• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, May 18, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (5)

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
January 4, 2026
in Gizago
0
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (5)

Al'ummar Hausawa Da Fulani 'yan uwan juna ne a addini da al'ada da zaman tare

39
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (5)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Al’ummar Hausawa Da Fulani ‘yan uwan juna ne a addini da al’ada da zaman tare


                         __________
√ Wasu Muggan Manufofin Ƙungiyar Hausawan Bogi:
Malam Lamiɗo Suleiman Dungal, ɗaya daga cikin masana masu nazarin illolin da ke tattare da Ƙungiyar Hausawa Zalla ko kuma Hausawan Bogi, ya zayyano wasu daga cikin munanan ƙudurori da manufofinsu. Daga ƙarshe dai nazarin nasa ya tabbatar mana da cewa ita wannan karkatattar ƙungiya, an tsira ta ne da mugun ƙudurin tarwatsa Arewa da al’ummarta.

A wannan nazari nasa mai ƙima, Malam Lamiɗo ya kawo wasu bambance-bambancen da ke tsakanin wannan ƙungiya ta Hausawa Zalla da sauran ƙungiyoyin ƙabilu, waɗanda aka kafa da nufin bunƙasa al’ummarsu da taimakon juna. Ga bayanin nan daki-daki:

√ A yayin da sauran ƙabilu suke kafa ƙungiya domin inganta rayuwar al’ummarsu, ba wai don ware kansu daga sauran al’umma ba, su Hausawan Bogi sun bayyana ƙarara cewa babu ruwansu da wata ƙabila sai tasu. Alhali sauran ƙungiyoyin suna bai wa abokan zaman rayuwa damar musharaƙa da juna, ba tare da la’akari da ƙabila ba.

√ Shugabannin sauran ƙungiyoyin ƙabilu ba su kafirta ko cin mutuncin wata ƙabila, sai dai su yi aiki tuƙuru don ci gaban ƙabilarsu. Amma ƙungiyar Hausawa Zalla tana yawan rikici da wasu ƙabilu, musamman ma Fulani, waɗanda take zagi da la’anta tare da jan hankalin al’umma domin a tsane su kuma a ƙyamace su.

√ Ƙungiyoyin ƙabilu na gaskiya suna da bayyanannun shugabanni kuma ba sa ɓoye asali ko shaidarsu. Suna aiki tare da kowace gwamnati. Amma a ɓangaren Hausawa Zalla kuwa, ba a san shugabanninta ba, ba su fitowa fili. Babu abin da suke yi sai dai su riƙa yaɗa saƙonni a kafafen sada zumunta, domin kawo ruɗani. Saƙonnin nasu suna ɗauke da gubar ƙabilanci da cin zarafi da zage-zage.

√ Masu kiran kansu Hausawa Zalla, ba su da ofis kuma ba za ka samu wanda ya fito fili ya ce shi memba ba ne. A kafafen sada zumunta ma suna ɓoye sunayensu na ainihi, suna rufe bayaninsu (profile), ta yadda mutum ba zai fahimci ko su wane ne ko adireshinsu ba.

√ Ƙungiyar Hausawa Zalla, yawancinsu ma ba Musulmi ba ne, domin shugabarsu ta fito a kafafen sada zumunta tana cin mutuncin Musulunci, tana cewa ƙabilanci ya fi addini muhimmanci. Tana faɗin cewa hatta kashi ko najasar Bahaushe ta fi Musulunci.

√ Wata babbar alama ko tambarin ‘yan Ƙungiyar Hausawa Zalla ita ce, tsana da ƙiyayya da Musulunci da Musulmi. Duk wani malamin Musulunci, tun daga Mujaddadi Shehu Ɗanfodiyo zuwa malamanmu na zamanin nan, babu wanda ba su ci wa zarafi, suka zage shi ba. Kuma za ka ga suna goyon bayan masu gwagwarmayar kafa ƙasar Inyamurai ta Biyafara kuma suna zuzuta wutar gaba da goyon bayan ƙabilun Middle Belt a kan Fulani.

√ A hannu ɗaya, ƙungiyoyin Fulani da makamantansu da aka kafa don maslahar rayuwa, ƙungiyoyi ne na makiyaya da al’umma baki ɗaya. Duk wanda ke kiwo, ko daga wace ƙabila yake, ana iya ba shi dama ya shiga cikinsu, har ma ya shugabanci ƙungiyar. Wannan ne ya sa a cikin shugabannin ƙungiyoyin Fulani ake samun waɗanda ba Fulani ba. Haka ma a ƙungiyoyin manoma ko mahauta, duk za ka samu bayaninsu da ayyukansu a bayyane kuma suna da rijista da hukumomin ƙasa, alhali ita wannan ƙungiya ta Hausawa Zalla, ba ta da rijista, ba ta da ofis kuma ba a san membobinta da shugabanninta ba a zahiri. Wasu ma ba ‘yan Najeriya ba ne kuma ba a nan suke zaune ba.

Wani babban abin lura a nan shi ne, babu wanda zai hana kowace ƙabila kafa ƙungiya domin kare haƙƙin al’ummarta, komai ƙanƙantarta, ballantana babbar ƙabila irin ta Hausawa. Matsalar ita ce, ba a kafa ƙungiya da niyyar cin mutuncin wata ƙabila ko addini. Ba a kafa ƙungiya ba tare da bayyanannen shugaba ɗaya ba. Dole ƙungiya ta kasance an san ta kuma tana da rijista da gwamnati kuma tana da ofis kuma ayyukanta su kasance bayyanannu ga jama’a, ba a ɓoye ba.

A nan za mu ɗiga aya, tare da fatan sake haɗuwa a tsokaci kashi na 6. Da fatan muna fahimtar illolin wannan karkatattar ƙungiya da muggan manufofinta na kassara al’ummar Arewa.
__________

Previous Post

Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci

Next Post

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur - Dokta Tukur Tingilin

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

NO TO WAR

NO TO WAR

June 20, 2025
UNDP Partners Kaduna Ministry to Build Peace in the State

UNDP Partners Kaduna Ministry to Build Peace in the State

September 20, 2023
Prince Abdussamad Badamasi: Allah Tashi Kafaɗarka

Prince Abdussamad Badamasi: Allah Tashi Kafaɗarka

October 9, 2025
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (12)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (12)

January 31, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki
  • Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447
  • ALHAMDU LILLAH

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki

Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki

May 18, 2026
Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.