• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, April 6, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

TSOKACI

Mohammed Umar Midala by Mohammed Umar Midala
March 6, 2026
in Adabi
0
Let’s Speak Our Mother Tongue

Hagu-Dama: Mohammed Umar Midala, hoton gidan gargajiya da ake samu a garin Biu, Jihar Borno a shekarun baya, sai kuma Dr. Bukar Usman, OON

15
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

Daga Mohammed Umar Midala

Related posts

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)

March 1, 2026
Hagu-Dama: Mohammed Umar Midala, hoton gidan gargajiya da ake samu a garin Biu, Jihar Borno a shekarun baya, sai kuma Dokta Bukar Usman, OON

 

__________

Barka da Ranar Harshen Uwa.

Gudunmawar da Dokta Bukar Usman ya bayar ta zama ginshiƙi a fafutukar da Najeriya take yi wajen yaƙi da ɓacewar harsunan gida, inda ya jagoranci wani yunƙuri na ƙasa baki ɗaya wajen tattarawa da farfaɗo da al’adu da harsunan gida da suke fuskantar barazanar shuɗewa.

Tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015, ya jagoranci bincike na ƙasa baki ɗaya, inda ya tattara tatsuniyoyi da almara sama da 4,000 daga dukkan shiyyoyin Najeriya. Ya yi haka ne ta hanyar tattaunawa da dattawa, aka naɗi muryoyinsu da na’ura, inda suka bayyana tatsuniyoyin da ke akwai na asali a shiyyoyinsu.

Tarin littattafan da Dokta Bukar Usman ya wallafa, waɗanda suka taskance tatsuniyoyi da almarori a harsunan ƙabilun Najeriya.

Wannan aiki muhimmi ne, domin kuwa ya taskance al’adun gargajiya daban-daban na ƙabilun Najeriya cikin harsunansu na asali, kafin su ɓace.

Daga baya an fassara waɗannan tatsuniyoyi da almara da harsunan Hausa, Igbo, Yoruba da Turanci kuma aka wallafa su a manyan littattafai. Haka ke nuna cewa Dokta Usman  ya samar da babban rumbu na “Taskar Tatsuniyoyin Najeriya” wanda a yau yake zama ma’adanar ilimi mai gudana ga masana, makarantu da kafafen yaɗa labarai.

Wannan babban aiki da Dokta Usman ya samar, bai tsaya kan adana kalmomi kaɗai ba; ya ƙarfafa muhimmanci da bambancin al’adu ta hanyar nuna yadda harshe, tatsuniya da rayuwar yau da kullum suke haɗuwa wuri guda. A matsayinsa na shugaban Ƙungiyar Nazari da Bunkasa Al’adu ta Najeriya (Nigerian Folklore Society), ya mayar da waɗannan tarin littattafai, shirye-shiryen rediyo da kayan koyarwa a azuzuwa – yana bai wa matasan Najeriya damar samun tatsuniyoyi da almarorin da a da tsofaffi ke bayyana wa yara, a yayin hirar dare (cikin farin wata).

Wannan muhimmin aiki nasa, ya yi daidai da dabarun Hukumar Raya Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) na raya harsunan da suke fuskantar barazana. Aikin nasa, wanda ya haɗa da tattarawa, farfaɗowa da koyar da harshen uwa a makarantu; ya zama misali na ɗabbaƙa Shirin Raya Harsunan Gida na Asali na Majalisar Ɗinkin Duniya na Shekaru Goma (2022–2032).

Baya ga Najeriya, wallafe-wallafen Dokta Usman sun isa ƙasashen Afrika maƙwabta da al’ummomin da ke zaune ƙasashen duniya masu nisa. Lamarin da ya haifar da irin wannan ƙoƙari na tattarawa a yankunan Hausawa na Nijar da Chadi da sauransu. Masana daga ƙasar Sin, alal misali, sun yi ishara da aikinsa a matsayin abin koyi wajen kare gadon al’adun baƙar fata na Afirka a fagen ilimi na ƙasa da ƙasa.

Ta hanyar sarrafa tatsuniyoyi da almara daga waɗanda ake bayyanawa a zaman hira da dare, waɗanda ake ganin kamar sun ɓace, zuwa rubuce-rubuce a littattafai da intanet, Dokta Usman ya taimaka wajen ci gaba da bunƙasa tarin harsunan Najeriya, tare da gabatar da wata hanya mai sauƙin koyi ga sauran ƙasashen da ke fuskantar barazanar ɓacewar harsunansu na gida.

BARKA DA RANAR HARSHEN UWA

__________

Mohammed Umar Midala shi ne Mataimakin Sakataren Ilimi na Hukumar Ilimi ta Ƙaramar Hukumar Biu, Jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya.

Previous Post

RAMADAN KARIM: 17-1447

Next Post

RAMADAN KARIM: 18-1447

Related Posts

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)

March 1, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)

February 25, 2026
Next Post
RAMADAN KARIM: 18-1447

RAMADAN KARIM: 18-1447

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Reflections on the Nigerian Public Service: Way Forward for Governance

Reflections on the Nigerian Public Service: Way Forward for Governance

March 9, 2024
RAMADAN KARIM: 16-1447

RAMADAN KARIM: 16-1447

March 5, 2026
Matsalolin Da Suka Daƙile Super Eagles Daga Gasar Kofin Duniya

Matsalolin Da Suka Daƙile Super Eagles Daga Gasar Kofin Duniya

November 17, 2025
Ɗalibi Ɗan Najeriya Ya Mutu A Yayin Faɗa A Amurka

Ɗalibi Ɗan Najeriya Ya Mutu A Yayin Faɗa A Amurka

June 29, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)
  • JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles

Double or Die: Thrills, Suspense and Puzzles

April 5, 2026
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (9)

April 4, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.