GURƁATACCEN HATSI: An Ja Hankalin Hukumomin Jihar Katsina
Hankalin al’umma a Jihar Katsina ya tashi, yadda aka samu bayyanar wani gurbataccen hatsi, musamman masara da shinkafa a hannun mutane.
An yi zargin cewa, hatsin na daga cikin

wanda Gwamnatin Jihar Katsina ke rabawa ne ga mabuƙata a matsayin tallafin rage raɗaɗin matsin rayuwa da ake ciki. Da yake tsokaci game da al’amarin, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum kuma mai tallafa wa marasa galihu a Jihar Katsina, Malam Muhammad Aminu Kabir ya zargi wasu daga cikin ‘yan kwangilar da gwamnati ta ba aikin samar da hatsin, inda ya roƙe su da su ji tsoron Allah, su gyara lamarinsu.
“Don Allah ‘yan Kasuwa ko ‘yan kwangilar da aka ba damar kawo wa al’ummar Jihar Katsina tallafin masara, ku ji tsoron Allah…” in ji Muhammad.
Ya ci gaba da cewa, “bayanai daga mabambantan wurare na nuni da cewa masarar da ake rabawa, an yi amaja a cikin ta. Ma’ana, an gauraya sabuwa da tsohuwa a wuri guda, sannan wata ma ta fara lalacewa.”
Ya ce akwai buƙatar waɗanda aka ɗora wa wannan alhakin, su kula da duk wanda suka bai wa damar kawo masarar nan. “Idan ya kawo marar kyau, ya ƙwashe abinsa, kar su yadda a ba da abin da zai iya cutar da al’umma,” kamar yadda Muhammad Aminu ya bayyana.
A Malumfashi Jihar Katsina kuwa, wasu mutane sun koka ne game da gurɓatattar shinkafar da ake rabawa, a matsayin tallafin rage matsin rayuwar da ake ciki. Kamar yadda wani mazaunin garin, Malam Aliyu Umar S/Gini ya koka game da gurɓatattar shinkafar, ya ce: “Yanzu wani ya zo shagona, ya gaya mani cewa shinkafar da Gwamna Dikko Raɗɗa ya raba, wari take, sai ƙudaje ke bin ta.”
Wakilinmu ya tuntuɓi Babban Mataimaki Ga Gwamnan Jihar Katsina Kan Al’amuran Watsa Labarai, Malam Maiwada Ɗammallam, ta wayar tarho, domin jin bahasin gwamnati kan lamarin. Ya bayyana cewa babu shakka ya samu rahoton da wasu kafafen watsa labarai suka wallafa kan lamarin. Sai dai ya ce ba su bayyana hakikanin wuraren da aka samu gurɓataccen hatsin ba.
“Tabbas akwai tallafin hatsi kala biyu da gwamnati za ta raba, ɗaya daga Gwamnatin Tarayya, ɗaya kuma daga Gwamnatin Jiha. Ya zuwa yanzu hatsin tallafi daga Gwamnatin Tarayya bai zo ba, balle a fara rabawa. Shi kuma na Jihar Katsina, an ɗora aikin sanarwar da rabawa ga dukkan ƙananan hukumomin jihar, su za su sayi hatsin kuma su raba shi, ” in ji Malam Maiwada.
Ya ƙara da cewa, kasancewar kowace ƙaramar hukuma ce ke da alhakin raba hatsin, akwai yiwuwar a samu wani ɓangare da matsala, kasancewar ‘yan kwangila ne da yawa kuma daban-daban.
“Ya zuwa yanzu dai, a hukumance, har yanzu ba mu samu sahihin ƙorafi kan haka ba. Yana da kyau kafafen watsa labarai su zurfafa bincike, domin tabbatar da hakikanin wuraren da aka samu irin wannan matsalar, domin a gyara.” A cewar Malam Maiwada Ɗammallam.

Ya zuwa yanzu dai, al’umma na kokawa kan lamarin, inda suka nemi Gwamnatin Jihar Katsina ta binciki al’amarin kuma ta magance matsalar, domin gudun kada hatsin ya haddasa cuta ga al’umma.













