• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, April 25, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Addini

ALLAHU AKBAR! YAU TAKE ARFA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 27, 2023
in Addini
0
ALLAHU AKBAR! YAU TAKE ARFA

Mahajjata a Hawan Arfa

22
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Farfesa Sheikh Mansur Sokoto

1. Yau talata 9 ga Dhul Hajji ita ce ranar Arafa.

Related posts

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Mu Ji Tsoron Allah

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026

2. Ita ce rana ta 9 daga cikin kwanukan shekara mafi daraja da falala a wurin Allah.

3. A ranar Arafat ne Allah ya kammala saukar da Alkur’ani ga Manzonsa a wurin Hajjin bankwana.

4. A wannan ranar Allah yana gafarta zunubai, ya yafe kurakurai, ya karba addu’oin bayinsa.

5. Allah ya rantse da wannan rana a inda ya ce:
(واليوم الموعود * وشاهد ومشهود)
Al-Yaumul Mau’úd shi ne yinin alkiyama, Sháhid shi ne ranar Arafa, Mashhúd shi ne ranar Jum’ah.

6. Kuma Allah ya rantse da ranar Arafa inda yake cewa: “والشفع والوتر” Shafa’i shi ne ranar layya, witiri shi ne ranar Arafa.

7. Hadisi ya inganta daga Manzon Allah (S) cewa, “babu wani yini wanda yake mafifici a wurin Allah fiye da yinin Arafa. Allah yana saukowa zuwa saman duniya sai ya yi kuri da mutanen kasa, ga mutanen sama”. Sahihu Ibn Hibban 3583. Akwai hadisai da dama ingantattu a kan wannan. Duba Sahihu Muslim 1348 da Musnad Ahmad 8033.

8. A ranar Arafa ana son yawaita zikiri da addu’a. Kuma mafificiyar addu’a a ranar ita ce: “LA ILAHA ILLALLAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WALHUL HAMD, WAHUWA ALA KULLI SHAI’IN QADEER”.
Ana kuma son a yawaita fadin: “SUBHANALLAH, WALHAMDU LILLAH, WA LA ILAHA ILLALLAH, WALLAHU AKBAR”.

9. Magabata sun kasance a ranar Arafa suna aikata ayyuka iri daban daban na neman lada don samun gafarar Allah mahalicci.

10. An sunnanta yin azumi ga wanda ba ya aikin Hajji a wannan rana. Kuma ana fatar Allah zai yafe ma wanda ya yi shi zunubin bara da na bana.

11. Ana son mutum ya umurci iyalansa da yayansa – har kanana – su yi azumin ranar saboda gamewar falala da gafara.

12. Mutum yana iya yin azumin Arafa ko da ana bin sa bashin azumi. Idan kuma ya yi ramko a ranar babu laifi; ana sa ran zai samu karin falala saboda darajar wannan rana.

13. Babu laifi matafiyi ya yi azumin wannan rana idan ba zai sha wahala a kai ba.

14. Daga sallar asuba ta ranar Arafa ana so yin kabbarori bayan sallah “ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLALLAHU, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD” daga nan har zuwa sallar la’asar a rana ta uku bayan sallah.

15. Daga cikin abubuwan da Annabi (S) ya roka a wannan rana akwai: gafara da jinkai da afuwa, da shiriya da tsarkin zuciya da sutura da wadatar arziki da lafiya da kamun kai da kariya da nasara da aminci da mafi girma kuma uwa uba; samun aljanna firdausi. Don haka ana son mutum ya dukufa da tsarkin zuciya da magiya ga ubangiji musamman a yammacin wannan rana domin neman bukatunsa na duniya da lahira da neman gafara ga kansa da iyayensa da iyalansa da kasarsa da al’ummar musulmi.

16. Akwai matukar hatsari ga yin sabon Allah a ranar Arafa saboda girmanta da darajarta a wurin Allah.

17. Alhazai a wannan rana suna cikin gafarar Allah, kuma Allah yana shaida ma Mala’iku haka.

18. Wanda bai samu tsayin Arafa ba, ya tsaya a kan iyakokin Allah. Wanda ba zai samu yanka dabba a gobe ba, ya yanka son zuciyarsa.

19. Rana ta 10 ita ce ranar Idi babba, kuma ranar layya. Ta fi duk sauran ranaku muhimmanci kuma babu abinda Allah ke so a ranar kamar kwararar da jinin dabbobi ana kiran sunansa.

20. Ranaku 3 bayan Sallah su ne Ayyamut Tashriq. Ana son musulmi ya darajta su, ya ci abinci, ya ziyarci yan uwa, ya caba ado, ya yi sadaka da sashen naman da ya yanka.

Allah ya yi mana muwafaqa da samun gafara, ya saukar mana da aminci da zaman lafiya da yalwantar arziki a kasarmu, ya daukaka addinin Musulunci da Musulmi.

Previous Post

Sarautar Kano: Akwai Yiwuwar Muhammadu Sanusi II Ya Dawo

Next Post

Za Mu Zamanantar Da Ayyukan Hukumar Ruwa – Injiniya Tukur

Related Posts

Duniya Ba Gidan Zama Ba
Addini

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Mu Ji Tsoron Allah
Addini

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
MARTABAR MANZON ALLAH (SAW)
Addini

MARTABAR MANZON ALLAH (SAW)

April 13, 2026
Next Post
Za Mu Zamanantar Da Ayyukan Hukumar Ruwa – Injiniya Tukur

Za Mu Zamanantar Da Ayyukan Hukumar Ruwa - Injiniya Tukur

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Lallai Hukuma Ta Tallafa Wa Marubuta Domin Yaƙar Jahilci – Sheikh Gamawa

NASIHAR JUMU’A: Daga Sheikh Aliyu Said Gamawa

September 1, 2023
Tambayoyin Neman Sani A Kan Littafin: JAWAHIRUL MA’ANI

Tambayoyin Neman Sani A Kan Littafin: JAWAHIRUL MA’ANI

October 5, 2025
Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Muhammad Salissou Hamissou: Ta’aziyyar Ƙwararren Ɗan Jarida Mai Raya Al’adun Gargajiya

Muhammad Salissou Hamissou: Ta’aziyyar Ƙwararren Ɗan Jarida Mai Raya Al’adun Gargajiya

February 26, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.