Itaciyar Isa Dika: Bishiya Mai Ɗimbin Tarihi
Daga Mohammed Umar Midala

__________
Bishiyar Isa Dika ta kasance wata muhimmiyar alama ta tarihi, wacce ta kasance wani tambari mai alaƙa da al’adun gargajiya da kuma tarihin al’ummar Biu dangane da zango, ƙaura da hijira.
Kamar yadda aka ruwaito a tarihin baka, na kunne ya girmi kaka, an dasa bishiyar ce a shekarar 1872 ta hannun Kuthli na 22 (Sarkin Biu), Mari Biya, shekara guda kafin ƙaura daga Pelaminta zuwa Biu ta yanzu a shekarar 1873.
Dasa bishiyar ya kasance abin da ke tabbatar da alamar ƙasa mai da shi da albarka, wacce ake sa ran za ta samar da yanayi mai kyau, musamman dangane da dacewarta da noma da kuma kiwo. A bisa al’adar gargajiya, an ciri wani sashe daga cikin bishiyar aka kai shi zuwa sabon matsugunin Biu, a matsayin alamar ci gaba da raya al’ada, wadata da fatan sanun kyakkyawar makoma.
Tsawon fiye da ƙarni guda, Bishiyar Isa Dika ta kasance a kusa da filin Ƙofar Fadar Biu (Palace Square), kusa da Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Biu da kuma tsohuwar Kasuwar Biu.
Wannan bishiya ta rayu tsawon kimanin shekaru 145. Bushiyar tarihi, ta faɗi da kanta a ranar 21 ga Satumba, 2017, da misalin ƙarfe 2:04 na rana, ba tare da iska ko wani mutum ya sare ta ba.
Duk da cewa bishiyar ta mutu, muhimmancinta na tarihi har yanzu yana nan. Isa Dika tana wakiltar ƙaura, kafuwar matsuguni, yalwar ƙasa, noma da kuma ɗorewar dangantakar mutanen Biu da ƙasarsu.
Hakika, Isa Dika ta kasance alamar ƙaura, albarkar ƙasa, tarihi da al’adar gargajiya. Ya dace a kiyaye tarihinta ta hanyar yaɗa labarinta, hotuna, rubuce-rubucen tarihi da kuma, idan zai yiwu, a kafa gidauniya – abin tunawa a tsohon wurin da bishiyar ta kasance, domin al’ummomi masu zuwa su san wannan muhimmin sashe na tarihin Biu.
__________
Malam Midala, masani ne da yake zaune a garin Biu. Imel: Mumarmaidala@gmail.com













