Daga Bashir Yahuza Malumfashi
Sarkin Samarin Galadiman Katsina, Malam Abdul’Aziz bn Abdul’Aziz ya buƙaci attajiran Arewa da su himmatu wajen kafa kamfanoni da zuba jari a Arewa, domin samar da ayyukan yi ga ɗimbin matasan yankin da ke gararamba a titi ba tare da abin yi na sana’a ko aiki ba.
A cewar Sarkin Samarin, “In har masu kuɗi ‘yan bokonmu na Arewa ba za su saka jari a Arewacin Najeriya ba, tabbas haka Arewa za ta ci gaba da kasancewa kwangaba-kwanbaya.”
Ya ƙara da cewa”Mu talakawan Arewa da matasa, mun fi ganin laifin gwamnati fiye da kowa, bayan duk sun kwashe dukiyarsu sun kai ƙasashen waje sun zuba jari.”













To Allah ya sa su ji kira. Su kuma matasan Allah ya shirye su.
Amin Amin Ya Allah.