• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, March 5, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Nishadi

Shauƙin Son Faɗakarwa Ya Sa Na Zama Mawaƙi – ABDUL EXTRA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 13, 2023
in Nishadi
0
Shauƙin Son Faɗakarwa Ya Sa Na Zama Mawaƙi – ABDUL EXTRA
39
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

~~~~~~~
Waƙa na ɗaya daga hanyoyin isar da saƙo cikin nishaɗantarwa. Matashi Abdulbasid I. Salis na cikin mawaƙan zamani, wanda ba ya gajiya da rera waƙoƙin fadakarwa. TASKAR GIZAGO ta gana da shi, inda ya bayyana yadda ya fara harkar waƙa.
~~~~~~~
TG: Bari mu fara da gabatarwa. Ko za ka gabatar mana da kanka? Shin wane ne Abdulbasid A. Salis?
ABDULBASID: Ma sha Allah, assalaamu alaikum. To da farko dai sunana Abdulbasid A. Salis. An haife ni a garin Katsina, a Unguwar Ƙofar Ƙaura, a shekarar 1986.
TG: Yaya kuma batun karatu? Da ina da ina aka leƙa neman ilimi kuma waɗanne takardun shaida aka samu?
ABDULBASID: Na yi karatun nazare da firamare Nursery a makarantar Riyadhul Qur’an Katsina. Daga nan na wuce College of Arabic and Islamic Studies. Bayan na kammala a shekara 2009 na shiga Hassan Usman Katsina Polytechnic, inda na yi Diploma a kan Nazarin Harkokin (Business Admistration). A yanzu haka ina ci gaba da karatu a National Open University Katsina. Wannan shi ne kaɗan daga cikin taƙaitaccen tarihin rayuwata da matakin karatuna.
TG: Ga shi ka samu kanka a harkar waƙa. Tun yaushe ne ka fara kuma me ya ja hankalinka ga rera waƙa?
ABDULBASID: To na fara waƙa ce kusan shekaru kamar goma sha da suka wuce, sai dai a waɗancan lokutan, nakan rubuta waƙoƙin ne a cikin littattafai, kasancewar a lokacin ni marubucin littattafan Hausa ne; tare kuma da rubuta wa wasu daga cikin mawaƙa, suna rerawa a sitidiyo.
Daga baya-baya, kimamin kamar shekaru biyar haka, sai na maida hankalina a kan waƙar sosai. Na fara rubutawa tare da rerawa da kaina ina fitarwa.
Don haka ba komai ya ja hankalina a kan waƙa ba, wanda ya wuce cewa ita waƙar ta zamto sauƙaƙƙiyar hanyar isar da saƙo, cikin basira da fasaha da salo. Kasantuwar mutane da dama sukan fi sauraren waƙa fiye da karatun littafi ko kallace-kallacen bidiyo. Ba’ada bayan hakan kuma, da ita kanta yadda waƙar ta zamto abu mafi tasiri da tasirantuwa ga al’adunmu na Hausa/Fulani, tun kaka da kakanni.
TG: Ko da waɗanne mawaƙa kake koyi a wannan harka ta waƙa?
ABDULBASID: To magana ta gaskiya salon waƙoƙina na daban ne, ba zan ce kai tsaye babu wani mawaƙi mai irin salona ba, ko kuma babu wanda ni nake kwaikwayon salonsa ba. Amma dai, ni ban san wani mawaƙi da ya zamo min madubi a kan harkar waƙa ba. Misali, ina waƙa a kan soyayya da zamantakewa, ina yi a kan halin matsi ko ƙuncin rayuwa, ina waƙa a kan shaye-shaye, fyaɗe, tare da sauran wasu laifuka na ɓarna. Ina waƙa a kan matsalar tsaro, cin hanci da rashawa, rashin ayyukan yi, taɓarɓarewar addini da al’adunmu. Kusan ni kowanne ɓangare na rayuwa ina ɗauka in yi waƙa a kansa. Saɓanin wasu mawaƙan da za ka ga na soyayya ne kawai, ko na siyasa, ko a gidan biki, ko sharholiya. Wannan shi ya sa salon nawa ya zama na daban.
TG: Ko mene ne babban burinka dangane da waƙa?
ABDULBASID: Babban burina dangane da waƙa shi ne; ta zama wani makami da za mu yaƙi duk wasu gurɓatattun laifuka da muke aikatawa a rayuwa. Ina so waƙoƙina su zamo tamkar wani haske da yake haskaka duk wani wanda yake a cikin duhu.
Domin ina yin waƙoƙina a kan faɗakarwa tare da nuni a kan wasu ayyuka mararsa kyau da muke aikatawa a rayuwar yau. Don haka, ba ni da wani buri a waƙa wanda ya wuce a duk lokacin da na saki waƙa, ta zamto fitila da za ta haska koda rayuwar mutum ɗaya ne.
TG: Ya zuwa yanzu, waɗanne nasarori ka samu dangane da waƙa?
ABDULBASID: To ma sha Allah. Gaskiya nasarorin da na samu a waƙa ba su ƙirguwa a cikin ƙasa da shekaru biyar da na fara ta. Akwai tarin kyaututtukan yabo daga mabanbantan mutane da wurare. Na yi muhalli ta sanadiyyar waƙa, na yi abin hawa. A duk lokacin da na saki sabuwar waƙa, nakan samu ɗimbin mutane masu kira suna fatan alheri tare da jinjinawa. Haka duk inda zan wuce jama’a na kallo na cikin farin ciki, suna jinjina da fatan alheri. Wannan ma babbr nasara ce, babu abin da zan ce a kan waƙa sai dai Alhamdu lillahi.
TG: Ya zuwa yanzu waƙoƙi nawa ka wallafa?
ABDULBASID: Aƙalla na yi waƙoƙi za su kai guda talatin ko arba’in, waɗanda na wallafa, kuma za a iya samun su a ko’ina, musamman a dandalin soshalmediya, kamar su Facebook, Instgram, Tiktok, tare da sauransu kamar su AudioMack, Apple Music, SoundCloud, Youtube, Spotify da sauransu. Suna nan a ko’ina a intanet. Da zarar mutum ya yi binciko sunan ‘ABDUL EXTRA’ (saboda shi ne sunan da nake amfani da shi a waƙa) zai ci karo da duk waƙoƙina, tare da sabbi ma da za a saki nan gaba in sha Allah.
TG: Maganar iyali fa? Ya zuwa yanzu matanka da ‘ya’yanka nawa?
ABDULBASID: Hahahahaa! Ina da mata ɗaya da ‘ya’ya biyu, mace da namiji.

Related posts

TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?

TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?

February 15, 2026
Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

December 27, 2025
Previous Post

Ambaliya Ce Babbar Ƙalubalen Manoman Jigawa – Isa Billami

Next Post

Sanata Ahmad Babba Kaita: Ba Rabo Da Gwani Ba

Related Posts

TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?
Nishadi

TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?

February 15, 2026
Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?
Nishadi

Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

December 27, 2025
Burna Boy: Fitaccen Mawaƙin Da Ya Rabauta Da Ni’imar Musulunci
Nishadi

Burna Boy: Fitaccen Mawaƙin Da Ya Rabauta Da Ni’imar Musulunci

November 5, 2025
Next Post
Sanata Ahmad Babba Kaita: Ba Rabo Da Gwani Ba

Sanata Ahmad Babba Kaita: Ba Rabo Da Gwani Ba

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

RAMADAN KARIM: 11-1447

RAMADAN KARIM: 11-1447

February 28, 2026
TSOKACINMU NA YAU (16)

TSOKACINMU NA YAU (16)

March 16, 2025
Kwankwaso’s Return to APC: Between the Devil and the Deep Blue Sea

Kwankwaso’s Return to APC: Between the Devil and the Deep Blue Sea

July 11, 2025
BULALAR ZUMUNCI

BULALAR ZUMUNCI

August 6, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Injiniya Tukur Hassan Tingilin (1978-2026)
  • RAMADAN KARIM: 16-1447
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (7)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

RAMADAN KARIM: 16-1447

Injiniya Tukur Hassan Tingilin (1978-2026)

March 5, 2026
RAMADAN KARIM: 16-1447

RAMADAN KARIM: 16-1447

March 5, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.