FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)

__________
BABI NA BIYU
√ Wane Ne Tukur Tingilin?
Masu iya magana sun ce, a san mutum a san cinikinsa, ko kasuwa a san dillali. Shin wane ne Tukur? Yaushe kuma a ina aka haife shi? Su wane ne iyayensa, kuma yaya rayuwarsa ta kasance, tun daga yarinta har zuwa yau da muke rubuta wannan babi?
Kamar yadda ake ta jin Tukur…Tukur…Tukur, to cikakken sunansa dai Tukur Hassan Tingilin. An haife shi a Unguwar Tingilin Malumfashi, Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina, a ranar Asabar – 4 ga Rajab, 1398 (Hijiriyya), daidai da 10 ga Yuni, 1978 (Miladiyya).
√ Su Wane Ne Iyayensa?
Sunan mahaifinsa Malam Hassan kuma shi ma ɗan asalin Malumfashi ne, wanda ya yi makarantar Allo a Unguwar Holi, Malumfashi, a Makarantar Malam Lawal. A nan gidan Malam ya zauna a matsayin Almajiri har zuwa adadin lokacin da ya mallaki abin da ake buƙata na ilimin Ƙur’ani. Daga bisani ne ya tashi daga Unguwar Holi, zuwa Unguwar Tingilin, inda ya gudanar da rayuwarsa ta iyali.
Malam Hassan ɗan kasuwa ne. Ya yi harkar kasuwanci a kasuwar Malumfashi, har zuwa lokacin da Allah ya amshi rayuwarsa. Ya rasu a cikin watan Janairu na shekarar 1991, bayan rashin lafiya, shekara 36 ke nan a yanzu (2026). Allah ya ji ƙan shi da rahama, amin.
Mahaifiyar Tukur, Hajiya Zainabu, ita ma ‘yar Malumfashi ce kuma ‘yar uwa ce ga mahaifinsa, domin kuwa abokiyar wasansa ce. Zumunci ne ya yi ranarsa, ya ƙarfafa, har ya kai su ga aure kuma suka rayu da juna har sai da ta Allah ta raba – mutuwa.
Hajiya Zainabu ta ci gaba da rayuwa har zuwa watan Nuwamba na shekarar 2018, shekara 8 ke nan yau da ita ma ta koma ga Allah mahalicci. Tun daga wannan lokaci, Tukur ya zama maraya gaba da baya. Kodayake an ce babu maraya sai raggo. Tabbas, Tukur ba raggo ba ne, kamar yadda za mu gani a yadda rayuwarsa ta gudana a bayansu har zuwa yau ɗin nan.
ZA MU CI GABA IN SHA ALLAH!
__________













