RAMADAN KARIM: 10-1447

__________
‘Yan uwa, ina yi maku sallama irin ta Musulunci, Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Bayan haka, a yau Juma’a, Allah ya nuna mana rana ta 10 a Ramadan. Yau ma ga ‘yar nasiha:
Ma sha Allah! A yau nasiharmu za ta yi ishara ne zuwa ga girman rahamar Allah. Don haka, a matsayinmu na bayinsa, lallai ne mu kasance cikin godiya a kowane lokaci, kasancewar duk inda muka duba, tun daga halittar jikinmu da yadda rayuwarmu take gudana, za mu gane cewa lallai muna cikin rahamar Allah.
A cikin Suratul A’raf 7:156, Allah (swt) ya bayyana cewa: “Rahamata ta yalwaci komai.” Haka ma, Manzon Allah (saw), a ruwayar Bukhari, Hadisi mai lamba 7376 da Muslim, a Hadisi mai lamba 2319, ya ce: “Mai rahama, Allah zai yi masa rahama.”
‘Yan uwa, mu kasance cikin yaƙinin samun rahamar Allah a kowane lokaci. Mu yi ƙoƙarin kiyaye dokokinsa daidai iyawarmu.
Tare da wannan nasiha, muna roƙon ‘yan uwa da mu saka ɗan uwanmu, Injiniya, Dokta Tukur Tingilin cikin addu’a. Allah ya yi masa rasuwa a jiya Alhamis, a sakamakon haɗarin mota. Allah ya ji ƙan shi da rahama. Amin-Summa-Amin!
__________













