SAƘON JUMU’A: Daga Malam Anas Saminu Ja’en
~~~~~~~
A yau Juma’a, 21 ga Rabi’ul Awwal, 1445 (Hijriyya), daidai da 06 ga Oktoba, 2023 (Miladiyya), za mu fa’idantu da wannan muhimmin saƙo daga zaƙaƙurin matashi, Malam Anas Saminu Ja’en. Allah sa mu dace, Amin.
~~~~~~~
Ya Ubangijin Annabi Muhammadu ﷺ muna neman tsarin Ka daga dukkan sharri irin wanda Sayyiduna Rasulillahi ﷺ ya nemi tsari daga gare Ka. Ka ba mu ikon tsarkake zukatanmu da harshenmu, a duk inda muka tsinci kanmu cikin faɗin duniya.
Ƙuncin rayuwa da ake ciki, Allah ta’ala Ka yi mana maganinsa, Ka sada mu da alheri a duk inda muke kuma Ka dawwamar mana da shi har abada, tare da zuri’armu da masu ƙaunar mu, don darajar Annabi da Alƙur’ani!
– AMIN –
~~~~~~~












