• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, August 27, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Muhimman Ayyukan Da Shugaba Tinubu Ya Ɗora Mani – Ministan Yaɗa Labarai

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
October 19, 2023
in Labarai
0
Muhimman Ayyukan Da Shugaba Tinubu Ya Ɗora Mani – Ministan Yaɗa Labarai

Shugaba Bola Ahmad Tinubu

25
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Muhimman Ayyukan Da Shugaba Tinubu Ya Ɗora Mani – Ministan Yaɗa Labarai

Daga Wakilinmu

Related posts

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne

August 17, 2026
Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

August 13, 2026

~~~~~~~
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ɗora masa nauyin jaddada tasirin kishin ƙasa, aiki da gaskiya da kuma kawar da nuƙu-nuƙu, a matsayin kyawawan ɗabi’un da gwamnatin sa za ta ɗore kan turbarsu.

Ministan ya bayyana haka a cikin tattaunawar da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), a Abuja.

Ya ce ajandar Fata Nagari Lamiri da Gwamnatin Shugaba Tinubu ta hau mulki da ita, wani kyakkyawan muradi ne na ɗaukaka Nijeriya zuwa ƙololuwar nasara da bunƙasa a cikin manyan ƙasashe na duniya, tare da goge baƙin fentin da ake kallo a jikin wannan ƙasa.

Idris ya ce Tinubu ya hore shi da cewa ya tabbatar ya samu nasarar wayar da kan ‘yan Nijeriya cikin shekaru kaɗan masu zuwa, ta yadda aƙalla za a iya sake kankaro ƙima da martabar ƙasar nan, tare da fara ɗora ta bisa kyakkyawar turbar da ta fi dacewa ta bi.

“Wannan kuwa babban kalubale ne. Saboda kun dai san ba a zukatan matasa kaɗai ɗa’a da kishi suka yi ƙaranci ba, har ma a zukatan yara da manya.

“Ina ganin dalili ke nan shugaban ya canja wa sunan Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Bunƙasa Al’adu, zuwa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai.

“Hakan ke nan yana nufin Shugaban Ƙasa na so a ɗora batun wayar da kai da cusa kishin ƙasa a sahun gaba,” cewar Idris.

Ministan ya ƙara da cewa tasirin kishin ƙasa da aiki da gaskiya da Tinubu ke ta faɗi-tashin cusawa da kwaɗaitarwa.

“Ya ba mu umarnin kai-tsaye cewa mu tabbatar waɗannan kyawawan ɗabi’u da halaye nagari sun kasance jigo a ƙoƙarin faɗakar da akasarin ‘yan Nijeriya.”
~~~~~~~

Previous Post

Za Mu Sake Dasa Wa Al’ummar Nijeriya Ɗabi’ar Yarda Da Kalaman Shugabanni – Minista Idris

Next Post

The Bloomsbury Handbook of Muslims and Popular Culture: An Endorsement

Related Posts

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne
Labarai

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne

August 17, 2026
Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina
Labarai

Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

August 13, 2026
An Samu Sauƙin Matsalar Tsaro: Yanzu Dukkan Kasuwanninmu Suna Ci
Labarai

An Samu Sauƙin Matsalar Tsaro: Yanzu Dukkan Kasuwanninmu Suna Ci

August 12, 2026
Next Post
The Bloomsbury Handbook of Muslims and Popular Culture: An Endorsement

The Bloomsbury Handbook of Muslims and Popular Culture: An Endorsement

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Gwamnan Katsina Ya Raba Ma’aikatar Ilimi Zuwa Gida Uku

Gov. Raɗɗa Sponsors 40 Katsina Indigenes to Study Medicine Abroad

October 6, 2023
Taron editoci: Tinubu na so a riƙa yaɗa kyawawan labarai don jawo zuba jari a Nijeriya

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Minista Idris Cikin ‘Yan Kwamitin Garambawul

January 16, 2024
Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Eriya Malumfashi

Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Eriya Malumfashi

June 16, 2023
Na Yi Zaton Gwamna Badaru Ɗan Izala Ne

Na Yi Zaton Gwamna Badaru Ɗan Izala Ne

July 3, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • ALBARKAR HAUSA
  • Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)
  • Professor Bello Sa’idu: The Demise of a Literary Icon

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

ALBARKAR HAUSA

ALBARKAR HAUSA

August 26, 2026
Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)

Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)

August 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.