Masarautar Katsina Ta Karrama Dakta Haruna Maiwada
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman CFR, LLD ya karrama Dakta Haruna Maiwada, Ɗan-Amanar Katsina kuma Sadaukin Kaita, inda ya aika masa da takardar godiya da yabawa, bisa yadda yake taimakon al’umma a Jihar Katsina.
Takardar mai lamba, EPK/AKU/14/VOL.IV/1098, wacce kuma take ɗauke da kwanan wata, 02-09-2026, mai kanun: TAKARDAR GODIYA, ta bayyana cewa:
“Da fatan alheri ga jama’armu baki ɗaya. Bayan haka, na rubuto maka wannan takarda domin nuna farin ciki da godiya a gare ka, bisa ga ayyukan alheiri da kake gudanarwa a dukkan faɗin jihar nan baki ɗaya.”
Mai Martaba Sarki, a takardar, ya ci gaba da cewa: “Don haka, da ni da ɗaukacin ‘yan majalisata, muna matuƙar godiya da addu’a ta fatan alheri da kuma fatan Allah ya kare mu baki ɗaya. Allah kuma ya ƙara taimakonmu bisa ga taimakon da muke yi na addinin Musulunci. Allah ya sa mu gama lafiya amin.”
Shi kuwa a nasa ɓangaren, Ɗan-Amanar Katsina, Alhaji Dakta Haruna Maiwada, ya bayyana murna da farin cikinsa da wannan karimci da Fadar Masarautar Katsina ta yi masa.
Dakta Maiwada ya bayyana farin ciki a shafinsa na Facebook, inda ya ce: “Alhamdu lillahi, a yau Alhamis na karɓi gagarumar lambar girmamawa daga Masarautar Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Dakta Abdulmumini Kabir Usman. Wannan lambar yabo, babban abin farin ciki ne da alfahari a gare ni.”
Sadaukin na Kaita, ya yi godiya da cewa: “A madadina, iyalina, ‘yan uwa, abokan arziƙi da kuma ɗaukacin al’ummar Gidan Amana Aƙida, muna miƙa saƙon godiya da jinjina ga babanmu, Mai Martaba Sarkin Katsina, a kan wannan yabo da shaida da ya yi mana ta taimakon al’ummar Jihar Katsina.”
Ya ƙarƙare da kyakkyawar addu’ar cewa: “Allah Ubangiji ya ƙara ba mu damarmakin da za mu ci gaba da taimakon al’umma.
__________













