• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, June 9, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Addini

Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 8, 2023
in Addini
0
Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

Jana'izar Sheikh Abubakar Giro Argungu, wanda ya rasu a Larabar da ta gabata

10
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

~~~~~~~
Wannan huɗubar an yi ta ne a ranar Juma’a, 01-02-1445 (Hijriyya)/18-08-2023 (Miladiyya), Limamin Masallacin Unguwar Tumbu da ke garin Madallah, Ƙaramar Hukumar Suleja, Jihar Neja; Liman ya buɗe huɗubarsa da godiya ga Allah Ubangijin talikai (swt), da salati da sallama ga Manzon Allah, Sallallahu alaihi Wasallam.

Related posts

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026

~~~~~~~

Maudu’in Huɗuba: Muhimmanci da wajibcin soyayyar juna tsakanin muminai.

Liman ya ce mu ji tsoron Allah, mu kyautata kuma mu ƙarfafa soyayyar juna da jaddada’yan uwantaka da zumunci. Ya ce muminai, musulmi ‘yan uwan juna ne da suka kasance kamar gini, wani sashe yana tallaba da ƙarfafa sashe.

Shin wai yaya soyayyar juna take? Liman ya ce idan za ka yi so, ka so don Allah da ManzonSa. Haka ma idan za ka nuna ƙi, to ka ƙi wanda ya ƙi Allah kuma ya ƙi Manzon Allah. Wannan ke nan yake nuna cewa Musulmi ya tabbatar da cewa, ya so ɗan uwansa Musulmi a duk lokacin da ya aikata aikin Allah. Haka kuma ya ƙi wanda ya ƙi Allah, wanda ke take dokokin Allah da ManzonSa.

Malam ya ce a ranar ƙiyama, za a rarrabe tsakanin Musulmi waɗanda suka so juna don Allah da waɗanda ba su yi haka ba. Waɗanda suka yi don Allah da ManzonSa ne kaɗai za su rabauta.

Babu wata alaƙa mai girma a gaban Allah da ManzonSa sai alaƙa da ‘yan uwantaka ta Musulunci. Kuma wajibi ne Musulmi ya yauƙaƙa dangantakarsa da ɗan uwansa ta hanyar taimakekeniyar juna.

Liman ya ce, a wannan zamani da ake cikin jarabawar rashin kuɗi da matsaloli iri-iri, shi ne lokacin da Musulmi ya kamata su taimaki juna. Mutum ya taimaki wanda bai da shi, mai ƙarfi ya tallafa wa mara ƙarfi. Wannan ne zai sanya so da ƙaunar juna a tsakanin Musulmi.

Liman ya yi sharhi kan wani hadisin Manzon Allah, wanda ke cewa, “Ba ya tare da mu, wanda ya ci ya ƙoshi alhali ɗan uwansa ya kwana da yunwa.” Wannan ke ƙara nuna mana cewa lallai ne mu taimaki juna, mu ƙarfafi juna, ta yadda marasa shi za su samu walwala a cikin al’umma.

Babu wata hanya da ke ƙarfafa soyayyar juna kamar taimakon juna. Musulmi su yawaita yin sallama tsakaninsu, domin sallama na kawo kusanci da soyayya kuma tana kai mutum zuwa aljanna. Kuma tana kawo yarda da haɗin kan al’umma. Tana magance gaba tsakanin al’umma. Don haka mu yawaita sallama, mu yawaita taimakon juna.

Liman ya ce Musulmi su kasance ‘yan uwan juna masu taushe fushi, masu yafiya ga juna, masu sakawa da kyakkyawa ga wanda ya aikata masu mummuna. Duk wanda ya kyautata wa ɗan uwansa, zai jawo ƙaunarsa kuma zai kusance shi. Hakan zai kawo zaman lafiya da haɗin kai kuma ya haifar da ƙarfi a cikin al’ummar musulmi.

Liman ya ce mu yi gaugawar ciyarwa ga ‘yan uwanmu marasa shi, mu taimaka wa addini, mu taimaka wa al’umma a lokacin tsanani da lokacin yalwa.

Ya ce Allah Yana son masu yafiya ga juna kuma Yana son masu kyautatawa.

Liman ya rufe huɗubarsa da addu’a, Allah Ya ƙarfafi al’ummar Musulmi, Ya wadata mu da ruwan sama mai albarka kuma Ya yaye mana wannan yanayi na ƙunci da rashin tsaro.
Amin summa Amin!
~~~~~~~

Previous Post

GIRO ALLAH KYAUTA MAKWANCI

Next Post

TASKAR GIZAGO Adds category

Related Posts

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447
Addini

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
Duniya Ba Gidan Zama Ba
Addini

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Mu Ji Tsoron Allah
Addini

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
Next Post
TASKAR GIZAGO Adds category

TASKAR GIZAGO Adds category

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Komawar Kwankwaso Zuwa APC: Gaba Kura Baya Sayaki

Komawar Kwankwaso Zuwa APC: Gaba Kura Baya Sayaki

July 21, 2025
RAMADAN KARIM: 06-1447

RAMADAN KARIM: 06-1447

February 23, 2026
Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC

Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC

April 9, 2026
Kishin Ƙasa Ne Tubalin Farko Na Gina Rayuwar Al’umma (2)

Barkwancin Ƙarshen Mako

July 22, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido
  • Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji
  • Wasu Daga Manyan Ayyukan Sardauna Ga Al’ummar Arewa (1954-1966)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

June 8, 2026
Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji

Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji

June 7, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.