• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

BAKIN JAƁA (6)

Labarin Cin Amana

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 1, 2025
in Adabi
0
BAKIN JAƁA (6)

Bakin Jaɓa (6)

62
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

BAKIN JAƁA (6)
(Labarin Cin Amana)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Bakin Jaɓa (6)


                       _______________
Haka dai Jummalo ta ci gaba da zama a gidansu, ita da mahaifiyarta duk suna zaman jawarci, kodayake ita tana ɗauke da ciki, haihuwa ko yau ko gobe. Ita kuwa mahaifiyar, tana aikin koyarwa ne a makarantar firamare ta unguwarsu.

Related posts

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

January 17, 2026
SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025

A haka lokacin haihuwarta ya yi. Nan ma sai da aka samu taƙaddama tsakaninta da tsohon mijin nata. Lokacin da alamun maƙuda suka bayyana, sai mahaifiyarta ta aika wa surukanta da saƙo, cewa suna neman Naira miliyan biyar domin zuwa asibiti. Su kuma suka ce ba za su bayar da ko kwabo ba, illa iyaka za su kai ta asibitin da iyalinsu suke zuwa. Asibiti ne mai zaman kansa, kuma an shaida cewa ba ƙaramin asibiti ba ne.

Haka aka yi ta kai ruwa rana, daga ƙarshe dai a kan dole suka haƙura, suka amince ta je wannan asibiti. Wani abin ikon Allah ma, ko da aka kwantar da ita a gadon jinya, ko awa biyu ba ta yi ba ta haihu. Ta haifi namiji.

Jummalo da mahaifiyarta, ganin cewa ba su yi nasarar tatsar kuɗi masu yawa ba a yayin zaman jego, sai kuma suka ƙara shirya wata yaudara. Sun yanke cewa ba za ta shayar da jaririn ba, sai an ba ta kuɗin shayarwa. Al’amari ya yi ƙamari, har sai da aka zauna gaban alƙali.

Mahaifin Jummalo ya yi matuƙar baƙin ciki da wannan mataki da suka ɗauka. Gari ya ɗauka da ɗumi yadda ɗiyarsa ta zubar masa da mutunci. Lamarin ya zama abin tattaunawa a majalisu. Haka ma abin ya kasance a tsakanin mata, a gidajen biki ko suna. Masu zunɗe suna yi, masu shaguɓe ma suna nasu aiki.

Kafin a yi zaman kotu na ƙarshe, Jummalo ta nemi a riƙa ba ta Naira dubu ɗari biyar duk wata, a matsayin kuɗin shayarwa. Daga ƙarshe dai aka daidaita, cewa Mamman zai riƙa ba ta Naira dubu ɗari biyu duk wata.

“To, kuma za a ƙirga tun daga watan da na haihu, a biya ni.” In ji Jummalo, tana magana a gaban alƙali.

Jin wannan batu, sai alƙali ya daka mata tsawa. “Ke wace irin shashasha ce?”

Nan da nan Jummalo ta zuciya, ta turɓune baki tana ƙunƙunai. Alƙalin kuwa ya lura da haka. Nan da nan ya umurci ɗan sanda da ya kai ta ajiya gidan yari. Daga bisani kuma ya ba masinja takardar sammaci, a kai wa mahaifinta.

Wanshekare aka sake hallara a gaban kotu, Alƙali bai zauna a zauren kotu ba, a ofishinsa ya zauna da su. Ya aika an kawo Jummalo daga gidan yari, har da mahaifinta da mahaifiyarta sun hallara, a gefe ɗaya kuma ga Mamman Big Boy.

“Kai ne mahaifin yarinyar nan ko?” Alƙali ya tambayi babanta. Bai jira ya amsa ba sai ya ci gaba da magana. “Ko kaɗan ban ji daɗin irin tarbiyyar da ka ba ta ba. Ba ta da kunya ko kaɗan…”

Koda mahaifin Jummalo ya ji rashin kunyar da ɗiyarsa ta yi wa alƙali, bai san lokacin da hawayen takaici ya fara zuba daga idanunsa ba. “Ke dai Allah wadaran halinki.”

A haka ne ya roƙi Alƙali aka kashe maganar, tare da sharaɗin cewa Naira dubu 200 za a riƙa ba ta, a matsayin kuɗin shayarwa.

An samu tsawon wata uku Mamman yana biyan wannan adadin kuɗi. A wata na huɗu sai aka samu akasi bai kai mata kuɗin ba kan lokaci. Jinkirin kwana biyar aka samu, domin ya yi tafiya wani gari. Jummalo ta neme shi a waya ba ta samu ba. Ai kuwa ba ta yi shawara da kowa ba, sai ta haɗa akwatin yaron da kayansa, ta ɗauke shi ta kai ƙofar gidan tsohon mijin nata ta kwantar da shi. Yana tsaga kuka, haka ta juya baya ta bar shi yana ta wutsul-wutsul da ƙafafu.

Dayake gidan Mamman daban yake, nesa kaɗan da gidan iyayensa , babu wanda ya ankara da wannan ɗanyen aiki, kasancewar babu motsin mutane a wurin.

Sai da aka ɗauki kimanin awa uku da faruwar lamarin sannan Jummalo ta aika wa Mamman tes. “Ba na buƙatar kuɗinka na shayarwa, ka riƙe abinka. Kuma daga yau na daina shayar da yaronka. A yanzu haka ma yana can ƙofar gidanka. Idan kana buƙatarsa ka je ka ɗauki kayanka.”

Koda Mamman ya karanta wannan saƙo sai ya kiɗime. Nan take kuwa ya amince da cewa za ta iya wannan shirmen, musamman ya yi zargin cewa ta sha ƙwaya. Hakan ya sa nan da nan ya sanar da mahaifiyarsa abin da ake ciki.

Koda aka je ƙofar gidan Mamman, an samu jariri ya ci kuka har ya daina don ƙashin kansa. Ya saka yatsa a baki yana tsotsa amma duk ya galabaita. Koda aka kai shi asibiti, kafin ma a fara yi masa magani ya ce ga garinku nan. Ya m+tu.
(Za Mu Ci Gaba)
_______________

Previous Post

NAJERIYA A 65: MU SAKE DUBAWA

Next Post

ALLAH YA JI ƘAN HAUWA ƘAMSHI

Related Posts

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a
Adabi

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

January 17, 2026
SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)
Adabi

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine
Adabi

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025
Next Post
ALLAH YA JI ƘAN HAUWA ƘAMSHI

ALLAH YA JI ƘAN HAUWA ƘAMSHI

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

August 18, 2023
ZUWA GA ‘YAN UWA MUSULMI ‘YAN SHI’A: SHIN DA GASKE KUNA KOYI DA ALI (RTA) NE?

ZUWA GA ‘YAN UWA MUSULMI ‘YAN SHI’A: SHIN DA GASKE KUNA KOYI DA ALI (RTA) NE?

July 23, 2025
SHEIKH ƊAHIRU BAUCHI YA CIKA SHEKARA 100 CIF A DUNIYA

SHEIKH ƊAHIRU BAUCHI YA CIKA SHEKARA 100 CIF A DUNIYA

July 8, 2024
Bayan Nasara A Kotun Ƙoli, Shugaba Tinubu Zai Ci Gaba Da Aikin Gina Nagartacciyar Ƙasa – Idris

Bayan Nasara A Kotun Ƙoli, Shugaba Tinubu Zai Ci Gaba Da Aikin Gina Nagartacciyar Ƙasa – Idris

October 28, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.