Daga Garba Al-Hadejawy
Gidauniyar Qatar Foundation Za Ta Gina Katafariyar Makarantar Zamani A Jigawa
Mai girma Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi FCA, ya Kai ziyara ofishin Gidauniyar Qatar Foundation, a ofishinta da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Gidauniyar wadda mallakin ƙasar Larabawa ta Qatar ce, tana gudanar da ayyukan ci gaba a ƙasashen duniya, da suka shafi fannin Ilimi, lafiya, addini da sauransu.
Gwamnan ya kai wannan ziyara ce domin sada zumunci da kuma gode wa wannan gudauniya a kan irin ayyukan taimako da take yi. Sannan ya buƙaci da ta faɗaɗa ayyukanta har zuwa Jihar Jigawa.
Nan take shugaban Gidauniyar reshen Najeriya, a yayin mayar da jawabi ya nuna jin daɗin ziyarar da Gwamnan ya kai masa, sannan ya yi alƙawarin faɗaɗa ayyukansu da kuma samar da katafariyar makaranta (Mega school) tare da babban masallaci a haɗe.
A lokacin ziyarar, Gwamnan ya samu rakiyar Shugaban Hukumar Samar Da Ayyuka ta Jihar Jigawa; Dokta Habeeb Ubale, Babban Sakataren Watsa Labarai, Malam Hamisu Gumel da sauransu.












