Malam Saifuddeen Ya Zama Shugaban Hukumar Hisba Katsina
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda ya naɗa Malam Saifuddeen Yakubu Musa a matsayin sabon Babban Kwamandan Hukumar Hisba ta Jihar Katsina.

Naɗin, ya biyo bayan ajiye aiki da tsohon Shugaban Hukumar, Sheikh Aminu Usman (Abu Ammar) ya yi a makon jiya.
Baya ga Malam Saifuddeen, Gwamna Radda ya yi wasu naɗe-naɗen muƙamai daban-daban a jiya Talata. Waɗannan kuwa sun haɗa da Sheikh Dr. Nasiru Abdulrahman Funtua, a matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Al’amuran Alhazai ta Jihar Katsina (Katsina State Pilgrims Welfare Board) da kuma Alhaji Shamsuddeen Surajo Wowo Dutsin-Ma, wanda aka naɗa a muƙamin Babban-Darakta na Hukumar Kiyaye Kwararowar Hamada (Director-General, Katsina State Erosion and Watershed Management Agency – KEWMA).
Sauran sun haɗa da Dr. Sirajo Yakubu Batagarawa da Abubakar Kabir Kusada, waɗanda aka naɗa a muƙaman Masu Ba Gwamna Shawara na Musamman (Special Advisers to the Governor).
Haka kuma, Gwamna Radda ya naɗa Alhaji Ma’aruf Shehu Sanin Kawo Dandume, a matsayin Babban Mataimaki Na Musamman Ga Gwamna (Senior Special Assistant to the Governor); a yayin da shi kuma Alhaji Lawal Ibrahim Musa, aka naɗa shi muƙamin Mamba a Hukumar Kula Da Al’amuran Alhazai ta Jihar Katsina (Member, Katsina State Pilgrims Welfare Board).
_________













