Daga Shanshani
Oh ni Shanshani, yau na ga ma’anar sarki goma zamani goma. E, mana. Idan ba haka ba, ni dai na san manoma sukan yi sare da sassabe da ƙone haki a bazara. Da zarar ruwan damina ya sauka, su yi huɗa da shuka da sauran hidindimu har zuwa kaka, inda za su girbe amfanin gonarsu, su fara cin gajiya. Dalili ke nan ake cewa bawan damina, tajirin rani.
To, amma abin mamaki, a Najeriya, ga dukkan alamu “Manoman Siyasa” tun a damina za su fara girbin kayan gonarsu. Ta yaya haka za ta faru? Ta hanyar ɗibar babban albashi da alawus-alawus da sauran ganimomin zahiri da na baɗini. Ko ba ku ji tun yanzu Hukumar Tattara Haraji Da Tsara Albashi Ta Ƙasa ta ayyana ƙudurin ƙara albashin Shugaban Ƙasa da na sauran masu riƙe da muƙaman siyasa da na Shari’a ba?
Wannan abin mamaki ne, idan aka yi la’akari da abin da ake ciki a ƙasar nan. Na farko, kwanan nan fa aka cire tallafin fetur, inda farashin komai ya yi tashin gwauron zabo, alhali albashin ma’aikata yana nan jiya-i-yau. Na biyu, albashi da alawus-alawus na shugabanni da masu riƙe da muƙaman siyasa yana da yawa, inda kuma dukkan wata ɗawainiyarsu ta rayuwa gwamnati ke yi masu daga aljihunta. Na uku, ga shi babu wutar lantarki wadatatta amma an ƙara farashinta. Haka zai ƙara ta’azzara farashin muhimman kayayyakin masarufi, ƙananan sana’o’i za su mutu.
A wannan yanayi da ake ciki, abin da ya kamata shugabanni su yi shi ne, su rage albashinsu, su sadaukar da rayuwarsu domin yi wa talakawa hidima. Ba kawai su handame arzikin ƙasa su kaɗai ba. Haka aka san shugabanci – sadaukarwa da hidima ba haɗama da zalunci ba.
Kodayake me kake zaton zai faru tun da farko? Shin ta yaya suka samu kansu a kujerun mulki? Nawa Shugaban Ƙasa ya kashe, tun daga kuɗin sayen fom ɗin takara har zuwa zaɓe da sauransu? Wasu ‘yan siyasar bashi suka ci daga banki ko daga iyayen gidansu na siyasa suka shiga takara. Don haka tun da sun shiga gwamnati, dole ne su bi hanyoyin da za su maida kuɗinsu har su ci riba kafin su koma kan aikin talakawa.
Ni dai a gani na, ya kamata Najeriya da ‘yan Najeriya su dawo cikin hankalinsu. Ya kamata a dawo cikin tsarin gwamnati yadda ya kamata – tsarin da zai samar da ‘yanci da ci gaba ga kowa, tsarin da zai kawo bunƙasar tattalin arziki da ci gaba ga kowa, ba ga shugabanni da ‘yan siyasa kaɗai ba!













