Muhammad Salissou Hamissou: Ta’aziyyar Ƙwararren Ɗan Jarida Mai Raya Al’adun Gargajiya
Daga Bukar Usman

Tare da cikakken alhini nake rubuta wannan ta’aziyya, domin tunawa da sanannen ɗan jarida, makusanci kuma aboki, Muhammad Salissou Hamissou, wanda Allah Ya amshi ransa a ranar Laraba, 14-02-2024, a sakamakon haɗarin mota.
Marigayin, ɗan asalin Jamhuriyyar Nijar, Hamissou, kafin rasuwarsa ya kasance wakilin Sashen Hausa na Gidan Rediyon Faransa (RFi) da ke Legas. Tun da farko dai, abokinmu Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, sanannen marubuci a Najeriya kuma ɗan fim ne ya fara gabatar mani da marigayin a shekarar 2009. Shi Ado, kamfaninsa na wallafa, Gidan Dabino Publishers Kano ne ya wallafa mani littattafaina na Hausa. Tun daga wannan gabatarwa, marigayi Hamissou bai ɓata lokaci ba, ya gayyace ni zuwa gidan rediyon na Rfi da ke Legas, inda muka tattauna game da rubuce-rubucena da suka shafi adabi, musamman ma dai littattafaina na tatsuniyoyi na Hausa.
A yayin amsa wannan gayyatar, tare da Gidan Dabino muka je gidan rediyon, a mazauninsa da ke Legas. Tattaunawar tamu ta shafi babban kundina na Taskar Tatsuniyoyi, wanda ke ƙunshe da littattafai 14 da na wallafa cikin harshen Hausa. Marigayin ya yi mamaki ƙwarai, ganin cewa ni ɗan ƙabilar Babur/Bura ne amma na wallafa littattafai da Hausa, duk da cewa ba yarena ne na gado ba. Haka kuma abin ya burge shi, yadda na zaɓi farfaɗo da tatsuniya, ɓangaren adabin da ya kusa macewa kuma aka banzatar da shi.
Babu shakka marigayin ƙwararren ɗan jarida ne da ya ginu da son jin kowane ɓangare, a yayin tattaunawa tsakanin mutane. Ya aminta da batuna, cewa lallai bai kamata a bar al’adunmu na gargajiya su mutu ba, musamman ma al’adunmu masu amfani, masu ilimantarwa, masu koya ɗa’a da tarbiyya ga al’umma. Kan haka, Hamissou ya tattauna da ni dangane da wasu rubuce-rubucena da suka danganci al’adu da tarihi, ciki har da littafin Tarihin Biu, wanda a cikinsa na samar da bunƙasasshen bayani da ya shafi al’adun Daular Biu, mahaifata. Daga bisani kuma ya tattauna da ni game da kyaututtukan karramawa da aka ba ni saboda ayyukana na hidimar adabi. A nufinsa, wannan tattaunawar za ta ƙarfafi mutane, domin su tsunduma cikin nazari da bincike a kan al’adu.

Babu wai, masu sauraren tashar Hausa ta RFi za su rika tunano zazzaƙar muryar Hamissou mai armashi da jan hankali, a duk lokacin da yake gabatar da shirye-shiryensa. Shi ya kasance gwanin mai watsa labarai, ƙwararren ɗan jarida, kamar kuma yadda ya kasance gwanin marubucin rahoto kuma mai gabatarwa. Za a riƙa tuna shi ta fuskar yadda yake bayar da sahihan labarun Hausa da kuma tasirin shirye-shiryen da yake gabatarwa na Hausa, masu muhimmanci, masu armashi da inganci.
Haka kuma masu sauraren Sashen Hausa na RFi, za su riƙa tuna marigayin dangane da ƙayatattun shirye-shiryensa da yake gabatarwa na Al’adunmu Na Gado da kuma Dandalin Fasahar Fina-finai. Ya sha gabatar da tattaunawata da labaruna da dama a waɗannan shirye-shirye nasa. Ganin yadda a kowane lokaci nake jaddada muhimmancin fina-finan tatsuniyoyi da katun, domin koya ɗa’a da tarbiyya ga yara da kuma yadda nake ta buƙatar ganin yadda za a juya wasu daga cikin tatsuniyoyin da na wallafa zuwa fina-finan katun, su saka sanya ya ga dacewar ya tattauna da ni a shirin Dandalin Fasahar Fina-finai. Haka kuma duk da cewa shi ɗan asalin Jamhuriyyar Nijar ne, Hamissou ya ba da gudunmowa mai yawa wajen bunƙasa al’amuran fina-finai a Najeriya.
Gidan Rediyon RFi ya ciri tuta wajen bunƙasa al’adu, musamman yadda ya samar da shirye-shirye ta wannan fuska. Wasu daga cikin irin waɗannan muhimman shirye-shirye, Hamissou ne ya ƙirƙiro su kuma shi ya riƙa gabatar da su cikin armashi. Ya kasance jajirtacce wajen ƙoƙarin tattara rahotannin da suka shafi al’adun gargajiya. A matsayina na Shugaban Ƙungiyar Raya Fasahohi Da Al’adun Gargajiya Na Najeriya, wato Nigerian Folklore Society (NFS), na taɓa gayyatar marigayin zuwa babban taron ƙungiyar da aka gudanar a Jami’ar Bayero Kano a shekarar 2014. Haka kuma na tuno kuma na yaba matuƙa, yadda ya kewaye wasu makarantu a Babban Birnin Tarayyar Najeriya Abuja, inda ya gudanar da tattaunawa daban-daban dangane da muhimmancin littattafan tatsuniyoyi da Gidauniyar Dokta Bukar Usman ta raba kyauta ga wasu makarantu da cibiyoyin ilimi. Ya tattara waɗannan tattaunawa da rahotanni kuma ya gabatar da su a tashar Rediyon RFi cikin ƙwarewa da armashi.
Hamissou mutum ne mai sha’awar al’amuran al’umma, musamman ma dai waɗanda suka danganci al’adu da batun abin da zai kawo ci gaban al’umma. A misali, ya taɓa nuna damuwa game da yadda hukumomin ilimi suka soke koyar da darussan tarihi a makarantun Najeriya. Kan haka ya gudanar da tattaunawa daban-daban da masu ruwa da tsaki a batun, domin bin kadin dalilan ɗaukar wannan mataki. Dukkan mutanen da marigayin ya tattauna da su a kan al’amarin, cikinsu har da Gangaran Farfesa Ɗandatti Abdulƙadir, wanda fitaccen masanin tarihi ne da Gidan Dabino da ni kaina, dukkanmu mun yi ittifakin cewa wannan mataki bai dace ba ko kaɗan. Mun jaddada cewa, duk mutumin da bai san daga inda ya fito ba, ba zai taɓa sanin inda ya nufa ba. Abin farin ciki shi ne, a sanadiyyar ƙorafe-ƙorafen da masu ruwa da tsaki suka yi ta yi da kuma yadda mutane suka nuna damuwa kan lamarin, sai aka soke wannan ƙuduri.

Na shiga damuwa kuma na kaɗu sosai, lokacin da labarin rasuwar Muhammad Salissou Hamissou ya ishe ni, a ranar Alhamis, 15 ga Fabrairu, 2024. Ya gamu da haɗarin mota ce, a yayin da yake dawowa Najeriya, bayan ya ziyarci iyalansa da ke Jamhuriyyar Nijar.
Ganawa ta da shi ta ƙarshe, ita ce a ranar 29 ga Janairu, 2024, lokacin da ya kawo mani ziyara a Abuja. A wannan lokacin, mun tattauna al’amuran siyasar Afirka ta Yamma. Na nuna wa marigayin wasu sababbin littattafai nawa da na wallafa (My Literary Works: Reviews and Reports da Conversations with Bukar Usman). A ɗaya daga cikin littattafan biyu, akwai dukkan tattaunawar da shi marigayin ya yi da ni. Mun ma tsaida maganar cewa idan ya dawo daga wannan tafiya, zai biyo ta wajena kafin ya wuce zuwa Legas, domin ya amshi nasa littattafan da kuma waɗanda zai kai wa wurin aikinsa, RFi. Ikon Allah! Ashe wannan ita ce ganawarmu ta ƙarshe. Malam Hamissou dai ya rasu ne ya bar matar aure ɗaya da ‘ya’ya, waɗanda a cikinsu ma har da wanda yake aikin soja a ƙasashen waje.
Rasuwar Hamissou babban rashi ne a gare ni, musamman na rasa aboki mai amana, ƙwararren wakili a aikin jarida, ƙwararren mai karanta labarai, ƙwararren ɗan rahoto na ji da gani. Ya kasance mutumin kirki mai zumunci. Tun daga ranar da na fara haɗuwa da shi har zuwa ƙarshen rayuwarsa, ya kasance mai zumunci da sakakkar fuska a gare ni. Ina ta’aziyya cikin alhini da tausayi zuwa ga iyalansa da dukkan abokan aikinsa da ɗimbin masu sauraren shirye-shiryensa a RFi da abokan arziki. Allah Ya ji ƙan shi da rahama, Ya saka shi gidan farin ciki – Aljanna Firdausi. Allah Ya kyautata bayansa, Ya ba su hakuri.
__________
Bukar Usman, tsohon Babban-Sakatare a Fadar Shugaban Kasa ne kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Raya Fasahohi Da Al’adun Gargajiya Na Najeriya, wato Nigerian Folklore Society (NFS).













