AIKIN JIN ƘAI: Isma’eel Jauro Ya Shiga Kundin Tarihi Na Duniya
~~~~~~~
Ɗan Najeriya mai aikin jin ƙai da kare haƙƙin ɗan Adam, Malam Isma’eel S. Jauro, wanda aka sani da laƙanin “Activist” ya shiga Kundin Tarihi Na Duniya, saboda la’akari da ayyukansa na jin ƙai da tallafa wa raunana.

Binciken Taskar Gizago ya gano cewa wannan kambu da aka ba Jauro, babbar shaida ce da shahararriyar ƙungiyar adana muhimmanci bayanai ta “Notable Book of World Record” ke bai wa waɗanda suka yi fice ko suka kafa wani tarihi a duniya.
Da yake ƙara bayani game da dalilin ba shi wannan kambu, Isma’eel ya ce: “An ba ni wannan ne saboda ficen da na yi a duniya a kan aikin jin ƙai da kare haƙƙin ɗan Adam da kuma gudunmawar da nake bayarwa ga ilimi, muhalli da ci gaban al’umma.”
Da aka tambaye shi ko yaya ya ji kuma yaya ya ɗauki wannan karramawa da ya samu, sai ya bayyana cewa: “Eh, gaskiya na samu ƙwarin gwiwa sosai saboda wannan ya nuna cewa dukkanin abubuwan da nake yi, duniya tana biye da ni kuma tana kallon irin wannan sadaukarwa da muke. In sha Allahu za mu ci gaba da hidimta wa al’umma.”
Wane ne Isma’el S. Jauro? An haife shi ne a garin Babaldu, na Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu, Jihar Jigawa, shekaru 33 da suka gabata. Ya yi makarantar allo (almajiranci) a garin Giyaɗe na Jihar Bauchi. Ya yi karatun firamare da sakandare a Jihar Jigawa da kuma gaba da sakandare a Abubakar Tatari Ali Polytechnic Bauchi, inda ya karanta darasin Aikin Jarida wato Mass Communication.
“Na samu halartar kwasa-kwasai da dama kan abin da ya shafi Bincike ta Fuskar Aikin Jarida a Jami’o’i irin su Atlantic International University USA da European Research Institute Vietnam da kuma kwasa-kwasai kan kare haƙƙin ɗan Adam daga Amnesty International da United Nation for Human Rights.
~~~~~~~













Alhamdulillah ya can-canci hakan dama
Ma sha Allah. Muna godiya da bibiyar mujallar Taskar Gizago.