Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (4)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
√ Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Batun Ramuwar Gayya:
Ya ku ‘yan uwa masu bibiyar wannan muƙala da jimiri, a wannan fitowa kashi na huɗu, za mu ci gaba da bayani dangane da wasu munanan manufofi da muka ankara da su daga ‘ya’yan Ƙungiyar Hausawa Bogi, musamman yadda suke nuna su a kafafen sadarwa na zamani (Soshalmidiya).
Ga duk mai tu’ammali da waɗannan kafafe, babu shakka zai riƙa gamuwa da munanan kalaman masu ƙumajin kafa Ƙungiyar Hausawa Zalla. Ɗaya daga cikinsu shi ne, za su kafa wannan ƙungiya ce, kacokan da nufin haddasa gaba da ƙiyayya tsakanin al’ummar Arewa, musamman ma dai tsakanin Fulani da Hausawa. Babbar manufarsu ita ce, ramuwar gayya da ɗaukar fansa a kan musamman Fulani.
A ƙoƙarinsu na bayyana wannan muguwar manufa, ƙarara za ka ji sun kama sunan Mujaddadi Usman Ɗanfodiyo, suna zagin shi da tozarta shi; sannan kuma suna ƙirƙirar tarihin ƙarya suna jingina masa. Ba shi kaɗai ba, masu wannan ƙungiya ta Hausawa zalla, za ka ga suna ta haƙilon haddasa gaba da husuma tsakanin al’ummar Musulmi. Su a nufinsu, al’ummar Fulani gaba ɗayansu ‘yan ta’adda ne, don haka ya kamata Hausawa su tashi su yaƙe su gaba ɗaya.
To, abin tambaya a nan shi ne, shin anya kuwa akwai alheri ga ƙungiyar da take bijiro da irin waɗannan baƙaƙen halaye? Shin da gaske ne, cewa Sheikh Usman Ɗanfodiyo (ra) bai shuka alheri ba a ƙasar Hausa? Shin wai ma da suke kiran dukkan Fulani da sunan ‘yan ta’adda, musamman kasancewar wasu daga cikinsu suna garkuwa da mutane da ta’addanci a yankin nan, shin a rigar ƙungiyoyin Fulani suke gudanar da wannan ta’addanci? Shin wannan ta’addanci da wasu baragurbin Fulani suke aikatawa, Hausawa kaɗai suke kamawa da kashewa?
Za mu bi tambayoyin nan ɗaya bayan ɗaya, inda da yardar Allah, za mu ida fahimtar gaskiyar manufar masu ƙungiyar Hausawa, cewa ba wani abu suke ɗauke da shi ba sai babbar guba da dasisar wargaza al’ummar da ke zaune lafiya da juna na tsawon zamani.
Game da Sheikh Usman Ɗanfodiyo (ra) kuwa, babu shakka, duk wani mai kyakkyawan tunani, musamman idan dai shi Musulmi ne na ƙwarai; to ba zai taɓa kushe Mujaddadi ba. Domin kuwa Sheikh ya kafa babban tarihi, abin yabawa a duniyar Musulunci. Daular Muslunci ta Sakkwato da ya kafa, tun kimanin sama da shekara 200 da ta gabata, ta kasance daula mafi girma da bunƙasa a Afrika ta Yamma.
Ya jaddada Musulunci. Ya yaɗa ilimi. Ya kafa gwamnati mai tsari, abin alfaharin baƙar fata, tun kafin zuwan Turawa. Ya kafa tsarin tafiyar da al’umma mai cike da adalci da ɗa’a da nagarta – wanda har zuwa yau ana cin gajiyarsa.
Jama’a, yau ma a nan zan dakata. Sai kuma karo na gaba, in sha Allahu. A ci gaba da bibiyar mu da haƙuri. Muna kuma maraba da dukkan martani, ƙarin bayani ko tambaya a Comment Section.
_______________













