• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, October 11, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Siyasa

Darasin Rayuwa Daga Al’amarin Malam Nasir El-Rufa’i

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 28, 2026
in Siyasa
0
Darasin Rayuwa Daga Al’amarin Malam Nasir El-Rufa’i

Malam Nasir El-Rufai

64
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Darasin Rayuwa Daga Al’amarin Malam Nasir El-Rufa’i

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

October 10, 2026
Fati Muhammad ‘Yar Fim Ta Taro Fushin Mabiya Atiku

Fati Muhammad ‘Yar Fim Ta Taro Fushin Mabiya Atiku

October 8, 2026
Malam Nasir El-Rufai


__________
Babu shakka, rayuwa makaranta ce wadda kullum take koyar da mutum darussa, wasu ta hanyar farin ciki, wasu kuma ta hanyar jarrabawa. Al’amarin Malam Nasir Ahmad El-Rufai, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna kuma tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, ya sake buɗe wani babi mai zurfi na wannan makaranta.

El-Rufa’i ya kasance ɗaya daga cikin fitattun masu ruwa da tsaki a siyasar Najeriya, inda ya yi gwamnan Kaduna na tsawon shekaru takwas, bayan da ya taɓa zama Ministan FCT daga 2003 zuwa 2007.

A cikin rayuwarsa ta siyasa da zamantakewa, El-Rufa’i ya kasance mutum mai ƙulla alaƙa da mutane, musamman abokai, abokan aiki da waɗanda suke ƙarƙashinsa ko suke kallonsa a matsayin jagora.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 23 ga Satumba 2026, ya bayyana cewa a tsawon rayuwarsa ya taɓa tsaya wa mutanen da yake tare da su a lokutan da suka shiga cikin halin matsi da jarabawa, wani lokaci har lamarin nasu yakan shafi shi kansa. Ya ce bai yi hakan ne domin neman yabo ko tsammanin wata rana za a rama masa ba, sai dai saboda ya yi imanin cewa abin da yake yi shi ne daidai.

Sai dai a yau yanayi ya sauya, ga Malam El-Rufa’i shi ma yana fuskantar jarabawa mai girma a rayuwarsa. Ga shi yana fuskantar shari’o’i da kuma tsarewar ake masa, wadda ya ce yana da alaƙa da zarge-zargen da ake yi masa, waɗanda shi kuma ya musanta tare da cewa bai aikata laifin da ake tuhumarsa da shi ba.

A irin wannan yanayi ne na “mayar da bikin” wasu daga cikin mutanen da a baya suke kusa da shi kuma ya taimaka masu iya ƙarfinsa amma suka yi shiru da lamarinsa. Wasu tsoffin abokan siyasarsa, ba shiru kawai suka yi ba, sauya sheka suka yi. Wasu ma cikin yaransa da tsofaffin hadimansa, a yau suna riƙe da manyan muƙamai amma sun juya masa baya.

A kwanakin baya, cikin watan nan na Satumba, jaridu sun ruwaito cewa wasu tsoffin abokansa da jami’an da suka yi aiki a ƙarƙashinsa sun canja sheƙa zuwa jam’iyyar APC, tare da bayyana goyon bayansu ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani.

Wannan shi ne inda darasin rayuwa yake da muhimmanci. Lokacin da mutum yake da iko, duk waɗanda suke kewaye da shi, ba lallai ne su kasance suna tare da shi saboda soyayya ko ƙaunar sa da gaskiya ba.

Wani lokaci yanayi ne yake haɗa mutane. Idan mulki ya ƙare, matsayin ya gushe, ko kuma idan mutum ya shiga wani yanayi na jarabawar rayuwa, a nan zai fara gane aminansa na gaskiya da kuma abokan rani.

A nan zai gane bambanci tsakanin abokin ƙwarai, aboki mai amfani, mabiyi na ƙwarai da kuma abokan rani, waɗanda suke tare da kai saboda wani dalili na ƙashin kansu, ba naka ba.

Sai dai kuma duk da haka, wannan ba wai yana nufin duk wanda ya yi shiru a lokacin jarrabawa maci amana ba ne; domin kowane mutum yana da dalilansa na ɗaukar matakin da ya ɗauka kan wani lamari. Shi kansa El-Rufa’i ya ce mutane suna da ’yancin yin abin da suka ga ya dace da yanayinsu.

Amma akwai wani babban darasi da wannan lamari yake tunasar da mu – kyautata wa mutane ba tare da tabbacin wannan taimako ko kyautatawa za ta dawo gare ka a matsayin ramuwa daga mutumin da ka taimaka ba. Mutum zai iya taimakon abokinsa lokacin da yake cikin jarabawa, ya buɗe masa ƙofa lokacin da ƙofar ta rufe, ya kare shi lokacin da yake cikin matsala amma idan tarihi ya juya, wannan mutumin na iya kasa taɓuka masa komai.

Wannan shi ne abin da El-Rufa’i ya nuna a cikin bayaninsa, inda ya ce bai yi nadamar tsaya wa aminansa da abokansa ba a baya kuma ba zai yi ramuwar gayya ko ɗaukar fansa ga waɗanda suka zaɓi guje masa ba a yanzu.

Don haka, darasin da ya kamata talaka, attajiri, shugaba, ɗan siyasa, ma’aikaci da kowane ɗan Adam ya ɗauka shi ne: Ka yi wa mutane alheri amma kada ka gina rayuwarka gaba ɗaya a kan tsammanin za su rama maka. Ka taimaki mutum saboda Allah, saboda kyakkyawar ɗabi’a, ba wai domin ka mallaki amincinsa har abada ba. Kuma idan Allah ya ba ka iko, kada ka ɗauka cewa duk wanda yake maka murmushi a yau, zai kasance tare da kai gobe. Haƙiƙa, jarabawa tana bayyana wasu abubuwa da zaman lafiya da wadata ba sa iya bayyana maka.

Al’amarin El-Rufa’i, ya kamata ya zama madubi ga duk wani mai mulki da duk wani mai tasiri a cikin al’umma. Mu gane cewa mulki yana wucewa, muƙamai da yanayi suna canzawa, abokan siyasa suna sauya matsayi amma abin da mutum ya yi wa mutane da kuma halayensa, su ne abin da suka rage a tarihi.

El-Rufa’i ya ce abin da ya fi damunsa shi ne, ya kasance cikin kwanciyar hankali, ya gyara tsakaninsa da Allah. “Na bar dukkan lamurrana ga Allah,” in ji shi.

Darasin rayuwa a wannan lamari kuwa shi ne: Ka yi alheri lokacin da ka samu dama. Ka tsaya kan gaskiya lokacin da ka samu iko amma kada ka jingina makomar zuciyarka ga amincin ɗan Adam, domin yanayi yana canzawa, mutane suna canzawa amma Allah ba ya canzawa!
__________

Previous Post

Masarautar Katsina Ta Karrama Dakta Haruna Maiwada

Next Post

Nasiharmu Ta Yau (05)

Related Posts

Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami
Siyasa

Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

October 10, 2026
Fati Muhammad ‘Yar Fim Ta Taro Fushin Mabiya Atiku
Siyasa

Fati Muhammad ‘Yar Fim Ta Taro Fushin Mabiya Atiku

October 8, 2026
Gombe 2027: Kotu Ta Soke Takarar Pantami…
Siyasa

Gombe 2027: Kotu Ta Soke Takarar Pantami…

September 24, 2026
Next Post
Nasiharmu Ta Yau (05)

Nasiharmu Ta Yau (05)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Rai Baƙon Duniya: Allah Ya Ji Ƙan Abokinmu Yahaya Skito

Rai Baƙon Duniya: Allah Ya Ji Ƙan Abokinmu Yahaya Skito

November 15, 2025
Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro

September 26, 2026
Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja

Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja

July 28, 2026
Jigon Ɗan Kwankwasiyya Ya Canja Sheƙa Zuwa APC  Daga Muhammad Mustapha

Jigon Ɗan Kwankwasiyya Ya Canja Sheƙa Zuwa APC Daga Muhammad Mustapha

September 28, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami
  • NASIHARMU TA YAU 17
  • NASIHARMU TA YAU (16)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

October 10, 2026
NASIHARMU TA YAU 17

NASIHARMU TA YAU 17

October 10, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.