SAƘON ADDU’A DA TAYA MURNA GA SHUGABAN JAMI’AR FUDMA: FARFESA AMINU ADO KAFUR
Daga Sani Ahmed Malumfashi

__________
Ni Sani Ahmed Malumfashi da dukkan iyalai da ‘yan uwa da abokan arziki, muna miƙa saƙon addu’a da taya murna ga mai girma Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya Dutsin-ma, Jihar Katsina, Farfesa Aminu Ado Ƙafur.
Wannan babban matsayi da shugabanci da ka samu, ya nuna ƙarara irin jajircewarka, hangen nesa, da kuma kishinka wajen ciyar da harkar ilimi gaba a Najeriya.
Zaɓen ka ba abin mamaki ba ne ga duk wanda ya san ka, ko kuma yi aiki tare da kai. Ka daɗe kana nuna ƙwarewa a harkar shugabanci, gaskiya da riƙon amana, da kuma jajircewa wajen ganin an cin ma nasara a dukkan al’amura. Halayenka na tausayi, adalci da kuma ƙwarewa sun sa kowa yake girmama ka, ya kuma koyi abubuwa masu amfani a ƙarƙashin jagorancinka.
A matsayinka na shugaba, kana jagoranci da haƙuri da hangen nesa, kana kuma ƙarfafa gwiwar ma’aikata da abokan aiki. Ka kafa kyakkyawan tarihi na iya mu’amala da kowa, kana sauraron kowa, kana kuma ba kowa dama ya nuna ƙwarewarsa. Waɗannan halaye naka na musamman, za su taimaka matuƙa a sabon matsayin da Allah ya ɗora maka.
A baya, ka sha nuna ƙwarewa wajen haɗa kan jama’a da kawo cigaba. Muna da yaƙinin cewa, Jami’ar FUDMA za ta ƙara haɓaka da bunƙasa a ƙarƙashin jagorancinka, ta fuskar ingancin karatu, bincike, da kuma rawar da jami’ar ke takawa a ci gaban ƙasa. Salon shugabancinka mai cike da tawali’u da hangen nesa ne – daidai abin da ake buƙata a wannan lokaci.
Wannnan sabon matsayi da Allah ya ba ka, yana ɗauke da manyan nauye-nauye da ƙalubale iri-iri, amma muna da tabbacin cewa za ka shawo kansu da ƙwarewa da kwarjini tare da taimakon Allah. Ƙwarewarka, nutsuwarka, da kuma adalcinka za su taimaka matuƙa wajen tafiyar da al’amuran jami’ar cikin kwanciyar hankali da ci gaba.
Mu, a matsayinmu na yaranka, waɗanda muka amfana da shiriya da jagorancinka, muna alfahari da wannan babban ci gaba da ka samu. Wannan nasara ba taka kaɗai ba ce – ta dukkanmu ce. Muna fatan Allah ya ƙara ɗaukaka ka, kuma ya ba ka nasara a dukkan matakan rayuwa.
Yayin da kake fara wannan sabon babi na rayuwarka, muna roƙon Allah ya ƙara maka basira da lafiyar jiki da ta zuciya. Allah Ya ba ka ikon sauke nauyin da aka ɗora maka cikin nasara. Muna fatan alheri da ganin nasarori masu tarin yawa a lokacin mulkinka a matsayin Shugaban Jami’a Federal University Dutsin-ma.
Wasallam.
Naka da ladabi da biyayya,
Sani Ahmed Malumfashi













