Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Tumbu-Madalla
A yau Juma’a, 03-01-1445 (Hijriyya) = 21-07-2023 (Miladiyya), Limamin Masallacin Unguwar Tumbu da ke Garin Madallah, Ƙaramar Hukumar Tafa, Jihar Neja ya gabatar da huɗubar mai taken Muhimmancin Watan Muharram.
Liman ya buɗe huɗubarsa da godiya ga Allah da salati da sallama ga Manzon Allah, Muhammadu (saw). Ya buƙaci al’umma da mu ji tsoron Allah a kowane lokaci. “Mu jajirce wajen roƙon Allah, domin Ya sahale mana shiriya, domin yi masa ɗa’a da jin tsoron Sa a kowane lokaci,” in ji Liman.
Ya bayyana mana cewa, Allah Ya halicci rayuwa da mutuwa ne domin jarabawa ga bayinSa, don tantance wanda ya fi aiki mai kyau. Saboda haka mu dage wajen aikata kyawawan ayyuka, mu guje wa munana iya gujewa, domin mu rabauta a ranar lahira.
Liman ya ce lallai watan Muharram yana da girma da matsayi na musamman a cikin watannin Musulunci. Domin kuwa yana cikin watanni huɗu masu alfarma – Zulƙida, Zulhijja, Muharram da Rajab. Haka kuma shi ne wata na farko a jerin watannin Musulunci.
A cikin Muharram, akwai rana ta musamman, ta 10 ga wata, wacce take da muhimmanci, kasancewar a ranar ce Allah (swt) Ya kuɓutar da Annabi Musa (as) da mutanensa, Ya halaka Fir’auna da mabiyansa a cikin teku.
Liman ya kawo sahihan hadisai daga Manzon Allah (saw), cewa Musulmi su azumci wannan rana ta 10 ga Muharram. Haka kuma a haɗa da ranar 9 ga wata, domin saɓa wa Yahudawa da Nasara. Ke nan azumin biyu za su kama ranakun Alhamis da Juma’a masu zuwa ke nan in Allah Ya yarda.
Malam ya bayyana irin falalar da ke akwai ga wanda ya azumci Tasu’a da Ashura, cewa Allah zai kankare zunubban bawa na shekarar da ta gabata.
Liman ya yi gargadi ga al’umma da mu nisanci bidi’o’in da aka ƙirƙiro game da watan Muharram, kamar shafa kwalli sau bakwai, yin ado ko wata salla ta musamman a ranar 10 ga wata, ko yin abincin cika-ciki da kuma yin hasashen abin da zai faru a shekarar da sauransu.
Malam Ya rufe huɗubarsa da addu’a ta musamman ga al’umma. Alheran da ke cikin shekarar, Allah Ya datar da mu da su, Ya kiyaye mu daga sharruka da fitintinun da ke cikinta.
Amin summa Amin.












