• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, May 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Amana: Ita Ce Sinadarin Tabbatar Da Haɗin Kai, Aminci Da Zaman Lafiya A Najeriya

Sani Usman Kukasheka by Sani Usman Kukasheka
August 12, 2023
in Gizago
0
Amana: Ita Ce Sinadarin Tabbatar Da Haɗin Kai, Aminci Da Zaman Lafiya A Najeriya

Birgediya-Janar Sani Usman Kukasheƙa, mni (mai ritaya)

42
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Amana: Ita Ce Sinadarin Tabbatar Da Haɗin Kai, Aminci Da Zaman Lafiya A Najeriya

Daga Sani Usman Kukasheƙa, mni

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026

~~~~~~~
A wannan rikitaccen zamani namu, musharaƙa da juna ba za ta taɓa armashi a cikin al’umma ba, dole sai da amana, wacce ita ce sinadarin da ke gina al’umma, ita ke bunƙasa ƙasashe su ɗaukaka cikin wadata da arziƙi.

Amana ce ke zama jagora ga al’umma wajen inganta ayyukanmu, ita ce ke sassaita hanyoyinmu na rayuwar, don samar da haɗin kan ƙasa da ci gaba.

A wannan ƙasa tamu Najeriya, wacce Allah Ya azurta da mabambantan ƙabilu, mai daɗaɗɗen tarihi, amana ce ta taka rawar kasancewarmu ɗinke a matsayin ƙasa ɗaya a can baya, don haka har yanzu dai ita ce za ta yi mana jagora domin ɗorewa cikin nasara a rayuwarmu ta gaba.

A yayin da muke rayuwa cikin wannan duniya mai faɗi a yau, idan mun lura, yadda muka yi wa amana riƙon sakainar kashi, yana haifar mana da mummunan sakamako. Rashin amana na haifar mana da rikice-rikice, rashin jituwa, rashin tsaro, wanda waɗannan sun yi hannun riga da ma’anar zaman tare a tsakanin mabambantan al’ummu a Najeriya.

Sai dai kuma duk yadda abu ya gurɓace, ba duka aka taru aka zama ɗaya ba. Ke nan idan muka buɗa ƙirjinmu muka rungumi amana da fahimtar juna, babu shakka za mu samu ɗinkewa cikin aminci da haɗin kan ƙasa.

Amana, kasancewarta jigon tabbatar da ɗorewar zaman lafiyar al’umma, ci gaban tattalin arziƙi da kishin ƙasa, ita ce kuma ke ɗinke mabambantan al’ummu su zama ɗaya cikin ƙarfi da haɗin kai. Haka kuma ita ce dai ke tabbatar da yarda, gaskiya da himma da amince wa juna cikin haɗin kai domin cin ma kyawawan muradun bunƙasa ƙasa da aka ƙudurta.

A yau ba sai gobe ba, Najeriya na fuskantar babban ƙalubalen zaizayewar amana da karyewar haɗin kai, wanda haka ke cutar da ƙasa da hana mata samun nasara da suɓucewar muhimman damarmaki. Domin saita tafiyarmu a matsayin ƙasa ɗaya, wajibi ne mu rungumi amana domin magance matsalolinmu na rashin fahimta da rikice-rikice, wanda haka zai tabbatar mana da tsaro, zaman lafiya, yalwar arziƙi, sannan kuma ya ɗaukaka darajarmu a faɗin duniya.

Idan muka waiga baya kaɗan cikin tarihi, za mu ga yadda Najeriya ta kasance cikin aminci da amana da juna. ‘Yan kasuwa suna aminta da juna, suna miƙa amanar dukiyarsu da ‘ya’yansu ga abokan hulɗarsu da suka fito daga kowane sashe na ƙasar nan. Wannan ya haifar da zumunci da aminci tsakanin mabambantan ƙabilu a zamunna daɗaɗɗu a can baya. Al’ummu ba su ƙyamar juna, suna baƙuntar juna su ba su wurin zama da karimci. A irin wannan lokaci, amana ita ce babbar kadarar cuɗanya da juna, wacce ke samar da aminci da arziƙi a cikin al’umma.

Sai dai kuma wani abin takaici shi ne, a yau mun samu kanmu cikin wani karkataccen yanayi. A yau mun kasance cikin hatsaniya da juna da harar juna da zargi da yaɗa ƙarairayi da haddasa ruɗani da zuganyewar amana.

Wasu tubala d suka turke mu cikin wannan sabon yanayi marar kyau sun haɗa da yadda muke amfani da addini da ƙabilanci, yayin tattauna al’amuran ƙasa. Wannan turba ita ce ta kai mu ga warware mana haɗin kan da aka san mu da shi a can baya.

Illar rashin amana ta haifar mana da gagarumin koma baya, wanda ya haɗa da rashin haɗin kai, ƙabilanci da ɓangaranci, ta yadda muka koma zama ‘yan marina. Babban misali a nan shi ne, sakamakon da ya biyo bayan zanga-zangar EndSARS (adawa da ‘yan sandan yaƙi da ‘yan ta’adda) da kuma abubuwan da suka faru a yayin zaɓuɓɓukan da suka gudana a bana. Mun ga yadda al’ummar ƙasa ta ɗimauce da son kai da shafi-faɗi da zubar da ƙimar juna.

A wannan mawuyacin zamani, muna da buƙatar mu yi nazari da karatun-ta-natsu domin maido da martabar al’ummarmu, mu kama sahihiyar hanyar sake gina amana, wadda rashin ta ya haifar mana da rashin ci gaba a ƙasa.

To amma idan za mu natsu mu tambayi kanmu, shin wai ma mene ne ya haddasa mana lalacewar amana kuma wane ne ummulhaba’isin haifar da haka? Manyan abubuwan da suka haifar mana da haka su ne, rashin tantance labaran da ake samarwa cikin al’umma da yaɗuwar labarun ƙanzon kurege da yaɗa jita-jita a soshalmidiya da wuraren tarukan siyasa da na addini. Haka kuma akwai son kai da ƙabilanci da suka samu gindin zama a tsakaninmu.

Madamar muna son cin moriyar bambance-bambancenmu, ya zama wajibi mu laƙanci amfanin zaman tare bisa ƙimar abin da ya haɗa mu zama a ƙasa ɗaya.

Akwai misalin ƙasashen da suke da mabambantan ƙabilu amma suka haɗa kai domin gina ƙasarsu. Sun samu nasara ne saboda kowane ɗan ƙasa yana ba da gudunmawa daidai ƙarfinsa wajen gina ƙasa ba tare da la’akari da bambancin yare ko shiyyar da ya fito ba. Don haka masu mulki ba wai za su tsaya ga tafiyar da mulki kaɗai ba, dole ne su samar da kyakkyawan yanayi da saka al’umma a hanya wajen rungumar juna cikin haɗin kai. Haka kuma wajibi ne su tafiyar da mulki cikin gaskiya da amana da adalci da kuma gudanar da manufofi na bai ɗaya, ba tare da nuna fifiko ko son kai ga wata ƙabila ko ɓangare ba. Haka su ma al’ummar ƙasa, a koya masu halin kyautatawa da tausayin juna da haɗin kai da aiki tuƙuru domin gina ƙasa.

Wasu matakai kuma da suka kamata a ɗauka domin magance matsalolinmu su ne, gangamin wayar da kan al’ummar ƙasa, Ilimantarwa da makamantansu. Haka kuma a dawo da waɗansu wasanni da ke da matuƙar amfani wajen haɗa kan al’umma. Haka kuma a ƙarfafa hukumomin wayar da kan al’umma kamar NOA da kuma shirin nan na yi wa ƙasa hidima, (NYSC). Ta hanyar wannan shiri ne za a ƙarfafa cuɗanya da juna a tsakanin ‘yan ƙasa ba tare da la’akari da yanki ko ƙabila ba, da auratayya tsakanin mabambantan ƙabilu, za a gina aminci da amana tsakanin ‘yan ƙasa. Hakan zai gina fandisho mai kyau wajen gina ƙaƙƙarfar ƙasa – Najeriya.

Hukumomi da ma’aikatu da cibiyoyin ƙasa, musamman ma Ma’aikatar Watsa Labarai, Al’adu, Matasa da Wasanni, Cibiyar Horar Da Dabarun Hulɗar Jama’a Ta Ƙasa (NIPR) da ƙungiyoyin sa-kai da sauran ƙwararrun ma’aikatu da cibiyoyin al’umma suna da matuƙar muhimmanci wajen fito da tsare-tsare na bunƙasa haɗin kai tsakanin ‘yan ƙasa.

Ya kamata a samar da wani shiri na ba da wani ɗauni ko kyauta ta musamman ga waɗanda suka yi aure tsakanin mabambantan ƙabilu. Wannan zai zama wani tsari mai armashi na sanya jituwa da haɗin kai da zumunci tsakanin kabilu kuma zai haifar da zaman lafiya a ƙasa.

Kafafen watsa labarai, su ma ya kamata su gyara ayyukansu ta yadda za su dace da inganta haɗin kai da tallafar juna tsakanin mabambantan ƙabilu, maimakon ƙarfafa wasu shirye-shirye da ke haddasa rarrabuwar kai.

Wani abu kuma da ya kamata mu fahimta shi ne, aikin samar da haɗin kai abu ne mai wuya, domin kuwa akwai ƙalubale mai yawa a hanya. Ya kamata hukumomin gwamnati su samar da hanyoyin yi wa al’umma bayani kan duk wani shiri da suka ɓullo da shi. Haka kuma a kula da yanayin da ya dace a fito da wani tsari ko shiri da ya shafi al’umma. Kuma a riƙa tafiyar da al’amura cikin gaskiya da adalci da gamsasshe kuma wadataccen bayani ga al’umma.

Gwamnati da hukumominta za su iya cin ma manufofin alheri ta hanyar amfani da kafofi da na’urorin zamani wajen samar da bayani mai gamsarwa ga al’umma cikin sauri. Waɗannan kafofi sun haɗa da jaridu da mujallu da rediyo da talabijin da soshiyalmidiya da ma ƙungiyoyin sa-kai da aka tabbatar masu kishin ƙasa ne. Kodayake aikin nan babba ne kuma mai cike da ƙalubale, to amfaninsa mai yawa ne, wanda ba za a iya ƙimanyawa ba – samar da haɗaɗɗar Najeriya da ta ginu bisa gaskiya da amana.

A kowane al’amari da ya shafi ƙasa, amana ita ce zare mai ƙarfi da ke ɗinke mabambantan zukata zuwa ɗaya. Ta hanyar rungumar mabambantan aƙidojin juna kamar yadda magabatanmu na dauri da suka kafa ƙasar nan suka koya mana, Najeriya za ta iya magance ɗiimbin matsaloli da ƙalubalenta, ta zama wani tambarin haɗin kai, mai ƙarfi da ci gaba a idanun duniya.

Idan muka sanya AMANA ta zama alƙiblarmu, za mu iya gina gobenmu mai ƙarfi, inda ƙasarmu za ta kasance bunƙasassa, mai zaman lafiya da ingantaccen tsaro da bunƙasasshen arziƙi. Ƙasarmu za ta kasance mai samar da walwala da jin daɗin tsakanin ‘ya’yanta, ba tashin hankali da fitina ba. Daga ƙarshe, amana za ta haɗa kanmu kuma da wannan haɗin kai ne za mu ci nasarar rayuwa a kowane lokaci.

~~~~~~~
Birgediya-Janar Sani Usman Kukasheƙa (mai ritaya), mni, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ƙwararren masanin harkokin tsaro ne da ke zaune a Abuja-Najeriya. Za a iya tuntubar shi ta adireshinsa na E-mail: usmanusk@yahoo.com ko ta Twitter: @skusman
~~~~~~~

Previous Post

Uƙubar Da Talaka Ke Ciki Ta Isa Haka Nan – ZAINAB AHMAD

Next Post

TAURARON GIZAGO: Idris Ibrahim Kubau

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
TAURARON GIZAGO: Idris Ibrahim Kubau

TAURARON GIZAGO: Idris Ibrahim Kubau

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

General Buratai Commiserates With Lagbaja’s Family, President Tinubu

General Buratai Commiserates With Lagbaja’s Family, President Tinubu

November 7, 2024
KATSINA TA YI RASHI: Sa’in Katsina Ya Rasu

KATSINA TA YI RASHI: Sa’in Katsina Ya Rasu

June 27, 2024
Minista Ya Buƙaci ‘Yan Kasuwa Su Zuba Jari Don Haɓaka Shirin Iskar Gas Na CNG

Minista Ya Buƙaci ‘Yan Kasuwa Su Zuba Jari Don Haɓaka Shirin Iskar Gas Na CNG

January 2, 2024
Go Back to the Roots, Write in African Tongues – PAWA

Go Back to the Roots, Write in African Tongues – PAWA

March 18, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • POSITIVE COMRADE
  • BUKAR USMAN: The Human Library
  • Sule Lamido’s Theme of Authenticity

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

POSITIVE COMRADE

POSITIVE COMRADE

May 20, 2026
BUKAR USMAN: The Human Library

BUKAR USMAN: The Human Library

May 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.