Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-03)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Sunan Fim:
Gidan Badamasi (08-03)
Marubucin Labari:
Falalu A. Ɗorayi
Tsara Labari:
Nazir Adam Salih
Mai Shiryawa:
Falalu A. Ɗorayi da Nazir Adam Salih
Tagwan Mai Shiryawa:
Nasiru NID
Umurni:
Falalu A. Ɗorayi, Ahmad A. Ɗorayi da Sunusi Ɗanyaro
Kanfanin Shiryawa:
Ɗorayi Films, Kano, Nigeria
Shekarar Shiryawa:
Nuwamba 2026
‘Yan Wasa:
Magaji Mijinyawa, Nura Muhammad Ɗandolo, Hussaini Sule Ƙoƙi, Sani Ɗangwari, Falalu A. Ɗorayi, Haruna Baban Chinedu, Abba S. Boy, Rabi’u Ibrahim Daushe, Sulaiman Yahaya Ɓosho, Ibrahim Muhammad Mandawari, Umma Shehu, Hadiza Kabara, Aminu Mirror, Hauwa Ayawa, Amira Shu’aib, Hajiya Jummai da Sauransu
__________
Tafiya sannu kwana nesa. Ya zuwa yanzu dai an kammala haska fim ɗin Gidan Badamasi, Zango Na 8, Kashi Na 3, a ranar Asabar da ta gabata, 21-11-2026 kuma mun ga yadda aka bijiro da sababbin al’amura, waɗanda babu shakka za su ƙara saita alkiblar fim ɗin zuwa ga cin ma abin da ake buƙata – Ilimantarwa, fadakarwa da kuma uwa uba, nishaɗantarwa.
A wannan fitowa, labari ya karkata ga nemo kuɗin Alhaji Badamasi (Magaji Mijinyawa), Naira miliyan 250, wanda zargi mai ƙarfi ya rataya ga wuyan ‘ya’yan attajirin da sacewa. Tuni ƙwararen ɗan sandan farin kaya, Ali Boy ya shiga bincike. Allah da ikonsa, cikin ƙwarewarsa ta mai bincike, ya gano kuɗin kuma ya amso su daga hannun Zillaziyya (Umma Shehu) da Ayuba Ɗankwambo (Nura Muhammad Ɗandolo) da kuma Sadanu (Abba S. Boy).
• Darussa Da Abubuwan Lura A Fim Ɗin
Irin yadda Ali Boy ya gudanar da aikinsa na mai bincike, kyakkyawan misali ne na yadda ya kamata jami’an tsaro su kasance, musamman yadda ya nuna gaskiya da riƙon amana wajen dawo da kuɗin Alhaji Badamasi da kuma irin nasihohi da gargaɗi da ya yi wa ‘ya’yan attajirin.
Al’amuran da suka wakana a yayin amso kuɗin da suka sace, ya haska yadda Ɗankwambo da Zillaziyya da Sadanu suka ƙeƙashe da duniyanci, ha’inci da damfara. Dubi dai yadda suka tattauna yadda za su kasafta ragowar kuɗin da suka maƙale a hannun Zillaziyya. Wannan gargaɗi ne da darasi ga al’umma da su kiyaye mu’amala da masu hali irin nasu.
Akwai wani darasi guda ɗaya game da dukiya da ‘ya’ya, cewa lallai fitina ne. Dubi dai yadda ‘ya’ya da dukiya suka fitini Alhaji Badamasi, musamman yadda a sanadiyyarsu yake ta faɗawa cikin fitintinu iri-iri. Yau matsalar aure, gobe matsalar ɓarayi, jibi kuma fitinar ‘ya’yansa. Hakan ke zama ishara ga al’umma, musamman attajirai, su yi taka-tsan-tsan da dukiya da ‘ya’yan da Allah ya ba su – su riƙa yin abin da ya dace. Hakan ya fito sarari daga nasiha da shawarwarin da Alƙali Mukhtar ya ba abokinsa, Alhaji Badamasi.
Akwai darasin da ke nuna cewa ba daidai ba ne ga maigida, ya fifita so ko ƙaunar wata daga cikin matansa fiye da wata ko wani daga cikin ‘ya’yansa fiye da sauran. Wannan rashin adalci ne kuma babu abin da yake haifarwa sai hargitsewar iyali da fitintinu. Ɗauki misalin abin da ke faruwa a gidan Alhaji Badamasi, musamman yadda ya fifita amaryarsa, Junaidiyya (Mira Shu’aib) da ɗanta Badamasi Jiniya, a kan sauran matansa da ‘ya’yansa.
Tasiri da muhimmancin aure a cikin al’umma. Hakan ya bayyana daga tattaunawar Alhaji Badamasi da Alƙali Mukhtar (Ibrahim Muhammad Mandawari da kuma tattaunawarsa da Baba Daure (Hussaini Sule Ƙoƙi). A kan haka kuma, an bayyana tasirin uwa ga ‘ya’yanta wajen inganta tarbiyya. Hakan ya fito ne daga tattaunawar Ɗankwambo da mahaifinsa, Alhaji Badamasi.
Akwai nishaɗantarwa damfare a cikin wannan fim. Hakan ya bayyana a kusan dukkan tattaunawar da ta wakana tsakanin taurarin. An samu barkwanci tsakanin Taska da Ali Boy, tsakanin Adnanu da Azima, tsakanin Ɗanƙwambo da Alhaji Badamasi da sauransu.
Akwai babban zaren labarin da aka ƙulla a Gidan Badamasi, wanda za a ci gaba warwarewa a kashi na huɗu. Wannan kuwa shi ne batun soyayya da aure. Mun ga yadda Adnanu ya fara kyarkyarar Azima. Ga Ɗankwambo ya ƙyallaro ɗiyar Baba Daure, kamar kuma yadda aka umurci Zaidu, cewa shi ma ya nemo matar aure.
Ɗaya zaren labarin shi ne, ayyana samar da sabon canjin yanayi da ɗabi’un iyalan Alhaji Badamasi. Kada mu mance, an naɗa Ɗanƙwambo muƙamin Shugaban Gida. Alhaji Badamasi ya yi alƙawarin tattara ‘ya’yansa da barorinsa da surukansa, domin inganta rayuwarsu.
Abin jira a gani shi ne, shin da gaske Alhaji Badamasi zai canja daga matsolon attajiri zuwa mai haiba? Shin karkatattun ‘ya’yansa za su natsu, su koma nagari ko kuwa za su koma ruwa daga bisani? Hausawa fa sun ce tun ran gini, ran zane, kamar kuma yadda suka ce, hali zanen dutse…
__________












