• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Taron COP28: Shugaba Tinubu Da Ayarinsa Ba Sharholiya Ta Kai Su Dubai Ba – Minista Idris

* Minista ya yi bayani kan masu cewa Ayarin Nijeriya a taron sauyin yanayi ta yi yawa

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
December 6, 2023
in Labarai
0
Taron COP28: Shugaba Tinubu Da Ayarinsa Ba Sharholiya Ta Kai Su Dubai Ba – Minista Idris

Shugaba Tinubu tare da wasu shugabannin ƙasashen duniya, a yayin taron COP28 a Dubai

10
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Taron COP28: Shugaba Tinubu Da Ayarinsa Ba Sharholiya Ta Kai Su Dubai Ba – Minista Idris

* Minista ya yi bayani kan masu cewa Ayarin Nijeriya a taron sauyin yanayi ta yi yawa

Related posts

Bura women Celebrate Bukar Usman at 83

Ƙungiyar Matan Al’ummar Bura Sun Karrama Dr. Bukar Usman Bisa Cika Shekaru 83

January 9, 2026
Sojoji Sun Ƙwato Muggan Makamai A Jihar Taraba

Sojoji Sun Ƙwato Muggan Makamai A Jihar Taraba

January 5, 2026

 

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba yawon sharholiya ne ya kai Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ‘yan tawagar Nijeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi da ake yi a Dubai ba, a’a, aiki wurjanjan ne ya kai su.

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya faɗi haka a cikin takardar sanarwa ga manema labarai da ya rattaba wa hannu inda ya yi tsokaci kan masu zargin cewa wai gwamnati ta kwashi mutane fiye da kima zuwa taron, wanda ake yi wa laƙabi da COP28.

Idris ya ce gwamnatin ta lura da maganganun da ake yi kan yawan ‘yan tawagar da su ka je Dubai domin halartar taron, kuma ta ga “akwai buƙatar ta samar da ƙarin haske kamar yadda ta yi alƙawarin za ta riƙa gudanar da al’amuran ta a bayyane tare da kasancewa mai fayyace komai ga jama’a dangane da abin da ya shafi bayani.”

A cewar sa, “Taron Masu Ruwa da Tsaki (Convention of Parties, COP) na Tsarin Shirye-shiryen Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sauyin Yanayi, wato ‘United Nations Framework Convention on Climate Change (UNFCCC)’ shi ne mashahurin Taron Duniya kan Sauyin Yanayi wanda a bana ya samu halartar sama da mahalarta 70,000 da tawagogi daga sama da ƙasashe 100. Wakilcin da Nijeriya ta samu ya yi daidai da matsayin mu na jagora mai faɗa a ji a Afrika kuma babbar mai taka rawa kan al’amarin sauyin yanayi, wato ‘climate action’.”

Ya ce waɗanda su ka halarta daga Nijeriya sun haɗa da jami’an gwamnati, wakilan ‘yan kasuwa da na ƙungiyoyi masu zaman kan su, da ‘yan sa kai, gwamnatocin jihohi, ‘yan jarida, hukumomin ƙasa da ƙasa, wakilan al’ummomin da ba a yi da su, da sauran su da dama.

“Ya na da muhimmanci a fahimci cewa gaba ɗaya tawagar Nijeriya a taron na COP28 ta ƙunshi mutanen da gwamnati ta ɗauki nauyin su (wato gwamnatocin tarayya da jihohi) da mahalartan da ba gwamnati ce ta ɗau nauyin su ba (wato daga kamfanoni masu zaman kan su da ƙungiyoyi da ‘yan jarida da malaman jami’a, da sauran su).

Idris ya bada lissafin ‘yan tawagar da su ka je a aljihun gwamnati su mutum 422, kamar haka:

1. Hukumar Sauyin Yanayi ta Ƙasa = mutum 32
2. Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya = 34
3. Dukkan Ma’aikatu = 167
4. Fadar Shugaban Ƙasa = 67
5. Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa = 9
6. Majalisar Tarayya = 40
7. Hukumomin gwamnati da cibiyoyi = 73

Ya bada tabbacin cewa a matsayin Nijeriya na wadda ta ke da ƙarfin tattalin arziki fiye da sauran ƙasashen Afrika kuma mafi yawan jama’a a nahiyar, kuma ta na da tattalin arziki da ake samu daga ma’adinai, wadda ke fuskantar barazanar sauyawar yanayi, ta na da muhimmin matsayi a batun sauyin yanayi, “don haka rawar da za mu taka a taron COP ba kaɗan ba ce.”

Ministan ya ƙara da cewa: “Taron COP28 ya bada damarmaki na zuba jari da ƙulla yarjejeniyoyin haɗin gwiwa a sassa daban-daban da sauyin yanayi ya shafe su, kuma yanzu har ma Nijeriya ta fara cin moriyar shiga taron da ta ke yi, kamar yadda waɗannan al’amurran su ka shaidar:

“1. Nijeriya da Jamus sun rattaba hannu kan gaggauta aiwatar da Shirin Shugaban Ƙasa kan Wutar Lantarki (PPI) domin inganta samar da lantarki a Nijeriya. Waɗanda su ka rattaba hannun su ne Mista Kenny Anuwe, wato Manajan Darakta kuma Shugaban Kamfanin Wutar Lantarki na Gwamnatin Tarayya, da Miss Nadja Haakansson, Babbar Mataimakiyar Shugaban Kamfanin Wutar Lantarki na Siemens Energy wadda kuma ita ce Manajar-Darakta ta shiyyar Afrika ta kamfanin, a wani biki da aka yi a gaban Shugaba Tinubu da Shugaban Jamus, wato Chancellor Scholz.

“2. Shugaba Tinubu ya jagoranci wani babban taro wanda masu ruwa da tsaki da masu zuba jari su ka yi ma kan Kasuwar Man Fetur ta Nijeriya da Shirin Kawo Motocin Safa Masu Aiki da Hasken Rana a lokacin da ake taron ƙoli na COP28 kan sauyin yanayi.

“a. Shugaban Ƙasa ya ƙaddamar da Tsarin Kasuwar Man Fetur ta Nijeriya, inda mataimakin shugaban taron shi ne Babban Ciyaman na Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Tarayya (FIRS), Mista Zacch Adedeji, da Darakta-Janar na Hukumar Sauyin Yanayi ta Ƙasa (NCCC), Dakta Ɗahiru Salisu.

“b. Shirin Motocin Safa Masu Aiki da Hasken Rana matakin farko kaɗai ne na shirye-shirye da tsare-tsare na zamani wajen rage dogaro da man fetur a sassa daban-daban, waɗanda dukkan su manufar su ita ce a magance matsalolin da su ka jiɓinci sauyin yanayi, da rage amfani da fetur, da zamanantar da wuraren aiki, tare kuma da ɗora Nijeriya kan turbar da za ta zama abar zaɓi ga masu zuba jari na duniya.

“3. Akwai alamun Nijeriya za ta ci moriyar Asusun Asara Da Ɓarna (Loss and Damage Fund) wanda aka kafa a lokacin taron COP27 da aka yi a Masar kuma aka ƙaddamar da shi a wajen buɗe wannan taron na COP28 a Dubai. Asusun zai samar da kuɗaɗen da ba bashi ba ne waɗanda za a kashe don tallafa wa ƙasashen da tasirin sauyin yanayi ya fi shafar su. Har an yi alƙawarin bada gudunmawar ɗaruruwan miliyoyin daloli a matsayin gudunmawa ga Asusun.

“4. Haka kuma Shugaban Ƙasa ya yi taro da Shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) don tabbatar da yarjejeniyoyin da ke akwai a tsakanin ƙasashen biyu. Duk wannan ban da fa tattaunawar diflomasiyya da aka yi da ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa daban-daban.

“Ya kamata a sani cewa, a tsawon shekaru, Nijeriya ta tabbatar da matsayin ta kan batun sauyin yanayi ta hanyar zama ƙasar Afrika ta farko da ta ƙaddamar da Tsarin Tafiyar da Makamashi (Energy Transition Plan), kuma ƙasar Afrika ta farko da ta fitar da Dukiyar Ƙasa Kan Daina Amfani da Makamashin Mai (Sovereign Green Bond), sannan ta na cikin ƙasashe na farko da su ka kafa dokar sauyin yanayi ta ƙasa.

“Shugaba Tinubu ya sha fitar da matsayin sa kan cewa Afrika, wadda ke fama da matsalolin fatara da rashin tsaro kuma ta na fafutikar samar da ilimi da kiwon lafiya ga jama’ar ta, babu wanda zai ce mata ta watsar da hanyar farko da ta ke samun kuɗin shiga, wanda yawanci daga masana’antun man fetur ne, ba tare da ƙasashen Yammaci sun samar da kuɗin da za a kashe wajen zuba jari a hanyoyin samar da makamashin da ba fetur ɗin ba.

“Tun daga lokacin da ya shiga aiki, Shugaba Tinubu ya zama gwarzon yekuwar matsayin Afrika a dandalin duniya, ya yi magana a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA), da taron G20, da wannan taron da ake yi na COP28. Shugaban Ƙasa ya samu goyon bayan zaƙaƙuran tawagar ‘yan Nijeriya su ma a waɗannan tarurrukan daban-daban.

“Saboda haka dai, ya na da muhimmanci a riƙa faɗin gaskiya a yayin da ake tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa Shugaba Tinubu da sauran jami’an Gwamnatin Tarayya sun je Dubai ne domin gudanar da aiki wurjanjan, ba wai sharholiya ce ta kai su ba.”

Previous Post

IGABI AIR STRIKE: A Call for Justice

Next Post

BIU: A Visit to a City on a Plateau (1)

Related Posts

Bura women Celebrate Bukar Usman at 83
Labarai

Ƙungiyar Matan Al’ummar Bura Sun Karrama Dr. Bukar Usman Bisa Cika Shekaru 83

January 9, 2026
Sojoji Sun Ƙwato Muggan Makamai A Jihar Taraba
Labarai

Sojoji Sun Ƙwato Muggan Makamai A Jihar Taraba

January 5, 2026
Hukuncin Nnamdi Kanu: Minista Bianca ta Nemi Igbo Su Guji Tada Fitina
Labarai

Hukuncin Nnamdi Kanu: Minista Bianca ta Nemi Igbo Su Guji Tada Fitina

November 22, 2025
Next Post
BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (1)

BIU: A Visit to a City on a Plateau (1)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Sojoji Sun Ƙwato Muggan Makamai A Jihar Taraba

Sojoji Sun Ƙwato Muggan Makamai A Jihar Taraba

January 5, 2026
Gen. Buratai Celebrates John Mahama’s Second Coming as Ghana’s President 

Gen. Buratai Celebrates John Mahama’s Second Coming as Ghana’s President 

December 10, 2024
KO ME YA SA MABIYA PETER OBI SUKA RIƘA MURNAR MUTUWAR HON. EKENE ABUBAKAR ADAMS?

KO ME YA SA MABIYA PETER OBI SUKA RIƘA MURNAR MUTUWAR HON. EKENE ABUBAKAR ADAMS?

July 17, 2024
Yau Maulidin Safinah Saleeth Adam

Yau Maulidin Safinah Saleeth Adam

July 7, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.