~
A bara cikin watan Agusta, tsautsayi ya haifar da shiga ta gadirum a karo na farko. Ni da nake daya daga wadanda aka yi wa sata, sai mutanen unguwa ke zargin wai na saki barawon da suka kama. Magana har gaban kotu. Mai shari’a ya kori karar saboda rashin abin kamawa, tare da taimakon lauyoyi uku da suka tsaya min.

Related posts

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

June 8, 2026
ALHAMDU LILLAH

ALHAMDU LILLAH

May 15, 2026

Tun farko a wajen ‘yansanda bayan doguwar magana, aka jefa ni gadirum saboda wai kada na gudu. Ina shiga na tarar da mutum bakwai kowa a takure. Sai dai cikinu akwai wani ƙato da ya zage ƙwanji yana ta jibgar wani ƙaramin yaro. Shi kuma yaron yana ta tsiwa da zage-zage. Ƙaton nan dukansa yake tun ƙarfinsa amma babu wanda ya kula cikin mutane da ke wajen. Wani ma na can gefe ya duƙunƙune. Sai idan titirniyar ta faɗo kansa ne yake kaucewa gefe daya yana gurnani.

Abinka da sarkin kankanba. Da ganin ana irin wannan aika-aika sai na tsunduma ciki ka’in da na’in. Da farko na soma da zagin yaron ina masa tsawa kan ya yi shiru shi kuma yana dagewa. Sai nima na rufa na bi sawun wanda ke jibgar tasa. Amma fa dabara na yi, idan katon ya kai naushi sai na tare shi. Ni kuma sai na kai wa yaron bugu mara zafi. Shi kuma yaron sai ya ture ni.

Duk lokacin da na tare dukan katon nan, sai na ji kamar buhun siminti aka jefo min. Duk da haka na hana bugun nasa ya samu yaron. Ni kuma sai na takarkare kamar gaske na kai wa yaron naushi amma bana yarda na same shi. Ina yi ina surutu ina aibata yaron da yawan tsiwa.

Da ƙaton nan ya fahimci abin da nake yi, sai cakumi ƙuguna. Ni dai ban san yadda aka yi ba, sai na ji an yi sama da ni kamar filfilwa. Na ji an yi gaba da ni, sai na ji an dawo da ni baya. Sai ga ni jikin wanda ya takure din nan kaina ya naushi hakarkarinsa.

Na yi zumbur na mike tsaye, mu uku duka kowa ya galabaita sai huci yake kamar zakaran da ya kasa ƙoto. Na dubi yaron nan fuskarsa jina-jina duk ta kumbura amma sai tsiwa yake yi bai fasa ba. Shi kuma ƙaton nan sai hararata yake yi yana cewa, “wai kai taya ni dukansa kake yi ko kuwa hana ni kake yi?” Na yi farat na ce duka biyun.” Na ce, “yanzu kai da girmanka, yaushe za ka ɓatawa kanka lokaci wajen dukan wannan dan tamilon?”

Ya ce, “ba ka san shegen yaron nan ba ne.” Nan ya soma bani labarinsa. Sai na fahimci ashe wannan ƙaton ɗan sanda ne mai mukamin Sajen, ya yi laifi aka sakaya shi. An ce ba zai fita ba sai yayi kwana bakwai. Shi kuma yaron, sata ya yi. Kuma a waje sun san juna suna takun saƙa. Haduwarsu a ciki ta sa yake masa gorin shi ma ga shi nan an kawo shi inda yake kai mutane. Tun da suka fara fadan babu wanda ya ce musu kanzil a tsararrun nan sai ni daga zuwa na. Sai dai lokaci zuwa lokaci ‘yan sanda na lekowa su yi musu tsawa.

Yana ba ni labarin abin da ya haɗa su ina goyon bayansa. Hira ta yi nisa tsakaninmu, sai aka manta da dukan yaro muka shiga hirar duniya. Ya riƙa gaya min irin manyan iyayen gidansa. Ni kuma ina ce masa na sansu. Wasu na san su, wasu kuma ban san su ba.

Zamana a cikin gadirum din bai wuce awa daya da mintuna ba, na sa aka sayo mana abinci da biskit da ruwa muka ci muka sha. Sanan na tilastawa yaron nan ya ba wa sajan hakuri.
Lokacin da zan fita, tsararrun nan suna mini godiya, sai yaron ya ce, “oga Allah ya sa gobe ka dawo.” Na juyo da sauri na ce masa, “bakinka ya sari danyen kashi.”

Wannan ne karon farkon shiga ta gadirum a tsawon rayuwata.
~~~~~~~

Previous Post

Humility and Gentility: My Encounter with Dr. Bukar Usman

Next Post

Yau Aka Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Al’ummar Jihar Katsina

Related Posts

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido
Adabi

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

June 8, 2026
ALHAMDU LILLAH
Adabi

ALHAMDU LILLAH

May 15, 2026
Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
Adabi

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Next Post
Yau Aka Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Al’ummar Jihar Katsina

Yau Aka Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Al'ummar Jihar Katsina

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

BUWDA is the Pride of Bura People, Humanity in General – Dr. Bukar Usman

BUWDA is the Pride of Bura People, Humanity in General – Dr. Bukar Usman

April 14, 2025
MUHAMMADU (SAW)

MUHAMMADU (SAW)

October 3, 2025
Jaafar Jaafar Da ‘Yan Siyasar Kano: Ashe Wanzami Ba Ya Son Jarfa?

Jaafar Jaafar Da ‘Yan Siyasar Kano: Ashe Wanzami Ba Ya Son Jarfa?

September 15, 2025
Za Mu Inganta Rayuwa Da Ayyukan ‘Yan Jarida – Minista Idris

Nijeriya Ta Ba Amurka Tabbacin Ci Gaba Da Riƙo Da ‘Yancin ‘Yan Jarida

November 27, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Inna Lillahi… We Lost Gen. Rabe
  • FIFA World Cup 2026: Yau Akwai Gumurzu Tsakanin Brazil Da Morocco
  • Yau Za A Fafata Tsakanin Canada Da Bosnia-Herzegovina

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Inna Lillahi… We Lost Gen. Rabe

Inna Lillahi… We Lost Gen. Rabe

June 13, 2026
FIFA World Cup 2026: Yau Akwai Gumurzu Tsakanin Brazil Da Morocco

FIFA World Cup 2026: Yau Akwai Gumurzu Tsakanin Brazil Da Morocco

June 13, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.