• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Wednesday, July 1, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Ɗan Majalisa Aminu Acid

Abduljalal Ɗayyabu by Abduljalal Ɗayyabu
October 1, 2023
in Gizago
0
Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Ɗan Majalisa Aminu Acid

Aminu Ibrahim Sa'id (Acid)

28
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Ɗan Majalisa Aminu Acid

~~~~~~~
Daga Abduljalal Ɗayyabu
~~~~~~~

Related posts

Tattaunawar Ɗan Jarida Da Bazawara ‘Yar Tuwo-Tuwo

Tattaunawar Ɗan Jarida Da Bazawara ‘Yar Tuwo-Tuwo

June 23, 2026
Ilimin Zamani: Babban Ƙalubale Ga Al’ummar Musulmin Arewa

Ilimin Zamani: Babban Ƙalubale Ga Al’ummar Musulmin Arewa

June 22, 2026

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki, mai kowa, mai komai, wanda ya ƙagi shugabanci da kuma shugaba.

Wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa ce zuwa ga Ɗan Majalasar Dokoki ta Jihar Katsina, mai wakiltar Ƙaramar Hukamar Malumfashi, Aminu Ibrahim Sa’id Acid.

Al’ummar Mazaɓar Na’alma suna ƙara tunatar da kai alƙawuran da ka ɗaukar masu a lokacin yaƙin neman zaɓenka na farko da na biyu. Musamman hanyar da ta tashi daga Babban Duhu da ke cikin Mazaɓar Dayi zuwa Karo, Garangozai, Gidan Mai Jumina da ke Mazaɓar Na’alma, har zuwa Ɗandashire da ke Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara.

Al’ummar wannan karkara suna cikin mawuyacin hali, musamman wajen kai mutane asibiti a lokacin damina. Mutum yana ji yana gani naƙuda za ta kama matarsa, ko yaronsa bai lafiya, ko shi karan kansa, wannan mai naƙuda ko mara lafiya zai mutu amma a kasa kai shi asibiti saboda rashin hanya.

Abu na biyu da nake son sanar da kai shi ne, wannan yanki na manoma ne amma saboda sashin hanya, mutum yana ji yana gani dole ya ƙyale abin da ya noma ko wata dukiya tasa.

Idan har Allah Ya sa suka samu wannan hanya, to za su samu sauƙi sosai, nusamman wajen taƙaita salwantar rayukan mutane da dukiyoyinsu.

Na uku, wannan yanki na Mazaɓar Na’alma, yana ɗaya daga cikin yankunan da suka fi matsala ta fuskar tsaro da ake fama da ita a Ƙaramar Hukumar Malumfashi. Kullum jama’ar wannan mazaɓa suna barin garuruwansu ne sakamakon rashin zama lafiya a wannan yanki.

Idan har wannan hanya ta samu to za a samu sauƙi ƙwarai matuƙa wajen taimaka wa jama’an tsaro, domin su shigo wannan yanki, domin su kawo wa al’ummar wajen taimakon gaugawa.

Akwai jami’an tsaro sosai a wannan ƙaramar hukuma ta Malumfashi, domin kuwa akwai Area Commander na shiyya, akwai kuma barikin sojoji amma rashin hanya zuwa karkarar Wannan ce ya sanya ko da an kiraKaramar Hukamar waɗannan jami’an tsaron, ba su zuwa kawo tallafinsu ga wannan wajen. Suna duba cewa kafin ma su zo, ‘yan ta’addar sun wuce ko kuma saboda rashin sanin hanya ga jami’an tsaron.

Don haka al’ummar wannan yanki suke neman taimakon ujila daga Ɗan Majalasar wannan yankin asu ko kuma masu faɗa a ji n wannan yanki, da ma ‘yan soshiyalmidiya, domin isar da saƙo ga Gwamnatin Jihar Katsina dangane da wannan matsala ta hanya.

Al’ummar wannan yanki suna fatan Ɗan Majalasa Aminu Ibrahim Sa’id Acid da ya duba girman Allah, ya isar masu sa saƙonsu zuwa inda za a share masu kukansu.

Daga ƙarshe muna roƙon Allah Ya kawo zaman lafiya a wannan yanki da Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.

~~~~~~~
Saƙo daga Abduljalal Ɗayyabu, Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina.
~~~~~~~

Previous Post

DARASIN JUMU’A DAGA SHEIKH GAMAWA

Next Post

Related Posts

Tattaunawar Ɗan Jarida Da Bazawara ‘Yar Tuwo-Tuwo
Gizago

Tattaunawar Ɗan Jarida Da Bazawara ‘Yar Tuwo-Tuwo

June 23, 2026
Ilimin Zamani: Babban Ƙalubale Ga Al’ummar Musulmin Arewa
Gizago

Ilimin Zamani: Babban Ƙalubale Ga Al’ummar Musulmin Arewa

June 22, 2026
Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa
Gizago

Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya: Janar Buratai Ya Buƙaci A Ɗauki Matakan Gaugawa

June 16, 2026
Next Post

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

A Harkar Rubutu: Na Fi Fuskantar Matsala Daga Mata – Uwa Idris

A Harkar Rubutu: Na Fi Fuskantar Matsala Daga Mata – Uwa Idris

July 4, 2023
MATSALAR TSARO: Sakkwatawa Mu Aje Siyasa Don Fuskantar Wannan Babbar Matsala

MATSALAR TSARO: Sakkwatawa Mu Aje Siyasa Don Fuskantar Wannan Babbar Matsala

October 4, 2023
Malam Haƙurau

Malam Haƙurau

July 8, 2023
DISCOS or Agents of Darkness?

DISCOS or Agents of Darkness?

April 25, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Lionel Messi: Tauraron Da Ya Sauya Tarihin Ƙwallon Ƙafa A Duniya
  • Lassa: A Different History
  • Asusun Tallafi na ACF Ya Tsara Sabuwar Hanyar Bunƙasa Ilimi da Ƙarfafa Al’ummar Arewa

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Lionel Messi: Tauraron Da Ya Sauya Tarihin Ƙwallon Ƙafa A Duniya

Lionel Messi: Tauraron Da Ya Sauya Tarihin Ƙwallon Ƙafa A Duniya

July 1, 2026
Lassa: A Different History

Lassa: A Different History

June 29, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.