• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, May 11, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Noma Da Kiwo

Ambaliya Ce Babbar Ƙalubalen Manoman Jigawa – Isa Billami

Akwai Bukatar Gwamnati Ta Tallafa

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 12, 2023
in Dausayin Kauna
1
Ambaliya Ce Babbar Ƙalubalen Manoman Jigawa – Isa Billami

Alhaji Isa Billami a gonarsa

138
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Bashir Yahuza MalumfashiI

~~~

Related posts

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

April 18, 2026
Shin Wai Akwai So? (1)

Shin Wai Akwai So? (1)

June 5, 2025

Idan ana maganar noman zamani a Jihar Jigawa, sunan Alhaji Isa Billami Haɗeja yana sahun gaba. Taskar Gizago ta tattauna da shi, inda ya yi bayanin yadda manoma ke tunkarar daminar bana. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

~~~
TG: Ko za ka gabatar mana da kanka a taƙaice?

BILLAMI: Ni dai haifaffen garin Haɗeja ne na Jihar Jigawa. An haife ni shekaru 56 da suka shige. Na yi karatun addini a gidanmu da na zamani kuma na yi aikin Gwamnati haɗe da kasuwanci da noma da kuma kiwo.

TG: Yaya gonarka ke shirin noman bana?

BILLAMI: Alhamdu lillah. Kamar kowace shekara, a bana mun sake duƙufa wajen noman damina, musamman gero, dawa, wake, riɗi, zoɓo da kuma gyaɗa. Abin da ya sa muka sauya akalar ba da muhimmanci a kan abubuwan da na lasafta a sama shi ne yawan hasarar da muke samu a noman shinkafa, sakamakon ambaliya da muke fuskanta duk shekara a gaɓar Kogin Haɗeja da sauran fadamu da ke yankunanmu. Don haka muka juya akalarmu zuwa noman tudu, na damina ke nan. Kuma alhamdu lillah, muna samu sosai.

TG: Yaya batun noman rani da ya gabata, waɗanne nasarori ko akasi aka samu?

BILLAMI: A gaskiya noman rani a ƙasar Haɗeja ya samu tasgaro mai yawan gaske a ‘yan shekarun nan, kasancewar ambaliyar ruwan kogi da muke fuskanta rani da damina. A gefe ɗaya kuma ga tsadar kayayyakin sinadarai da kayan noma, kamar su taki, iri, maganin feshi da na ƙwari da tsadar ƙwadagon ‘yan aiki. Amma duk da haka ƙalilan da suke da hali sun daure sun aikata, sai dai abin takaicin shi ne a wasu wuraren a tun halin yanzu ruwan sama bai kankama ba amma ambaliya ta shanye mafi yawa daga gonakin al’umma.
Wannan barazanar ta ambaliya da muke fuskanta rani da damina, ta kassara manoma da dama a wannan yanki na Haɗeja. Bayan haka akwai wasu nau’in abubuwa da suke kama da ambaliyar, suma suna taka rawa wajen durƙusar da noma da manoma a wannan yankin.
Abubuwan da suka durƙusar da manoma kuwa su ne kamar haka: Ambaliya, Kwarona, Canjin Kuɗi, Ɓarnar Makiyaya, Satar Kayan Aiki, kamar injin banruwa da kuma satar amfanin gona tun yana tsaye a gonar, ba a yanke ba. Sai kuma tsadar Kuɗin Ƙwadago.
Waɗannan abubuwan da na lissafta, su suka kawo tasgaro wajen ci gaban noma a wannan yanki.
Ɓangaren ci gaba kuma a gaskiya kafin waɗancan matsaloli da na lissafta a baya, manoma suna cikin walwala, domin a eka ɗaya muna girbar shinkafa kamar buhu 50 zuwa 55 a kowace eka.

TG: Yaya batun sabuwar gwamnati da noma, ko akwai shawarwarin da za ka ba Gwamnan Jihar Jigawa dangane da noma da kiwo?

BILLAMI: Shawarwarina ga gwamnati su ne: Na farko dai a magance matsalar ambaliya. Na biyu a samar da ƙaƙƙarfan kwamiti domin magance rikicin manoma da makiyaya. Na uku, a samar da ingantattun iri da kayan feshi da maganin ƙwari da samar da ƙwararrun malaman gona, domin Ilimantar da manoma a kan dabarun noman zamani. A ɗaya ɓangaren akwai buƙatar Gwamnati ta kalli sauran ɓangarorin noma, kamar kiwon kaji da kifi da dabbobin nama da noman itatuwa, kamar mangwaro da dabino da lemo da ayaba da abarba da zogale da makamantansu.

TG: Ko akwai wani ƙarin bayani da za ka ƙara, wanda ban tambaye ka ba?

BILLAMI: Kasancewar Gwaman Malam Umar Namadi (Ɗanmoɗi) manomi ne, ina kira a gare shi da ya bai wa fannin noma, kiwo da Kasuwanci muhimmancin gaske. Domin noma sh ine ginshiƙi, kuma ƙashin bayan tattalin arzikin kowace nahiya da al’umma. Muna yi masa fatan ya zaƙulo zakakuran mutane, bisa ƙwarewa da cancanta, ya sanya su musamman a fannin noma da kiwo.

Previous Post

Ranar Dimokuraɗiyya: Mu Jajirce Wajen Gina Ƙasa – MD Abubakar

Next Post

Shauƙin Son Faɗakarwa Ya Sa Na Zama Mawaƙi – ABDUL EXTRA

Related Posts

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?
Dausayin Kauna

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

April 18, 2026
Shin Wai Akwai So? (1)
Dausayin Kauna

Shin Wai Akwai So? (1)

June 5, 2025
MENE NE SO?
Dausayin Kauna

MENE NE SO?

April 27, 2025
Next Post
Shauƙin Son Faɗakarwa Ya Sa Na Zama Mawaƙi – ABDUL EXTRA

Shauƙin Son Faɗakarwa Ya Sa Na Zama Mawaƙi - ABDUL EXTRA

Comments 1

  1. Adamu sale says:
    3 years ago

    Nice

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

BETARA

BETARA

February 25, 2024
Tallafin Mai

Tallafin Mai

June 2, 2023
BIU: A Visit to a City on a Plateau (2)

BIU: A Visit to a City on a Plateau (2)

December 13, 2023
Lallai Ne A Sallami Shugaban Hukumar Zaɓe – Majalisar Musulunci

Lallai Ne A Sallami Shugaban Hukumar Zaɓe – Majalisar Musulunci

November 13, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi
  • Yan ta’addan Daji Kafirai Ne – Sarkin Musulmi
  • Farewell Ashaka

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

May 9, 2026
Yan ta’addan Daji Kafirai Ne  – Sarkin Musulmi

Yan ta’addan Daji Kafirai Ne – Sarkin Musulmi

May 8, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.