Gwamna Dikko Ya Ƙaddamar da Aikin Faɗaɗa Titin Cikin Garin Mashi Mai Tsawon Kilomita Uku
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON ya ƙaddamar da aikin ginawa da faɗaɗa titin cikin garin Mashi mai tsawon kilomita uku, a wani mataki na ƙara inganta ababen more rayuwa da bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Aikin, wanda zai gudana a kan babbar hanyar Katsina zuwa Daura, na daga cikin Shirin Sabunta Birane na gwamnatin jihar da ake aiwatarwa ƙarƙashin manufar “Building Your Future,” yayin da Kamfanin Mothercat Nigeria Limited zai gudanar da shi ƙarƙashin kulawar Ma’aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri ta Jihar Katsina.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da aikin, Gwamna Radda ya bayyana cewa titin zai taimaka wajen inganta zirga-zirga, ƙara tsaron masu amfani da hanya, sauƙaƙa jigilar amfanin gona da sauran kayayyaki zuwa kasuwanni, rage kuɗaɗen sufuri, tare da ƙarfafa harkokin kasuwanci da tattalin arziki a Mashi da ma yankunan da ke kewaye da ita.
Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan da za su inganta rayuwar al’umma da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a sassa daban-daban na jihar.
Tun da farko, Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri na Jihar Katsina, Engr. Dr. Sani Magaji Ingawa, ya bayyana cewa aikin wani ɓangare ne na ƙudirin gwamnatin jihar na samar da ingantattun hanyoyi da suka dace da ƙa’idojin aikin zamani.
A cewarsa, aikin zai haɗa da gina magudanan ruwa na zamani, hanyoyin masu tafiya a ƙasa da kuma sanya fitilun kan titi masu amfani da hasken rana. Ya kuma tabbatar da cewa ma’aikatar za ta sanya ido sosai domin tabbatar da cewa an gudanar da aikin cikin inganci da bin ƙa’idojin da aka shimfiɗa.
Shi ma wakilin Kamfanin Mothercat Nigeria Limited ya gode wa Gwamnatin Jihar Katsina bisa amincewar da ta ba kamfanin, yana mai tabbatar da cewa za su gudanar da aikin bisa ƙa’idojin ƙwararru tare da kammala shi cikin wa’adin da aka tsara.
A madadin Mai Martaba Sarkin Katsina, Durɓin Katsina kuma Hakimin Mani, ya yaba wa Gwamna Raɗɗa bisa ci gaba da zuba jari a fannin ababen more rayuwa. Ya kuma isar da godiya da fatan alheri daga Mai Martaba Sarkin Katsina, tare da yin kira ga al’ummar yankin da su ba da cikakken haɗin kai domin tabbatar da nasarar aikin.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Mashi ya bayyana cewa aikin zai taka muhimmiyar rawa wajen sauƙaƙa zirga-zirga da bunƙasa tattalin arzikin yankin.
Haka kuma, Shugaban Masu Ruwa da Tsaki na ƙaramar hukumar, Hon. Salisu Yusuf Majigiri, ya yaba wa Gwamna Raɗɗa bisa abin da ya bayyana a matsayin adalci da daidaito wajen rabon ayyukan ci gaba a faɗin jihar, tare da tabbatar masa da cikakken goyon bayan al’ummar Mashi.
A ƙarshen jawabinsa, Gwamna Radda ya umarci kamfanin da ke aiwatar da aikin da ya tabbatar da mafi girman inganci tare da kammala aikin cikin lokacin da aka tsara, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko ga ayyukan raya ƙasa da inganta jin daɗin al’ummar Jihar Katsina.
Bikin ƙaddamar da aikin ya samu halartar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahya Daura, mambobin Majalisar Zartarwa ta Jiha, ‘yan majalisa, sarakunan gargajiya, shugabannin ƙananan hukumomi, shugabannin siyasa da sauran al’umma.
__________













