Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Malam Nasir El-rufa’i, mutumin da sunansa ya buga tambari a zukatan mutane a ƙasar nan. Rayuwarsa cike take da ƙalubale. Tun daga lokacin da sunansa ya bayyana a Gwamnatin Obasanjo a 2000 zuwa yau da muke ciki, 2026, bai taɓa ɓuya ba. A wannan nazari, za mu bibiyi irin waɗannan ƙalubale da ya fuskanta.
Malam Nasir, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna ne wanda ya shahara wajen aiwatar da manufofi masu tsauri da kuma sauye-sauye a harkokin gwamnati. An haife shi a 1960 kuma ya fara fitowa fili a siyasar ƙasar nan a farkon shekarun 2000. Rayuwarsa ta ƙunshi hawa da sauka da suka danganci muƙaman gwamnati zuwa lokutan ƙalubale da rikice-rikice da kuma nasara.
A zamanin mulkin Olusegun Obasanjo (1999–2007), El-Rufa’i ya fara aiki a matsayin Darakta Janar na Hukumar Kula Da Kadarorin Ƙasa (Bureau of Public Enterprises) daga 2003 zuwa 2007, inda ya jagoranci shirye-shiryen sayar da kamfanonin gwamnati. Daga bisani, ya zama Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) daga 2003 zuwa 2007. A wannan lokaci, ya gudanar da rusau da gyaran Abuja domin bin tsarin birnin, wanda ya jawo masa suka da ƙalubale daga jama’a da ‘yan siyasa daban-daban.
A wannan lokaci (2003–2007), ya fuskanci manyan matsaloli, ciki har da adawa daga masu ruwa da tsaki da kuma zarge-zargen rashin tausayi ga talakawa. Duk da haka, ya samu goyon baya daga Gwamnatin Obasanjo saboda jajircewarsa wajen aiwatar da manufofi ba tare da tsoro ba.
Bayan saukar Obasanjo daga mulki a 2007, a zamanin Umaru Musa Yar’Adua (2007–2010), rayuwar El-Rufai ta sauya. A daidai lokacin ya bar Najeriya, ya koma ƙasashen waje, musamman Amurka da wasu ƙasashe, sakamakon matsin lamba na siyasa da bincike da ake zargin ana yi masa. Wannan lokaci ya kasance kamar na gudun hijira a gare shi.
Daga 2010 zuwa 2014, bayan rasuwar Yar’adua da dawowar sauyin siyasa, El-Rufai ya fara dawowa Najeriya a hankali. A wannan lokaci, ya shiga harkokin siyasa a jam’iyyar CPC, sannan daga baya jam’iyyar ta shiga haɗaka, ta rikiɗe zuwa APC.
A shekarar 2015, El-Rufai ya zama Gwamnan Jihar Kaduna, inda ya yi mulki daga 2015 zuwa 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC. A wa’adinsa na farko (2015–2019), ya mayar da hankali kan gyaran ilimi, rage kashe kuɗin gwamnati da kuma sake fasalin ma’aikata. Amma ya fuskanci ƙalubale, musamman kamar rikicin Kudancin Kaduna, matsalar ‘yan Shi’a mabiya Sheikh Eizakzaky da matsalolin tsaro da sauransu.
A wa’adinsa na biyu (2019–2023), ya ci gaba da manufofinsa masu tsauri, ciki har da sallamar ma’aikata da sake tsarin makarantu. Kodayake ya samu wasu nasarori, musamman wajen samar da gine-gine amma ya fuskanci suka daga ƙungiyoyin ƙwadago da jama’a da kuma matsalolin tsaro da suka ci gaba da addabar al’ummar jihar.
Bayan kammala mulkinsa a 2023, ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda a farko aka bayyana shi a matsayin wanda za a naɗa Minista amma daga bisani Majalisar Dattawa ta hana tabbatar da naɗin nasa. Wannan ya zama babban ƙalubale a rayuwarsa ta siyasa, domin kuwa shi ne dalilin da ya sanya ya raba gari da Gwamnatin Tinubu. Daga bisani ma ya fita daga Jam’iyyar APC zuwa SDP, sannan kuma zuwa ADC.
Daga 2023 zuwa yanzu (2026), El-Rufai na fuskantar ƙalubalen da suka haɗa da na batutuwan shari’a tsakaninsa da Gwamnatin Tinubu da ta Uba Sani a Jihar Kaduna. A kan haka ake ta jerangiya da shi, daga Hukumomin ICPC da EFCC, inda yake tsare sama da wata ɗaya, kodayake a zaman shari’ar da aka yi a wannan makon, an amince da belinsa bisa tsausaran sharuɗɗan da idan ya cika su za a sake shi kuma a ci gaba da fafata shari’a.
Malam Nasiru ya zama gugar ƙarfe, sha kwaramniya. Ko yaya makomarsa za ta kasance a nan gaba? Ko akwai yiwuwar zai sake zama mai tasiri bayan kammala wannan shari’a, ko kuwa hasken siyasarsa zai dusashe? Shin ko zai iya dawowa da ƙarfi kamar yadda ya taɓa yi a baya? Allah ne kaɗai masani!
__________













