NASIHARMU TA YAU 51
Mu Guji Hassada (6)
__________
Allah ya yi mana gargaɗi, mu guji nuna ƙyashi ga abin da ya ba wasu bayinsa na arziƙi.
A Alkur’aninsa mai girma, Suratun Nisa’i, aya ta 32, Allah yana cewa: “Kuma kada ku yi burin abin da Allah ya fifita sashenku da shi a kan sashe. Maza suna da rabo daga abin da suka tsirfanta, kuma mata suna da rabo daga abin da suka tsirfanta. Kuma ku roƙi Allah daga falalarsa. Lalle ne Allah ya kasance masani ga kowane abu.”
Wannan shi ke nuna mana cewa Allah ya riga ya raba wa kowa arzikinsa daidai yadda ya dace. Babu wani da zai mallaki abin da Allah bai ƙadarta masa ba. Don haka babu buƙatar hassada ko ganin ƙyashin abin da Allah ya ba wani bawansa.
(Za mu ci gaba)
___________













