• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, September 10, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 13, 2026
in Labarai
0
Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

Gwamna Malam Dikko, tare da 'yan Kwamitin Inganta Makarantun Alkur'ani

13
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026

__________

Nan ba da jimawa ba Gwamnatin Jihar Katsina za ta samar da ingantaccen tsarin gudanar da makarantun Alkur’ani, bayan da Gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Radda, ya karɓi rahoton kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin duba yadda makarantun Tahfiz ke gudanar da ayyukansu tare da samar da cikakken tsarin daidaita da kuma tsara yadda za a tafiyar da su a faɗin jihar.

Rahoton, wanda aka miƙa wa Gwamnan a hukumance yayin taron Majalisar Zartarwar Jihar, ya ƙunshi shawarwari da suka shafi gyaran dokoki da manufofi, ba da takardun shaidar kammala karatu, daidaita manhajar karatu, horas da malamai, inganta jin daɗin malamai da ɗalibai, tattara bayanai da kuma inganta tsarin sa ido kan makarantun koyar da Alƙur’ani.

Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Katsina, Dr. Ahmad Musa Abdullahi Filin Samji ne ya jagoranci mambobin kwamitin wajen gabatar da rahoton, yayin da ɗaya daga cikin mambobin kwamitin, Dr. Bashir Ruwan Godiya ya bayyana muhimman abubuwan da rahoton ya ƙunsa da kuma shawarwarin da aka bayar.

A yayin gabatar da rahoton, Dr. Ruwan Godiya ya ce kwamitin ya gano wasu ƙalubale da ke addabar makarantun Ƙur’ani, waɗanda suka haɗa da rashin cikakken tsari na gudanar da su, bambance-bambancen manhajar karatu, raunin tsarin sa ido, rashin isasshen tsarin bayar da takardun shaida da kuma matsalolin jin daɗin malamai da ɗalibai.

Ya bayyana cewa kwamitin ya gudanar da ziyarar bincike zuwa jihohin Kaduna, Kano, Yobe da Zamfara, tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a faɗin Jihar Katsina da kuma nazarin manufofi da hanyoyin gudanar da makarantun da ake amfani da su a yanzu, domin gano waɗanda suka dace a yi amfani da su bisa yanayin Jihar Katsina.

A cewarsa, kwamitin ya amince da muhimmiyar rawar da makarantun Ƙur’ani suke takawa wajen kare al’adun Musulunci, ilimin Alƙur’ani da kuma ɗabi’un kirki amma ya jaddada buƙatar ƙarfafa tsarin gudanarwa, sa ido da kuma tsarin ilimi na makarantun, me domin su dace da buƙatun zamani.

“Mun duba batun tsari, kuɗaɗen gudanarwa, tsarin makarantu da kuma yadda ya kamata a tafiyar da tsarin. Duk waɗannan an tanade su ne domin tabbatar da cewa makarantun suna aiki yadda ya kamata, suna da tsari mai kyau kuma suna tafiya daidai da buƙatun zamani da sauye-sauyen duniya,” in ji shi.

Dr. Ruwan Godiya ya ce ɗaya daga cikin manyan manufofin gyaran tsarin shi ne samar da damar da masu haddar Alƙur’ani za su samu takardar shaidar karatun da aka amince da ita, tare da samun damar ci gaba da karatu a manyan makarantu da kuma koyon ƙwarewar da za ta inganta damar samun aikin yi a hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Ya bayyana cewa wasu jihohi sun riga sun samar da alaƙa tsakanin haddar Alƙur’ani, ilimin zamani da kuma tsarin bayar da takardun shaidar karatu, inda wasu masu haddar Alƙur’ani suka samu damar shiga jami’o’i har ma da ci gaba zuwa matakin karatun digiri na biyu da na gaba.

“Kasancewar yaro ya haddace Alƙur’ani bai kamata ya zama abin da zai taƙaita masa damar samun ilimi ba. Idan aka ba su tallafi, takardar shaida da ƙwarewar da ta dace, waɗannan ɗalibai za su iya ci gaba da karatu kuma su ba da gagarumar gudummawa ga al’umma,” in ji shi.

Daga cikin manyan shawarwarin da kwamitin ya gabatar akwai sauya tsarin Hukumar Ilimin Musulunci ta Jihar zuwa Hukumar Ilimin Alƙur’ani, Larabci da Addinin Musulunci ta Jihar Katsina (QAIEB).

A ƙarƙashin sabon tsarin da aka gabatar, hukumar za ta kasance da sassa na musamman da za su kula da ilimin Alƙur’ani, Larabci da Nazarin Addinin Musulunci, da kuma ayyukan makarantu, domin samar da ingantaccen tsarin haɗa kai wajen sa ido da bunƙasa ilimin Musulunci a jihar.

Kwamitin ya kuma ba da shawarar samar da cikakken kundin bayanai da zai ƙunshi dukkan makarantun Almajirai, Islamiyya da Tahfiz da ke faɗin jihar.

Kwamitin ya kuma ba da shawarar kafa makarantun Tahfiz na gwaji a shiyyoyin Sanatoci uku. A ƙarƙashin wannan shawara, za a ƙarfafa tsarin da ake da shi a Katsina, yayin da za a kafa ƙarin cibiyoyi a shiyyar Daura da shiyyar Funtua.

Gwamna Malam Dikko, tare da ‘yan Kwamitin Inganta Makarantun Alkur’ani

Domin inganta lwmarin da kuma samar da hanyar bunƙasa ilimin Alƙur’ani, kwamitin ya buƙaci haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da hukumomin da suka dace, ciki har da Hukumar Kula Da Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Ƙasa  (NBAIS), Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua da hukumomin da ke da alhakin kula da ilimin Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta.

A cewar kwamitin, irin wannan haɗin gwiwa zai ƙarfafa tsarin bayar da takardun shaida, bincike, adana bayanai da kuma samar da hanyoyin da ɗaliban makarantun Alƙur’ani za su bi domin ci gaba zuwa manyan makarantu da tsarin ilimin zamani.

Dangane da aiwatar da shawarwarin, Dr. Ruwan Godiya ya ce kwamitin ya gabatar da tsarin aiwatarwa a matakai daban-daban. Matakin farko, wanda zai ɗauki watanni 12, zai mayar da hankali kan gyaran dokoki da manufofi, tattara bayanai da rajistar makarantun da abin ya shafa.

Mataki na gaba zai ƙunshi samar da manhajar karatu, cikakken rajistar makarantu da horar da malamai, kafin a shiga matakin tilasta bin ƙa’idoji, bayar da takardun shaidar kammala karatu ga ɗimbin ɗalibai da kuma haɗa ilimin Tahfiz da sauran shirye-shiryen ilimi.

Kwamitin ya kuma jaddada muhimmancin wayar da kan masu ruwa da tsaki kafin da kuma yayin aiwatar da shirin, tare da tabbatar da cewa gyare-gyaren da aka gabatar ba za su ci karo da ƙa’idojin Musulunci ba.

“Ba muna ƙoƙarin yin wani abu da ya saɓa wa Shari’a ba ne. Abin da muke ƙoƙarin yi shi ne ƙarfafa tsarin, mu sanya shi ya dace da buƙatun yau, tare da samar da ingantattun damarmaki ga ɗalibai domin gaba,” in ji Dr. Ruwan Godiya.

Da yake mayar da martani bayan gabatar da rahoton, Gwamna Radda ya yaba wa kwamitin bisa abin da ya bayyana a matsayin cikakken aiki mai muhimmanci wajen ƙarfafa ilimin Alƙur’ani a Jihar Katsina.

Gwamnan ya ce shawarwarin da rahoton ya ƙunsa za su taimaka wajen inganta tsari, gudanarwa da kuma tasirin ilimin Alƙur’ani, tare da tabbatar wa kwamitin cewa gwamnati za ta nazarci rahoton dalla-dalla kafin ɗaukar matakan da suka dace.

“Da gaske muna godiya ga Shugaban kwamitin da sauran mambobinsa bisa kyakkyawan aikin da suka gudanar. Za mu duba rahoton sosai kuma mu yi adalci ga shawarwarin da aka gabatar, in sha Allah,” in ji Gwamna Raɗɗa.

Sai dai Gwamnan ya buƙaci a sake nazarin wa’adin lokacin da aka tsara domin aiwatar da shawarwarin, yana mai cewa akwai wasu daga cikinsu da za a iya aiwatar da su tun kafin lokacin da kwamitin ya tsara.

“Ya kamata a sake duba jadawalin lokacin da aka tsara sosai, domin akwai yiwuwar mu aiwatar da wasu daga cikin waɗannan abubuwa kafin lokacin da aka tsara. Abu ne mai yiwuwa,” in ji shi.

Gwamna Radda ya ƙara da cewa gwamnati za ta tantance shawarwarin da za a iya fara aiwatarwa nan take, tare da samar da tsare-tsaren da suka dace ga waɗanda ke buƙatar dogon lokaci wajen shiryawa da aiwatarwa.

Gwamnan ya kuma yaba wa mambobin kwamitin bisa jajircewarsu da gudummawar da suka bayar wajen ƙarfafa ilimin Alƙur’ani, tare da tabbatar da cewa rahoton zai samu kulawar da ta dace a wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin jihar na ingantawa, samar da tsari da kuma dacewar ilimin Alƙur’ani da buƙatun zamani.

Manyan jami’an gwamnatin jihar da mambobin kwamitin ne suka halarci taron da aka gabatar da rahoton a hukumance.

__________

Previous Post

Tsakanin Maza Da Mata Wa Ya Fi Yawa A Duniya?

Next Post

Regulation, Standardisation of Qur’anic Schools Under Way in Katsina

Related Posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin
Labarai

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda
Labarai

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026
Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)
Labarai

Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)

August 31, 2026
Next Post
Regulation, Standardisation of Qur’anic Schools Under Way in Katsina

Regulation, Standardisation of Qur'anic Schools Under Way in Katsina

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Shekara 30 A Inuwar Aure: Fatan Alheri Ga Editan Rfi Hausa

Shekara 30 A Inuwar Aure: Fatan Alheri Ga Editan Rfi Hausa

July 17, 2023
AIKIN JIN ƘAI: Isma’eel Jauro Ya Shiga Kundin Tarihi Na Duniya

AIKIN JIN ƘAI: Isma’eel Jauro Ya Shiga Kundin Tarihi Na Duniya

September 26, 2023
Sokoto State: ASATTAHIR Foundation Supports 1000 IDPs, Vulnerables  By Ibrahim Danfulani

Sokoto State: ASATTAHIR Foundation Supports 1000 IDPs, Vulnerables By Ibrahim Danfulani

December 26, 2023
Za Mu Zamanantar Da Ayyukan Hukumar Ruwa – Injiniya Tukur

Za Mu Zamanantar Da Ayyukan Hukumar Ruwa – Injiniya Tukur

June 27, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai
  • Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
  • SANATA BELLO MANDIYA: Mun Yi Babban Rashi – Gwamnan Katsina

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026
Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.