Babban Saƙon Injiniya Muntari Sagir Ga Al’ummar Malumfashi
__________
Shugaban Kamfanin gine-gine na Muntasarab kuma fitaccen ɗan siyasa mai taimakon al’umma, Injiniya Muntari Sagir Malumfashi ya yi kira tare da jan hankali ga ɗaukacin al’ummar Malumfashi da kewaye, dangane da al’amuran rayuwa.
Matashin ɗan siyasa kuma mai kishin al’umma, ya yi wannan kira ne a shafinsa na Facebook. Ya ce:
“Ni Injiniya Muntari sagir Malumfashi, ba ni da garin da ya fi Malumfashi. Haka nan, babu wani gari da na fi ƙauna kamar Malumfashi da al’ummar Malumfashi.”
Ya ci gaba da cewa: “Ya ku al’ummar garin Malumfashi, ina kira gare mu, da mu so garinmu, mu nema wa garinmu mutunci a idon duniya. Haƙiƙa siyasa ra’ayi ce, kowa yana da damar yin ra’ayinsa amma ba ta hanyar hayaniya ko tada tarzoma ba. Babu wata al’umma da ta ci gaba ta iran wannan hanya; sai dai koma baya.”
Babban dalilin wannan babban sako na Injiniya Muntari Sagir, mai taɓa zuciya, ba zai rasa nasaba da al’amarin da ya faru, marar daɗi ba a jiya Laraba, inda aka samu rahoton wasu matasa marasa kunya da suka zubar da mutuncin garin Malumfashi; yayin da ayarin mai girma Gwamna Dakta Dikko Umaru Raɗda yake wucewa zuwa Funtua.
A ci gaba da saƙon nasa mai taɓa zuciya, Injiniya ya ce: “Ni ɗan Jam’iyyar APC ne kuma duk damar da na samu, na same ta ne a cikin Jam’iyyar APC. Duk abin da kuka ga ina yi, ina yi ne albarkacin Jam’iyyar APC.”
A cewarsa, “ban taɓa cikakken sati guda, ba tare da na shigo garin Malumfashi ba. Sai dai in ba ni cikin ƙasar kuma duk inda na je, hakalina yana Malumfashi. Shi ya sa ma ban ɗauƙe iyayena da iyalina ba daga cikin garin Malumfashi. To, ima na ɗauke su, ku dangi na fa, na cikin garin Malumfashi?”
A cikin wannan saƙo, Injiniya Muntari ya ɗauki alƙawari wa kansa, inda yake cewa: “Na ɗaukar wa kaina alƙawari, duk abin da zai same mu, ya same mu tare, mu gudu tare, mu tsira tare; bare ma in sha Allahu ba abin da zai same mu sai alheri.”
A ƙoƙarinsa na ci gaba da yi wa al’ummar Malumfashi hidima, Injiniya ya bayyana cewa sai da ya ware sati uku yana zama da ƙungiyoyin cikin gari da wajen gari, domin sauraren koken al’umma. Ya ce, wanda zai iya yi, ya amsa nan take, wanda kuma ba zai iya ba, ya ɗauki alƙawarin zai kai shi inda za avyi shi. Ya ƙara da cewa, duk sati kofarsa a buɗe take ta jin koken al’umma.
Duk dai a cikin wannan babban saƙo, Injiniya Muntari ya ci gaba da cewa: “Idan irin wannan na faruwa, da wace fuska kuke ganin za mu iya tunkarar manyan lmu wajen kawo wa garin Malumfashi ci gaba? Za mu ji nauyin tunkarar su, da irin wannan abin da tsirarun cikinmu suke aikatawa.”
Da yake nuna takaici da alhinin abin da ya faru na rashin kunya ga manya a Malumfashi, cikin fasahar kalami, Injiniya Muntari Sagir Malumfashi ya ce: “Ko guga ba ta yi tsiran komai ba, ta yi na igiya.
“Abin da ya faru jiya a Malumfashi, wanda ba shi ne na farko ba, ya tada mani hankali sosai. Malumfashi ba garin hatsaniya ba ne – gari ne na masu ƙima da mutunci a idon duniya. Duk inda ɗan Malumfashi ya je, ana yi masa kallon mutuntawa. Haka ya samo asali ne daga garin da mutanen garin.
“Mece ce ribarmu, idan muka jawo abin da zai taɓa ƙimar mahaifarmu? Abin takaici ne, duk labari ya bi kafafen sadarwa na zamani a kan abin da aka yi jiya a Malumfashi. Wannan zai iya taɓa ƙimar garin a idon duniya, duk da na san kashi ɗaya ne cikin ɗari na waɗanda suka aikata hakan.”
Da yake ƙarƙare muhimmin saƙon nasa ga al’ummar Malumfashi, Injiniya Muntari Sagir ya ce: “Ina jan hankalinku a kan duk wani mai ƙorafi, ni ƙofata a buɗe take, domin sauraren ƙorafe-ƙorafenku. Haka nan, duk wanda yake ganin an ɓata masa, muna bavshi haƙuri, tare da neman alfarmarsa.”
Ya kulle saƙon nasa da cewa: “Daga masoyin Malumfashi da al’ummarta, ɗan Jam’iyyar APC, Injiniya Muntari Sagir Malumfashi.”
__________













